shi ne silah page 5

1.3K 94 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

     Na Princess Amrah
              (NWA)
               2018

5~ Adaidaita sahu suka tsayar, Mallam ya zauna gaba mai adaidaita din ya jera kaya a booth sannan Ikram ta kama Umma ta shiga ciki ita ma din ta shiga, Goggo Indo ta zauna daga bakin kofa.
    Har suka isa gida babu wanda ya cewa kowa ci kanka. Kowa da kalar abin da ya ke sakawa a ransa.
      A haka har suka isa kofar gida, nan ma dai Ikram ce ta kama mahaifiyarta ta fita, Mallam kuma ya sallami mai adaidaita din sannan shima ya shiga cikin gida.
      Kai tsaye dakinsu Ikram ta zarce da Umma, hakan yasa Mallam da Goggo ma suka mara mata baya.
     Bayan sun shiga ciki Umma ta ce "mallam har yanzu kun barni a duhu fa."
     Gyaran murya mallam ya yi kafin ya ce "wato Rumana dazu ne bayan na iso na ke jin labarin ciwonki, shine subutar baki ta sani fadin wata magana ba tare da shiri ba.
    Maganar ce ta zame min dole na fada miki gaskiyar wani abu wanda ba ki sani ba, wani abu wanda ba ki taba tsammani ba." Ya yi shiru tare da goge 'yar guntuwar kwallar da ta zubo masa yana kokarin tsaida wanda ke shirin fitowa.
     Ya ci gaba da "yau zan baki tushen komai Rumana. Asalina balarabe ne wanda ya ke dan kasar Misrah. Tun ina saurayi matashi na ke soyayya da wata mai suna Ummu Rumana, ita ma balarabiyar ce amma ita gidansu babu wadata sosai ni kuma iyaye na suna da hali muna kuma da sarauta. A boye muke soyayyar saboda mahaifina da mu ke kira da Abii ya haneni da tarayya da yaran talakawa ko da kuwa abotaka da maza ne. Sosai Rumana ta ke kaunata nima kuma na ke kaunarta, sai dai ko ita kanta ba ta bari an sani ba a gidansu.
      Kwatsam wata rana Rumana ta zo har wani gidan mahaifina inda babu kowa dama a can mu ke mahada da ita, ta yi sa'a kuwa ta iskeni saboda ban san da zuwanta ba har ma ina kokarin barin gidan. Ganinta na yi tana kuka sosai kamar ranta zai fita.
    A rikice na ce "Rumana me ya sameki? Wani abu ne?"
     Bata bani amsa ba sai ma kara fashewa da kukan da ta yi.
     Sosai hankalina ya tashi, ganin haka ya sa na umurceta da ta zauna a kan kujera kafin ta samu natsuwa. Mun dauki kimanin mintuna talatin a haka kafin ta ce "Hubbii iyayena sun zaba min miji, na nunar masu cewa ina da wanda na ke so amma sun ce su basu san da wani ba, in har da gaske ne mesa basu san da kai ba? Me sa baka taba zuwa ka nemi izinin neman aurena a wurinsu ba?"
     Cike da damuwa na ce  "ya zasu mana haka? Ya zasu nemi rabani da abar kaunata? Tabbas in har ban aureki ba Rumana zan iya rasa rayuwata."
    "Nima haka Hubbii, dan Allah ka yi wani abu tin kafin lokaci ya kure mana, na san iyayena suna da saukin hali, ko yanzu ka je ka nunar masu da gaske ka ke zasu amince na tabbata."
     Shiru ya yi na dan lokaci kafin ya ce "ai iyayena su ne matsalar, ni ban ma san ta yanda zan tinkari su Abii da wannan maganar ba, amma ki bani nan da kwana uku zan san abin yi."
      "Har kwana uku Hubbi, iyayena fa maganar gobe su ke yi, wai gobe za'a turo wanda suke so ya aureni din, ka sama mana mafita Hubbi, wallahi bana so na rasaka." Ta fashe da kuka.
