*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Khadija Candy, Basman mai sanyinta, Aunty Balee yau shafin nan naku ne domin jin dadinku. Ikram da Khalid na gaisheku kyauta. Thanks for your love and support. Amrah na masifar sonku. #anatare._
28~ Ko da suka isa gida har isha'i ta yi, hakan ya sa basu samu momy a parlor ba wannan ya ba Ikram damar hayewa sama domin ita ma ta gabatar da tata sallar.
Bayan ta gama ta sauko a lokacin har momy ta gama ta fito, zaune ta ke tana kur'bar ruwan shayin da Naanah ta dafa mata mai kayan kamshi da na'a na'a.
Fara'a k'unshe a fuskar Ikram ta matso inda ta ke ta ce "Barka da hutawa momy."
"Barka dai 'yata, ashe kin dawo, yanzu da nake k'ok'arin kiran wayarki ai. Dan na yi tunanin ko adaidaita sahu ce baki samu ba, Khalid kuma bai dawo ba tun da ya fita gyaran waccan motar."
Mamaki ya cika Ikram matuk'a, ashe dama ba momy ce ta ce ya d'auko ta ba? Lallai yau yana jin 'yan mutunci ne.
"Momy ai ba ma napep 'din na hau ba, Yaa Haidar ne ya dawo da ni." Ta fad'a tare da tashi ta d'auko kofi domin zuba ruwan shayin, saboda duk da shayi bai dameta ba amma tana son mai kayan k'amshi.
Haka suka zauna har kusan k'arfe goma sai ga Khalid ya dawo. Bayan ya yi sallama ya shigo ya ajiye makullin mota a kan tv stand tare da fa'din "am very tired wallahi."
Momy ta ce "Sai yanzu aka gama gyaran ko kuwa dai ka wuce naka uzurin?"
Kafin ya bada amsa Ikram ta yi caraf ta ce "Momy wane wurin gyara ne har ya war haka ya ke a bud'e? Daga wurin sarakuwarki dai ya ke."
Harararta ya yi yana k'ok'arin takowa inda ta ke ya jefeta da handky d'inshi ya ce "Momy dont conshider this girl. Ni wata budurwa ce da ni?"
Dariya suka yi su duka shima Khalid ya d'auko kofin ya zuba shayi.****
Yau ta kasance rana ta farko wacce Ikram zata fara zuwa makarantar koyon kwalliya. Shiryawa ta yi tsaf cikin wani purple d'in leshi 'dinkin doguwar riga, mayafi purple ta yafa tare da 'yar 'karamar jaka irin na zamani itama d'in purple.
Ko da ta sauko k'asa sai ba'dad'a k'amshi ta ke murmushi k'unshe a fuskarta.
Zaune su ke su uku a parlor, momy, Khalid sai kuma Haidar zaune a tashi kujerar daban.
Magana su ke yi hakan ya sa ta nufi dining ta zauna domin cin indomie da Baabah Naanah ta dafa mata.
A hankali ta ke d'an jiyo muryoyinsu suna magana.
Momy ta ce "Ban san me yasa ba Goggoji ta dameni da magana d'aya ko yaushe. Ko jiya bayan tafiyar su Ikram sai da ta zo, maganar kud'ad'en nan dai ce ta k'i shafa min lafiya. Shi ne na yanke shawara kawai a kan ni zan bata wani abu daga cikin kud'ad'en da na ke kasuwanci. Allah bishi idan wancan ku'din sun fito aka raba, in da ciko sai na mata, idan kuma babu ni na biyota ma dai na yafe mata.."
Bata gama rufe baki ba cikin wani yanayi Haidar ya ce "Haba momy! A kan me kike tunanin bata kud'i bayan kuma ku'din da ta ke maganar basu fito ba? Cutar kanki kike son yi ko kuwa jarin naki kike son karyawa?"
Ajiyar zuciya momy ta sauke ta ce "Haidar har yanzu ku yara ne. Goggoji na da matsala sosai, a kan abin duniya komai zata iya yi wa mutum, gashi kuma su Samira suna 'kara tunzurata."
