*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
(NWA)
20184~ Babu ko alamar annuri a fuskar Ikram ta tafi gida, dan ba ta so Goggo Indo ta ga fuskarta da fara'a barin har ta rainata.
Sallama ta yi kai tsaye ta shige dakin ummanta, ba ta ko jira Goggo Indo da ke zaune tsakar gida ta amsa ba.
"Ke Ikram! Ikram ke!" Goggo Indo ta fada a wulakance.
Ko waigowa Ikram bata yi ba barin Goggo ta sa ran Ikram zata amsa kiran da ta mata. Ganin haka ya sa Goggo fadin "jar uban can kai! Lallai Ikram wuyanki ya isa yanka. Ba da ke na ke ba ne wai Ikram?" Sai a lokacin ta waigo a daidai isarta kofar dakin. Ta ce "ai ji na yi kina kiran ke, ni kuma na ga babu ke a gidan nan saisa ban tanka miki ba, amma yanzu da kika kirani da ainahin sunana ai kinga na tanka miki."
Mamaki sosai ya kama Goggo Indo, tun da ta ke da Ikram bata taba mata magana irin haka ba, a ranta ta ce 'lallai yarinya ta waye, wannan tsageranci haka, idan ban kula ba ma wata rana sai ta mareni.' A zahiri kuma ta ce "ya jikin uwar ta ki?"
Cikin halin ko in kula Ikram ta ce "yau ashe ma kin san bata da lafiya, to Alhamdulillahi ta ji sauki, kuma idan 'yarki ta mutu *ke ce sila* saboda a kan horon yunwar da ki ke min ne."
Da masifa Goggo ta ce "to da na ke miki horon yunwa ai ba ita na ke yi wa ba. Ba na barinta da yunwa saboda na san ba wadatacciyar lafiya gareta ba kuma ita dolenmu ce, dan haka ki rufe min shashashan bakinki, ki yi abin da zaki yi ki rakani mu tafi asibitin."
"Assalamu alaikum." Wata sallama ce ta katse masu tattaunawar tasu.
Waigawa Goggo ta yi ganin ko waye ya bata mamaki.
Bata ko amsa sallamar ba ta ce "wannan irin zuwan ba zata haka, lale marhabun malam, sannu da isowa, Sannu sannu." Baki wangale ta ke maganar tare da yi masa iso bisa tabarmar da Ikram ta isketa zaune a kai.
Kyakkyawan tsoho ne fari sol, gashin kansa duk ya koma fari, kasumbarshi ma fara ce sol, ya yi kama da irin larabawan nan, tsawonsa ba wani mai yawa bane kuma bai da jiki. Kamar sa sak da Umman Ikram, hakan ya sa ita ma Ikram din ta yi kama da shi, saboda irin fuskar Ummanta gareta.
Ganin Ikram tsaye kuma bata tanka masa ba ya sa shi fadin "Ikram jikata lafiya na ganki tsaye? Haba amaryata ko irin dan lemun taryar angon ma babu?" Ya karisa maganar da zaulaya.
Goggo Indo ce ta yi saurin fadin "ranta bace ya ke ne Ummanta ba lafiya an kwantar da ita asibiti a can ma suka kwana, ka ga kuwa dole ka ganta a haka."
A rikice Malam ya ce "Ya Salaam! Me ya samu Rumana? Ko asumar tata ce ta tashi?"
Ikram kam ciki ta shige bata tsaya bashi amsa ba, saboda gani ta ke har da laifinsa, duk da yana sonta amma ai shi ya ke nuna yana jin tsoron Goggo har ta ke masu yanda ta ga dama, inda yana gwada mata ce wa shi namiji ne da sun samu saukin wani abun.
"Me sameta Indo? Dan Allah ki fada min me ya samu 'yata? Bana son na rasata, kin san cutar asuma *ita ce silar mutuwar mahaifiyar Rumana da kuma sauran yan uwanta guda hudu."*
Wannan maganar da yayi ita ce ta daki kunnuwan Ikram da ta tattaro kayan asibiti tana kokarin fitowa.
Sakin kayan ta yi a rikice tana zare idanuwa. Kar dai abin da kunnuwanta suka jiye mata gaskiya ne, shin menene ma kunnuwan nata suka ji? Mahaifiyar ummanta ta rasu ke nan? Ba Goggo Indo ba ce ta haifi Ummanta?
Mamaki da firgici bai bar Ikram fitowa ba sai wani irin siraran hawaye ke fito mata wanda bata san dalilin yinsu ba. Amma fa biri ya yi kama da mutum, abin da Goggo Indo ta ke mata inda a ce jininta ce ba zata mata shi ba. Saboda yanda ta ke kyautatawa Ummanta inda uwar tata ce ta gaske da zata so jininta ba zata taba kinta ba ko da kuwa tsintota ta yi a bola.
Bata san lokacin da ta fasa kuka da karfi ba. Karar kukanta ce ta daki kunnen Mallam wanda ya sashi razana da fargabar kar dai Ikram ta ji maganar da yayi wadda shi kanshi bai so ya yita ba subutar baki ce.
Cikin dakin ya shiga Goggo biye da shi a baya, ganin kaya watse ga Ikram tsugune ya sashi shiga tashin hankali.