    Kukanta ba karamin kara tayar min da hankali ya yi ba, hakan ya sa na ce mata "ki daina kuka Rumana, tashi ki tafi gida, na miki alkawarin insha Allahu yau zan yi ta ta kare, kuma gobe goben nan iyayena zasu turo a yi maganar aurenmu."
     Rumana bata san lokacin da ta saki murmushi ba, tafiyar kuwa ta yi ni kuma na ci gaba da tunanin hanyar da zan bullowa lamarin.
      Sai dare na iya fita, kai tsaye gidanmu na nufa. Ko da Ummii ta ganni ta tabbatar da akwai damuwa a tattare da ni, hakan ya sa ta jawoni a jikinta tana tambayana dalilin ganina a wannan halin, hakan kuwa ba karamin dadi ya yi min ba.
    Nan na samu damar zayyane mata duk abin da ya ke raina.
    Da sauri ta sakeni tare da daka min tsawa da karfi "Yar talaka ka ke so ka shigo mana zuria da ita? To ba ka isa ba! Ya zama dole ka canza tunani ko kuma mu sab'a da kai, babu jininmu babu talaka ka ji na fada maka, kuma kar ma ka bari mahaifinka ya ji wannan maganar."
     "Ai na ma riga na ji, kuma in dai 'yar talakawa zai aura to sai dai mu raba jaha, babu shi babu mu tun da shi baya jin magana, tun yana yaro muke nunar masa da hanyar da ya kamata ya bi amma baya ji, kai ba zaka yi koyi da yan uwanka ba? Tun daga mazan har matan wa kaga ya auri talaka? Sai kai? Ko dan ka ga kaine auta ina ji da kai ka ke mana haka? To sam ni ban yarda da wannan abin kunyar ba." Ya juya zai tafi.
      Kamoshi na yi ina kuka sosai na ke rokonsa amma ko saurarena bai yi ba ya fice daga dakin. Hakan ya sa na juya ga Ummii a tunanina ko ita zata ji tausayina na ce "Ummi da talaka da mai kudi fa duk Allah ne ya yi su, ba kuma dan ya fi son mai kudin ya sa ya yi shi a haka ya bar talakan ba. Ki duba wannan lamarin Ummi sannan kuma ki aunashi a mizani. Me sa aka tsani talaka bayan kuma idan so samu ne shima kanshi ba zai yarda ya zauna a halin da ya ke ciki ba? Ummii tarbiyya da asali mai kyau shi ake mawa, Rumana kuwa duka ta hada. Dan Allah ki lallaba min Abii, wallahi ina sonta ba zan iya rayuwa ba tare da ita ba." Kuka sosai na ke har muryata na rawa ina sarkewa.
      Duk da na bata tausayi amma ita kam sam bata goyon bayan danta ya auri talaka ya kawo cikin zuriarsu.
     Ganin Ummii bata da niyyar tausaya min ya sa na barta na shiga dakina, harhada kayana na hau yi kaf da yan kudadena da duk wani abu wanda na san zai min amfani, sai dai kuma ban dauki takardun karatuna ba. Da ya ke dare ne ban jira komai ba na bi ta kofar baya na fice.
     Kai tsaye gidan su Rumana na nufa, wani wuri na samu na ajiye jakata sannan na nufi kofar gidan, kasantuwar dare ne ya sa babu mai gittawa barin na tura a kira min ita. Haka na ringa tsayuwa ga dare yana kara yi.
      Ina tsaye ne yayanta ya dawo daga shagon da ya ke tsaro, ganina a kofar gidansu ya sakashi rusunawa ya gaisheni saboda ya sanni, ya san duk wani dan gidanmu ma.
      Amsa gaisuwar na yi sannan na ce "dama sako ne aka bani na bawa Rumana, ko zaka taimaka ka shigamata da shi, amma dan Allah kar ka bari kowa ya sani."
      "Na maka alkawari babu wanda zai sani da yardar Allah. Barin kai mata Allah sa bata yi barci ba." Ya karbi takardar ya shiga cikin gida.
     A daidai inda na ajiye jakata na je na boye ina jiran fitowarta.
