*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)24~ Cak! Ikram ta tsaya babu ko alamar damuwa a tattare da ita.
Matsowa inda ta ke Corpers d'in suka yi, mace da namiji ne.
"Wher are you going to? (Ina zaki je)" Namijin ya tambayeta.
"Sir...sir...I want to go home..(Malam ina son zuwa gida ne)" ta fad'a in tammered.
"Going home? In this night? Let me see your face..(Tafiya gida? A cikin daren nan? Bari in ga fuskarki)" macen ta fad'a tare da kunna fitilar wayarta tana kallon Ikram.
"Ikram! Are you the one? Whats wrong with you? Why do you want to go home?(Ikram! Ke ce? Me ya sameki? Me yasa kike son tafiya gida?)" Ta fad'a cike da mamaki.
Shiru Ikram ta yi saboda hawayen da ya fito mata. Tana matuk'ar jin kunyar Aunty Precious saboda sonta da ta ke yi, tun tana bak'uwa a makarantar Aunty d'in ke k'aunarta, saboda dama Ikram akwaita da farin jini ga mata da maza, dan akwai gashi ga uwa uba kuma farar fata mai d'aukar hankali.
"Calm down Ikram. Stop crying ehhn...tell me please, what is your problem? (Kwantar da hankalinki Ikram, ki daina kukan kin ji? fada min dan Allah, menene matsakarki?)" Ta fad'a cikin natsuwa, saboda yanayin da ta ga Ikram ta tabbatar da akwai damuwa.
Cikin rawar murya Ikram ta fara mata bayanin kaf abin da ya faru da ita tun daga farko har k'arshe bata rage mata komai ba, tun da dama Aunty'n tana jin hausa amma ba sosai ba, sai ta dinga mata mixing da kalmomin turanci 'yan wanda ta sani, saboda a d'an zaman da ta yi makarantar ta fara koyon turanci, ko a class dama ba'a hausa kwata kwata sai dai turanci dole.
Cike da tausayi Precious ta ke d'an bubbuga bayanta tana fad'in "Am sorry Ikram, if you go now, where are you going to? Or are you going to your village..? (Ki yi hak'uri Ikram, idan kin tafi yanzu ina zaki je? Ko zaki koma k'auyenku ne?)" Dakatar da ita Ikram ta yi ta hanyar tashi zaune ta ce "wannan k'auyen? Allah ya kyauta min, ai gwara na mutu a kan na koma can."
Kad'a kai precious ta yi ta ce "ehhn, you don't have any alternative than to stay here. Haba mana Ikram (kin gani ko? Baki da wani zabi banda ki zauna a nan), that Momy ta miki komai fa, mesa kina so ki saka mata da guduwa. Ki yi haku'ri kin ji? Any person da ya yi hak'uri yana samun nasara. Please dont run.." ta fad'a cikin sigar rarrashi da hausarta wadda bata gwanance da ita ba.
"Ok Aunty, Na hak'ura zan tsaya tare da momy for your own sake! Thanks for your advice..(Na hakura zan tsaya amma saboda ke. Na gode da shawararki)" Ta fad'a tare da share hawayenta. Zuciyarta cike da sak'e sak'e wanda ita kad'ai ta barwa kanta sani.
"Am very happy my Ikram, let me escort you to your class.(Na ji dadi sosai Ikram, mu je na rakaki ajinku.)" Tashi suka yi su duka har da d'ayan corper'n wanda suka fito yawo tare da Precious Allah ya had'asu da Ikram tana 'ko'karin guduwa.
Har class suka kaita, prefect di'n na neman yi wa Ikram masifa Aunty precious ta mata bayani cewa ita ta aiketa shisa ta dad'e bata dawo ba.
Zama ta yi zuciyarta sai rad'ad'i ta ke mata. Har ga Allah bata so ta sake kwana a cikin makarantar ba, kawai dai ta hak'ura ne saboda kar precious ta ce ta k'i ta mata wannan alfarmar, amma fa ta k'udura a ranta cewa ko hutu aka yi ba zata koma gidan su momy ba, sai dai duk inda zata tafi ta tafi.
Ko da miemie ta ga yanayinta ta tabbatar cewa akwai damuwa, hakan ya sa ta ce "Ikram akwai abin da ya ke damunki. Ko Aunty'n taki ta zaneki ne yau?"
Kai Ikram ta kad'a ta ce "Ko kad'an wallahi. Ai kin san ni da Aunty Pre ba damuwa tsakaninmu."
"To ki fad'a min, me ya sakaki kuka, dan wannan fuskar taki akwai alamun kin sha kuka."
"Ban so na fad'a miki ba miemie amma ya zama dole na fad'a miki d'in, na so ace Aunty pre ta barni na gudu amma ta dakatar da ni, bana son gidan momy su duka na tsanesu!" Ta sake fashewa da wani kukan.
Ido bud'e miemie ta ce "To su kuma me suka miki? Ina ce Dr. Ali ne ya miki laifin? Haba mana Ikram! Wace irin zuciya gareki ne wadda laifin wani ke shafar wani? Ke da kanki kike bani labarin irin halaccin da matar nan ta ke miki. Ta d'aukeki tamkar 'yar da ta haifa da cikinta. Haka Khalid ma ya miyar da ke tamkar k'anwarsa ta jini. Me sa ba zaki duba alkhairin da suka miki ba kika duba sharrin da wani ya miki ba su ba? Ki duba wannan zancen ki aunashi a ma'auni. Kin san kalar rayuwar da zaki fad'a idan kin gudu? Kin san gidan da zaki koma? Dr. Ali shi ne makashin ummanki, kika san ko ki fad'a inda za'a zama makashinki? Sam! Baki yi tunani mai kyau ba Ikram, dan Allah kar ki ma Momy da Ya Khalid haka, ki bar komai ya wuce, Allah yana tare da mai yafiya..."
Sosai jikin Ikram ya mutu, ta san cewa har ga Allah duk maganar da miemie ta fa'da mata gaskiya ne, ta yarda da duk maganganun kuma ta d'auki shawararta, ta hak'ura zata zauna d'in.
"Sanda Aunty Pre ta min magana na dai ce mata na hak'ura ne ba wai kuma dan na ha'kura di'n ba. Amma yanzu na rantse miki da Allah na hak'ura, ba zan tab'a guduwa na bar Momy ba. Amma fa maganar komai ya wuce ne babu ita, kin san cewa ba zan tab'a manta abin da Dr. Aliyu Haidar ya min ba, kuma ko ba dad'e ko ba jima sai na d'auki *FANSA."*
D'an dafa kafad'arta ta yi ta ce "Zaki yafe masa Ikram, na tabbatar cewa akwai wannan ranar. Tun da dai kin hak'ura ai shi ke nan."
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.