Khalid da tun fara maganarsu ya gama k'ulewa ya ce "Su Samirar wa? Wallahi in ma dan su ne yasa Hajiya ta ke cin zarafinki ni zan iya b'a'b'ballasu kuma babu yanda za'ayi da ni. Ni ku barni da su, nasan maganinsu."
"Ba zan barka dasu ba Khalid dan kar ka je ka yi abin da ba shi bane. Ku barni na yi kamar yanda na ce d'in. Zan bata a cikin kud'ina ai ba wani abu ba ne. Zama lafiya ai ya fi zama 'dan sarki. Yanzu dai kai." Ta nuna Haidar. "Ka kira Alhaji Kallah ka ji ya ake ciki? Ka kuma tambayar mana shi kamar nawa ne ake tsammanin zasu kai? Idan ya fad'a maka ka ga daga nan kawai sai na bata a nawa. Kar ku ji komai Allah yana tare damu."
Duk kansu basu kuma fad'in komai ba sai dai cike suke da takaicin wannan al'amarin, tun Abbansu yana raye Hajiyarsa ke guma masa daga shi har iyalinshi, yanzu ma da ya rasu ba zata saduda ta shafa masu lafiya ba? Ita wato jikokin 'ya'yanta mata kawai ta ke so, kuma su ne ma wanda bata jin d'ad'insu.
Ikram da ke zaune ta kasa cin indomie wani irin tausayinsu ne ya kamata. Ashe dai kowa da kake gani da tashi matsalar, mai d'aki kuwa shi ya san inda ya ke masa yoyo. "Allah ya kyauta." Ta fad'a tare da mik'ewa dan da alama sun gama maganar.
Murmushi ta yi ta ce "Sannu da hutawa momy."
Itama momy murmushin ta k'irk'iro ta ce "Yauwa Ikram, ba dai har kin shirya ba?" Dan dama bata ga fitowar Ikram ba, baya ta bama dining table d'in kuma akwai 'yar tazara a tsakaninsu, sai dai kuma mutum zai iya jiyo fira idan ana yi.
"Na shirya momy ai har ma na karya." Ta bata amsa tare da zama a d'aya kujerar wadda ke fuskantar ta Haidar.
"Yaa Khalid ka karya mu tafi, ka ga har 8 d'in ta kusa." Ta fad'a tana kallonshi.
"Mu tafi kawai, zan karya idan na ajiyeki." Ya fad'a cike da damuwa a fuskarsa.
"Me ya faru ne yaya? Ko na maka laifi ne?" Ta fad'a sukuku.
K'ak'ulo murmushi ya yi ya ce "Ehh kin min laifi, na kamaki da laifin saka gyale alhalin kuma makaranta zaki je."
Baki ta turo ta ce "To ai dai makarantar koyon kwalliya ce, idan ban yi kwalliya ba za'a rainani."
Momy ta ce "Haka ne 'yata. Ki tashi ku tafi to, Allah ya bada sa'a."
Duk wannan firar da suke Haidar na zaune bai ko d'aga kanshi ba sai latsar waya kawai ya ke.
Hannu Khalid ya mik'a mashi ya ce "To bari mu wuce yaya, daga can nima zan wuce INEC d'in, tun last week ya kamata ace na yi clearance amma na tsaya shiririta."
Shima Haidar mi'kewar ya yi ya ce "Momy nima zan wuce, akwai patients da yawa masu jirana, tun k'arfe bakwai Musa masinja ya kirani wai sun shiga layi."
A ran Ikram ta ce 'Ashe kana da wannan tunanin, 'dan rainin hankali.'
"Tou Allah ya tsareku ya maku albarka." Momy ta fad'a fuskarta d'auke da fara'a.
Fita suka yi tare, a bakin motar Haidar suka rabu, Khalid ya masa fatan alkhairi Ikram kuwa har yanzu ko k'ala bata had'ata da Haidar d'in ba.
A cikin mota ta Kira Yaya Kareema, bugu biyu ta d'auka da sallama suka gaisa.
