53

881 55 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Godiya mai tarin yawa ga Ashnur Pyaar. Na gode ƙwarai Allah ya saka miki da alkhairi ya raya mana Hibban ɗinmu...amin ya Allah_


53~  Tun da suka shiga motar kowa shiru ta yi babu wacce ta yi magana. Sai da suka kusa Birnin Kebbi dan har sun wuce Argungu Miemie ta kira Smart a waya. Kiran farko bata ɗauka ba sai a na biyu ta ɗauka.
   Cikin murya ƙasa-ƙasa dan bata so ta takurawa Haidar ta ce "Hello smart."
    Daga ɗaya ɓangaren Smart ta ce "Wallahi baku da kirki ko kaɗan daga ke har Ikram. Ashe ina da sauran darajar da zaki kirani a waya..."
   Katse ta miemie ta yi ta ce "Ni dai yanzu ki min text na address ɗinku, gobe insha Allahu zan zo har gida na yi ban haƙuri." Miemie ta shirgo mata ƙarya.
   Kai Haidar ya gyaɗa a ranshi yana mamakin yanda wasu mutanen su ke da ƙarya sosai, shi fa ko a gabanshi mutum ya yi ƙarya ko ta wasa ce sai kimarshi ta zube a idonshi.
     Smart ta ce "Ke dai kika sani. Ai ni ba taɓa yarda zan yi ba in ba ganinki na yi a ƙofar gida ba. Tun yaushe kike sakani turo miki address amma baki taɓa zuwa ba? Ni wallahi na yi tunanin kun manta da wata Halimatu a rayuwarku."
     "Ni dai ina jiranki dan Allah yanzu." Miemie ta faɗa.
    "To zan turo miki yanzu insha Allah. Sai ki ci gaba da ado da shi a waya." Ta kashe wayar daga nan.
   Bayyanannen tsaki Haidar ya yi wanda miemie ta jishi har cikin zuciyarta, wani sanyin daɗi ta ji duk da cewa shi ya yi hakan ne dan ya gaji da wayar da ta ke, kasantuwar shi ɗin ba mutum ne mai son yawan magana ba.
    Ikram kuwa haushi ne ya kamata, ji ta ke kamar ta tsaidashi tun ma kafin abin ya yi nisa, tunawar da ta yi da maganan da momy ta mata yasata danne zuciyarta kawai har suka ƙarisa Birnin Kebbi.
    Cikin sanyin jiki kamar ba zata iya ba ta ce "Ga text ɗin da smart ta min nan..." Cike da faɗuwar gaba ta yi maganar tana gudun kar ya faɗa mata zazzafa.
    A maimakon ya miƙo hannu ya karɓi wayar ma sai banza ya mata ko kulata bai yi ba.
     Shiru ta yi kafin ta sake maimaita "Yaa Haidar ga..."
    Guntun tsaki ya yi haɗe da faɗin "Ki karanto mana! Ko baki iya karatu ba ne?"
    Sai da gabanta ya faɗi yanayin da ya yi maganar cikin tsawa.
    Murya na rawa Miemie ta ce "Uhm..Gesse ne.." Ta yi shiru daga nan tana tsoron tsawaita zancen ya kuma yi mata wata tsawar da zata gigitata.
    Banza ya mata a daidai isarsu ƙofar da zata tabbatarwa mutum ya shigo cikin garin Birnin Kebbi.
    A maimakon su ga ya kama hanyar Gesse sai ganin suka yi ya nufi hanyar makarantarsu wadda suka yi. Kallon kallo suka yi inda Ikram dai har yanzu bata ce komai ba, sai dai takaicin hali irin na Haidar kawai da ta ke. Wai a haka ma ya yi sauƙi ke nan. Ga kuma dariya da ke son ƙwace mata tun sanda Haidar ya dakawa miemie tsawa. Husnah da ke matuƙar mamakin Haidar ma shiru ta yi bata ce komai ba.
