*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)60~ Khalid ne kawai zaune a falon lokacin da suka shiga, Ikram ce gaba sai momy biye da ita, wanda kallo ɗaya zaka masu su duka ka gane cewa suna cikin farin ciki ba kaɗan ba.
Khalid ya ce "Ai ni nan da har zan je filin cigiya da sanarwa, na zata kun ɓata ne." Ya yi murmushi.
Ikram ta ce "Ai da ɓacewa muka yi kai kanka da ba'a ganka haka ba."
Zama suka yi sai ga Nana ta fito tana masu sannu da zuwa, momy ta amsa sannan ta ce ma Khalid "Ina yayanku? Ko bai dawo ba shima?"
"Ya dawo yanzu ba da daɗewa ba. Ina ji wanka ya ke." Khalid ya faɗa haɗe da hangen ƙofa.
Da fara'a momy ta ce "Je ka kira min shi."
Tashi kuwa Khalid ya yi ya nufi ɗakin Haidar, ya same shi yana sharce sumarsa yana ɗan duba madubi.
"Yaya ango momy na kiranka." Ya faɗa cikin zaulaya.
Kallonshi ya miyar ga Khalid ta cikin madubi ya ce "Ka fiya wasa da yawa. Je ka ce gani nan zuwa."
Ta cikin madubin shima Khalid ya dube shi ya ce "Babu wani wasa sai gaskiya. Ai ba ƙarya na yi ba kai ɗin ango ne."
Banza Haidar ya masa haɗe da ɗauko turaren oud al-abyad ya feshe jikinshi da shi sannan ya fita, Khalid na ganin haka shima ya mara masa baya suka fice tare.
Bayan ya gaishe da momy ne ya zauna ya ce "Na shigo ai ashe bakwa nan kuma."
Momy ta ce "Wallahi kuwa. Mun je gidanka ne mun yi ƴan dube-dube, Ikram ta rakani."
Murmushi ya yi haɗe da ɗan satar kallon Ikram ya ce "Momy dai da alama kin matsu bikin nan, ko amaryar da angon da ƙyar idan sun kaiki ƙosawa."
"Uhm." Kawai ta faɗa a ranta tana tunanin ya kamata fa ta sanar da Haidar wadda zai aura, saboda tun wuri su ci gaba da tsare tsare yanda ya kamata.
"Wani abu ya faru yau, shiisa na sa Khalid ya kiraka na maku bayani." Momy ta faɗa.
Ɗago kansu suka yi su duka biyun suka kalle ta, sai dai kuma babu wanda ya ce komai har ta fara magana.
"Yau dai Allah ya haɗani da dangina, da kuma dangin mahaifiyar Ikram..." Ta kwashe komai tun daga farko har ƙarshe ta zayyane masu, har da labarinta da bata taɓa faɗa masu ba yau sai da ta faɗa, da kuma na Ikram ma duk ta basu labari.
Mamaki sosai su ke su duka biyun, sun kasa furta komai sai dai ganin abun ma da suke kamar a mafarki.
Momy ta ƙara da "Ikram ma dangin mamanta sun ce zasu zo." Bata yarda ta faɗi ko me zasu zo yi ba.
Murna suka yi a tare, har da Haidar wanda bakinshi ya kasa rufuwa, ashe dai suma da rabon zasu ga dangin uwarsu kamar kowa, da rabon zasu gana da kakanninsu na wurin uwa.***
Washe gari momy ta kira Haidar kafin ya tafi aiki, bayan sun gaisa ta ce "Wai ni kam wani abu ne ya ke ɗaure min kai. Ni ban faɗa maka wadda zaka aura ba, kaima kuma baka taɓa nuna alamun kana son saninta ba. Me hakan ke nufu?"
Murmushi Haidar ya yi wanda har sai da haƙoranshi suka bayyana, bai ce komai ba bai kuma daina murmushin ba.
Cikin haushi momy ta ce "Da kai fa na ke magana kana neman miyar da ni wata sha-sha-sha."
"Momy ai wata magana ce na ji kina yi. Asali fa auren nan ke ce kika ƙirƙira min yinshi ina zaman zamana, kuma kika ce kin zaɓa min mata. To ni miye nawa na zakwaɗin sanin ko wacece bayan kuma ta kusa dawowa a ƙarƙashina?"
"Wannan ba magana ba ce! In dai har kana son farin cikina ya kamata a ce tun sanda na ce na zaɓa maka mata ka nemi sanin ko wacece, ko dan ku dai-dai-ta kanku."
Shiru ya yi bai faɗi komai ba, sai binta da kallo kawai da ya ke.
"To matar da zaka aura ba wata ba ce face Ikram, Ikram dai ta cikin gidan nan." Momy ta faɗa cikin faɗa.
A hankali ya ɗan taune harshenshi sannan ya ce "Na sani!" Kawai ya miƙe zai tafi.
Momy bata iya furta komai ba tsabar mamaki, ya sani? To garin ya? A ina ya ji? Ko yawan suɓutar bakin da Khalid ke yi ne yasa ya gane?
"Idan akwai wani abu da ta ke buƙata sai a bata ATM ɗina, su yi duk abin da su ke so amma ba zan je ba." Ya faɗa a hankali.
"Dawo zauna." Momy ta faɗa haɗe da gwada masa wurin zama.
Komawar kuwa ya yi ya zauna babu musu.
"Ya za'a yi ka ce ba zaka je ba? Kar ka yi haka mana kai ko. Auren budurwa fa ne ba na bazawara ba, yo ko zaurawan yanzu ai sun waye, babu abin da ba'a yi a bikinsu."
Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Momy wannan abubuwan fa naku ne ku mata."
"Kuma ɗin mazan har da ku ai. Ko abu ɗaya ne sai ka je. Na ji suna maganar za'a yi dinner ranar da aka ɗaura aure, ko ita sai ka daure ka je." Momy ta faɗa tana kallonshi.
"Bayan an ɗaura aure kuma? Wane irin abu ne wannan da auren mace a yi dinner? In dai shi ne ba zan je ba. Ina laifin daren biki su yi tun da ba'a riga da an ɗaura auren ba?"
Momy ta ce "Idan suka dawo da ita daren bikin zaka je ko?"
"Insha Allahu." Ya faɗa a taƙaice.
"To hakan za'a yi, zan mata magana sai a miyar daren ɗaurin aure. Ko fa IV ba'a bugo ba. Kai baka da wani aboki wanda zaka haɗa ƴan matan da shi wanda zasu ringa yin irin wannan maganganun da shi?"
Cikin ƙosawa ya ce "Momy su yi magana da Khalid mana."
"Ka fa san Saifullah tafiya zai yi ranar jumu'a. Kuma ma ko yana nan ya za'a yi ya tsaya a abin da ya kamata a ce abokai sun yi a matsayinshi na ƙaninka?"
"To ni dai banda wanda zan haɗasu da shi momy. Tun da ina da ATM a wurinki kawai ki bata, maganar kuɗi idan ta taso kar su ji komai kawai su cira, kuma ai akwai mota hannunta barin a ce dole sai an kaisu duk inda zasu je."
Bayyanannen tsaki momy ta yi ta ce "Kai kam wani irin bahagon mutum ne wallahi. Allah ya kyauta maka."
"Amin." Ya faɗa ƙasa- ƙasa haɗe da fita ya bar ɗakin.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.