Bayan ta tambayeta lafiyar miemie da Khairat ta ce mata "Ai miemie ma yau zata koma gida, dama su Umma ne suka yi tafiya zuwa k'asar Cairo kuma yau zasu dawo."
Ikram ta ce "Tou masha Allah! Allah ya dawo mana dasu lafiya. Dama maganar da muka fara ce, na ce yaushe kike da lokaci na zo mu k'arisa? Saboda in da wani taimako da za'a mana a yi, kuma ko miemie bana so ta san da wannan maganar."
Kareema ta d'an yi tunani kafin jim kad'an ta ce "Ranar Thursday mu had'u da ke Shari'a court, wuraren k'arfe sha biyu na rana, kin ga daga can sai mu wuce gida tare."
"Dama kuwa k'arfe sha biyun nake tashi daga makaranta. Kin ga fad'uwa ta zo daidai da zama ke nan."
"Ehh, Allah ya kaimu to, sai na jiki." Ta tsinke wayar.
Juyowa ta yi ta fuskanci Khalid da ke driving zuciyarsa cike da damuwa ta ce "Yaya dama akwai wata magana ne da na ke son yi da kai, wani taimako ne na ke so ka min, kuma dan Allah tsakanina da kai ne kawai."
Kallonta ya d'an yi sannan ya juya ga driving d'inshi ya ce "To ina saurarenki."
Magana ta mai 'kasa k'asa, wadda duk k'wak'wata ta in kwaso wannan rahoton na kawo maku ban samu yi ba, haku'ra na yi kawai dan na san zan ji komai daga baya.
Gani nai kawai ya d'an yi murmushi ya ce "Deal! Allah ya taimaka."
A daidai nan kuma suka isa makarantar.
"Ai ba sai na rakaki ba ko?" Ya tambayeta bayan ya yi parking.
"Ehh yaya, ga reciept d'in nan ai a jakata, gwadashi kawai zan yi." Ta bashi amsa tana 'kok'arin bud'e motar.
"To Allah ya bada sa'a Ikram!" Ya fad'a cikin sanyin murya.
Juyowa tai ta kalleshi dan yanayin yanda ya yi maganar sosai ta shiga cikin wani yanayi wanda ita kanta bata san wane irin yanayi ba ne. Bata san sanda ta sakar mai murmushi ba ta ce "Na gode Yaa Khalid." Ta fice daga motar.
Ya jima bai tayar da motar ba, kallon wurin da ta zauna kawai ya ke saboda har yanzu 'kamshin turarenta yana nan bai gushe ba.
Kusan minti goma ya yi kafin ya tayar da motar ya nufi inda ya ke service d'inshi.***
Bayan Ikram ta shiga ta yi reporting a kan ta zo, wani babban littafi aka d'auko aka rubuta sunanta sannan aka mata tick alaman ta zo.
"Ikram Mahmoud, you can go there." Matar ta nuna mata wani wuri wanda k'ofarsa glass ne, ta hangi mutane ka'dan a ciki sai kuma wata budurwa zaune daga gefe wacce da alama ita ce mai koya kwalliyar.
Kai tsaye ta isa wurin, slice door ce hakan yasa ta jata ta bu'de.
"Assalamu alaikum." Ta fad'a tare da isa inda suke zaune.
"Wa alaikissalam." Budurwar mai koya kwalliyar ta fad'a, dan dama tun daga yanayin dressing d'inta zaka tabbatar da cewa musulma ce kuma cikakkiyar bahausa.
"Good morning ma." Ta fad'a tana kallonta.
Daga ganin budurwar ka san ba wata babba ba ce, dan da kad'an zata wuce sa'ar Ikram d'in ma.
"Morning, are you a new student?"
"Yes ma." Ikram ta fad'a.
"Ok, you can sit here." Ta nuna mata kujerar kusa da ita.
Zama Ikram ta yi bayan ta ba sauran 'yan matan wurin hannu sun gaisa.