     Cikin sarƙewar murya miemie ta ce "Yaa Haidar ba fa nan ba ne hanyar Gesse, na taɓa zuwa sai round na uku fa."
    Gyaɗa kai Haidar ya yi tare da ci gaba da tuƙinshi bai tanka mata ba.
    Da ƙyar ta iya haɗiyar yawu ta ce "Allah na san hanyar Yaya..."
    "Dan Allah ki ƙyale ni. Kina da damuwa wallahi." Ya buga uban tsaki.
   Wata irin dariya Ikram ta ɗauka wadda ita kanta bata san sanda ta yita ba. Idonta har hawaye ya ke tsabar dariya, babban abin da ya ba Miemie mamaki shi ne; yanda Ikram ta dage dariya amma Haidar ya kasa ce mata ko uffan. Har sai da ta gaji dan kanta sannan ta yi shiru amma hawaye bai daina fita daga idonta ba.
     "Kin yi daidai." Kawai miemie ta faɗa ƙasa-ƙasa.
    Wata dariyar Ikram ta yi ta ce "Ai diramar taku ce akwai ban dariya a ciki. Wannan uban tsawa haka.." Ta sake yin wata dariyar.
   Banza kawai suka mata, sai Husnah da ta yi ƙarfin halin cewa "Haba mana Ikram ya isa haka. Kin tasa ƴar mutane gaba sai dariya kike mata." Duk da itama tana son yin dariyar daurewa kawai ta yi dan kar Haidar ya rainata.
     Tun daga nan sai shiru ya biyo baya har suka isa makarantar. A bakin gate suka samu masu gadi kamar dai yanda tsarinta ya ke a baya. Sai da suka bincike masu kaya sannan suka tambaye shi inda zai je. Gidan Hajiya Hinde ya shaida masu zai je nan kuwa suka barshi ya shige har staff quarters.
      A bakin gidan ya paka motar, bai ce masu su fita ba sai dash board ɗin gaban Ikram ya fara ƙoƙarin buɗewa har hannunshi ya ringa taɓo ƙirjinta. Jin ɗan laushi laushi yasashi saurin janye hannun wanda tuni itama ta fara ƙoƙarin janye jikinta ta yi gefe sannan ya samu damar buɗewa ya fiddo wata baƙar leda mai ɗan girma.
   Buɗe motar ya yi ya nufi gidanta, bayan ya yi nocking aka buɗe masa ya ga wani saurayi. Tambayarshi ya yi ko Hajia Hinde na nan ya shaida masa da tana ciki ya shigo.
   Shigar kuwa ya yi tana ɗakinta sai da aka kirata, shi kuma Haidar ya zauna falo zaman jiranta.
   Babu jimawa sai gata ta fito da fara'a ƙunshe a fuskarta sanda ta ga Haidar.
    "Maraba maraba da babban ɗa." Ta faɗa tana ɗan tafa hannuwa cikin farin ciki.
    Murmushi ya mata sanann ya gaishe ta ta amsa tana kiran mai aikinta akan ta kawo masa abin sha.
      Ledar ya miƙa mata ta karɓa ya ce "Momy ce ta ce a kawo miki. Kun yi waya ai ko?"
    "Bamu yi waya ba kam. Amma zan kirata." Ta faɗa tare da ɗan bubbuɗa kayan.
    Da murmushi ta ce "To! Kayan menene wannan? Ko an tashi auren ne?"
   Miƙewa Haidar ya yi ya ce "Ki dai kirata ta miki bayani Hajia. Barin kama hanya ni."
    "Ahh, ya da tafiya ko ruwa baka sha ba? Ke yi sauri ki kawo masa ko lemu ne ya tafi da shi mota." Hajia Hinde ta faɗa da ƙarfi yanda mai aikin tata zata ji.
    Lemon ta kawo masa guda ɗaya, ya karɓa yama Hajia Hinde bankwana sannan ya nufi mota.

SHI NE SILAH!Onde histórias criam vida. Descubra agora