     Na jima a haka kafin Rumana ta fito hannunta rike da jaka tana waige waigen ta inda zata hangoni. Ganin haka ya sa na fito bayan na dauko jakata, ganina da ta yi ya sa ta bini muka ringa tafiya gudu gudu sauri sauri, muna yi muna dan waigen baya ko wani yana binmu. Sa'a muka ci kuwa har muka bar unguwarsu babu wanda ya bimu, saboda dare yayi sosai babu giccin mutane ko kadan.
    Sosai muka gaji da tafiya, Rumana ta zauna sai numfashi ta ke sama sama dan dama tana da matsananciyar athma.
      A rikice na ringa yi mata sannu, ita kuwa kanta kawai ta ke dagawa alamar yauwa.
      Ganin abin yana neman ya ci tura ya sa na ce "baki fito da inhaler dinki ba ne?"
       Da kyar ta iya fadin ka duba cikin kayana na taho da ita.
       Nan kuwa na hau bincikar kayanta har Allah ya hadani da inhaler din. Hamdala na yi ga Allah sannan na bata ta shaka. Cikin lokaci kadan kuwa Rumana ta dawo daidai.
     Muna cikin haka ne Allah ya kawo taxi ta inda muke, da sauri kuwa na tsaidata amma a tsorace kar ace daga gida aka zo nemanmu.
     Babu kowa a ciki mai taxi din ya tambayemu inda zamu je na bashi amsa da "filin jirgi zaka kaimu." Sannan na kwaso kayanmu, Rumana ta fara shiga sannan nima na shiga.
    Har cikin Airpot din ya kaimu, da kanshi ya dauko mana kayanmu sannan na biyashi kudinshi ya tafi.
     Wani wuri na kai Rumana ta zauna sannan ni na tafi na kama binciken hanyoyin da zamu bi dan samun jirgi.
     Ban wani jima ba aka fada min yanda zan yi komai, passport ne kuma ko a lokacin za'a iya yi mana shi sannan mu biya kudin duk kasar da muke son zuwa.
     Zuwa na yi na kirata, nan da nan muka gama komai, na binciki jirgin da zai fara tashi aka shaida min cewa na Nigeria ne, dan haka kudin Nigeria na biya mana nan muka dora kayanmu bisa layi. Wannan *shi ne silar* zuwanmu Nigeria ni da mahaifiyar Ummanki Ikram wato Rumana.
     A lokacin da muka sauka filin jirgin Mallam Aminu Kano ko kadan din hausa bama ji, sai dai zallar larabci da kuma turancina wanda bai kai ya kawo ba.
      A cikin filin jirgin muka samu wurin cin abinci bayan mun samu mai canjin kudi daga riyal zuwa naira, mun ci mun koshi sannan muka biya kudin abincin, muka tafi.
    Daga nan kuma sai gwagwarmayar inda zamu zauna kafin a daura mana aure, kafin mu bar wurin na shawarci Rumana cewa "ko dai mu roki wannan matar mai abinci ki zauna a wurinta kafin wani lokaci? Ni kinga namiji ne ko a masallaci zan iya zama. Ko ya kika ce?"
     Cikin wani irin yanayi ta ce "duk yanda ka ce Hubbii."
    Ko da na je na fara yi wa matar bayani bata san abin da na ke fadi ba,  dan haka na fara yi mata da turanci nan ma dai maganar daya ce. Tsaye na yi ba tare da na san abin yi ba. Muna cikin haka ne Allah ya jefo mana wani mutumi wanda shima a cikin jirgi daya mu ke, daga Misrah ya zo kuma yana jin larabci, dan haka na masa bayanin bukatarmu dan haka shima ya mata bayanin komai. Daga farko bata amince ba, sai da mutumin nan ya mata magiya sosai sannan ta yarda. Ta kira wata budurwa wadda ba zata wuce sa'ar haihuwar Rumana ba, ta umurceta da ta shiga da kayan Rumana cikin shago kafin lokacin tashi aiki ya yi su tafi da ita gidan matar.
@wattpad: PrincessAmrah

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now