A hankali a hankali har d'aliban suka fara taruwa, sun kai kusan mutum goma sha biyar ne malamar ta fara gabatar masu da darasin farko, wato kayan kwalliya da sunayensu.
Sosai Ikram ke jin da'di, ita dai dama tana son kwalliya da gayu ba tun yanzu ba, gashi kuwa Allah zai cika mata burinta.
Sai k'arfe sha biyu daidai aka tashesu, ko da ta fito Khalid na zaune a kan mota yana jiranta. Wani irin murmushi ta saki tare da nufar inda ya ke.
"Ahh 'yan mata an fito ke nan" ya fad'a bayan ya diro daga motar.
"Na fito kam, har an gama darasin yau sai kuma na gobe." Ta fad'a tana kallonshi.
"Masha Allah! Ai wata biyun kamar gobe ne. Albishirinki dai." Ya fad'a bayan ya shiga mota ya bud'e mata k'ofar.
"Goro." Ta fad'a tare da rufe k'ofar motar.
"Fari ko ja?" Ya tambayeta.
"Fari tass." Ta bashi amsa.
"Na dubo miki waec d'inki."
Dafe 'kirji ta yi gabanta ya fara fad'uwa ta ce "Yaya bana son ji wallahi, ban san ya zan yi ba idan sakamakona bai yi kyau ba."
"Matsoraciya kawai." Ya fad'a tare da bud'e dash board ya zaro wasu takardu guda biyu, d'aya ta exam card d'inta ce data bashi, hakan yasa ya miyar da ita a cikin dash board d'in
A hankali ya ke tuk'a motar hakan ya sa ya ringa karanto mata result d'in a hankali.
"English A1
Mathematics B3
Chemistry B3
Biology A1
Pysics B2
Islamic A1
Civic education C3
Geography A1
Economics D7"
Wata irin shewa Ikram ta d'auka da k'arfi kafin daga baya ta yi hamdala cike da farin ciki.
"Yaya Result d'ina ne haka? Oh ni Ikram ya zan yi dan murna? Am very happy." Bata san sanda ta 'kadaddabeshi ba duk da driving d'in da ya ke.
Wani irin sanyi ya ji a zuciyarshi, sai dai kuma ya zai yi? Ikram ba muharramarsa ba ce, dole ya yi saurin janyeta da dabara yana fad'in "Congratulations k'anwata."
"Thanks you yayana." Ta ma rasa inda zata sa kanta tsabar farin ciki.
Parking ya yi da mota a daidai bakin Mr. Bigs. Kallonshi tai ta kalli inda ya yi parking d'in, zata yi magana ta ji ya ce "shhh! Bana son yawan tambaya." Ya fito daga motar tare da zagayawa ya bud'e nata b'angarenta.
Jere da juna suka isa ciki, duk wanda zai kallesu sai ya yi sha'awarsu, duk da ya ke Khalid ba fari ba ne amma kuma shi d'in mai kyau ne, ga uwa uba k'warjini da fara'a wanda duk wata mace wadda zata kalleshi sai ta yi marmarin ta sake kallonshi.
Kai tsaye wurin cin abinci suka nufa, waitress ce ta kawo masu takarda dan su zab'i abin da suke so.
Sakwara da miyar ugwu ya zab'a, ita kuwa Ikram chips ta zab'a dan dama ba komai ta ke ci ba.
Kafin a kawo abincin ne Khalid ya d'an yi jim, sannan ya ce "Ikram dama akwai maganar da na ke son na sanar miki, na d'auki alwashin ba zan tab'a fad'a miki ba sai ranar da jarabawarki ta fito, saboda daga ranar ne yarintarki zata tafi, dan zaki fara tunanin tafiya jami'a. Sai dai kuma ban san ta yanda zaki fahimci zancen nawa ba."
D'agowa tai ta kalleshi, tabbas babu alamar wasa ko kuma barkwanci a fuskarsa, hakan yasa ta duk'ar da kanta ta ce "Ina saurarenka yayana."Classic_amrah ce
![](https://img.wattpad.com/cover/145187938-288-k711487.jpg)
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.