"Ikram me ya faru da ke? Ko jikin umman taki ne?"
Shiru ta masa, Goggo Indo ce ta ce "Ikram da ke fa a ke ko bakya ji?"
"A'a ki bita a hankali mana Indo, Ikram ki fada mana abin da ya sameki kin ji amaryata?"
Idonta ta dago, cikin kankanin lokacin idon ya canja launi, abinku ga mai dara daran idanuwa, sai ta zama kamar abin tsoro. Bakinta na rawa ta ce "Malam ashe ba Goggo ba ce mahaifiyar Ummana, dan Allah ka fada min yanda abin ya ke." Ta sake fashewa da kuka.
Bakinshi na rawa, labbanshi sai kyarma su ke da kyar ya iya fadin "Ita ce mahaifiyar ummanki mana, me kika gani?"
A fusace ta ce "ba halinka ba ne fadin zancen da ba gaskiya ba mallam, dan Allah ka fada min gaskiya, saboda aikin gama ya riga da ya gama, kaf na ji maganganun da ka yi, dan Allah kar ka barni a cikin duhu, ka warware min komai." Da kuka ta karisa maganar.
Ajiyar zuciya Mallam ya sauke kafin ya ce "ban so sirrin boyen nan ya bayyana gareki daga ke har Rumana ba, amma kuma bani da yanda zan yi, duk da cewa alkawari ne tsakanina da Indo da kuma mahaliccinmu cewa tun daga Rumana har jininta ba zasu taba gane cewa ba Indo ta haifeta ba. Yanzu kam ya zama dole ku san komai, ki harhada kayan mu tafi asibiti, a gabanta na ke son fadin komai in kuma nemi gafarar boye mata sirrin da na yi."
Babu musu kuwa Ikram ta harhada kayan ta yi gaba suka mara mata baya.
Ba su jima ba a hanya suka isa asibitin, dakin da Umma ta kwana suka isa. Ko da suka shiga da karfin hali irin nata ta share dakin tsaf kamar ba ita ce ta kwana ba lafiya ba.
Ganin mahaifinta da ta yi ba karamin faranta mata rai ya yi ba.
Saukowa ta yi daga bisa gadon har kasa ta gaisheshi sannan ta gaishe da Goggonta.
Fuskar Ikram ta kalla wadda baki daya ta canja launi, ta yi jajur kamar wadda ta ji ciwo, haka idanuwanta ma sun canza.
"Ikram me ya sameki? Wai ke wace irin yarinya ce wadda bata da aiki sai kuka? Ikram so kike ki siyowa kanki cuta da kanki?"
"Umma ba cuta na ke son na siyowa kaina ba, Mallam ne..." ta sa kuka bata gama maganar ba.
Kallonta ta miyar ga Mallam da da kyar ya iya hadiyar yawu. Bata furta komai ba sai dai ta kuma kallon Ikram ta ce "kin fara magana kuma kin yi shiru. Me ya faru da mallam din?"
Da rawar murya Ikram ta ce "umma ki tambayeshi gashi nan."
"Kun sakani a duhu, dan Allah ku fada min abin da ya ke faruwa."
Wata nurse ce ta yi sallama hannunta dauke da wani faranti mai magunguna da allurai.
"Ahh Lallai maman Ikram ta samu sauki tun da labarinta ta ke, bari na miki allura ki sha magani sai na baki sallama, sauran wanda ba'a gama ba kuma sai ki ringa zuwa chemist ana yi miki, na kwana biyu ya rage." Tana murmushi ta karisa maganar.
Ita ma Umma murmushin ta kirkiro, har ga Allah ta ji dadin sallamar da za'a bata, ko ba komai dama bata son su yi maganar a asibiti duk da ya ke ta fahimci cewa babbar magana ce.
Alluran aka mata sannan nurse din ta ce mata "kin ci abincin ko?"
"Ehh na ci" ta mata karya.
"To ya yi kyau, na ga jikin ma naki yana kyau sosai, barin kawo miki takardar." Ta fice.
Shiru kake ji cikin dakin tun fitar Nurse babu wanda ya kuma fadin komai sai ajiyar zuciya da Ikram ke yi.
Babu jimawa ta dawo, takardar ta mikawa Mallam ta ce "ga wannan takardar sallamar ce, amma dan Allah sai an kula kuma an yi taka tsan tsan ta daina zama da yunwa, ka ga yunwa ce ta mata mugun kamu har ta sakar mata chronic ulcer."
Duk da Mallam bai san ko miye chronic ulcer din ba amma ya fahimci cewa babban ciwo ne kuma yunwa *ce sila."*
"To insha Allahu za'a kula, ba za'a sake barinta da yunwa ba."
"Haka na ke son ji. Allah ya bata lafiya." Ta juya ga Ikram ta ce "kuma sai ki kula, kar ki ringa barinta ta na shiga hayaki ko kuma inda iska sosai ya ke, kinga athma din har yanzu ba wani lafawa ta yi sosai ba dan ma na mata allura ne ta samu sassauci. Na saka inhaler a ledar maganin sai ta ringa shakawa har numfashinta ya daidaita."
Godiya Ikram ta mata sannan suka hada komai suka kama hanyar gida.
@wattpad: PrincessAmrah.

YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.