25

1.1K 68 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

25~ Kallon wanda ya rik'e masa hannun ya yi, wa zai gani? Khalid ne tsaye sai huci ya ke ya kuma k'i sakin hannun.
    Cikin d'aurewar kai Momy ta matso inda su ke ta ce "Wai me kuke yi ne haka? Miye haka na ce iye!?"
    Sakin hannunshi Khalid ya yi har yanzu bai daina hucin ba, Ikram kuwa tuni ruwan k'walla suka soma wanke fuskarta.
    "Momy..." ya yi shiru yana jin zuciyarsa na masa zafi ga bugun da zuciyar ke masa da sauri da sauri.
    "Ka natsu Saifullah!   Baka san idan kana bari zuciyarka na irin wannan zafin sai dai kawai ka jita ta buga ba?"
    K'asa ya zauna dab'as dafe da kanshi, Haidar kuwa ya zama speechless, magana ma ya kasa yinta sai mamakin d'an uwanshi ya ke.
   "Ku ringa sakawa zuciyarku salama. Kai kuma duka kai ne mai laifin." Ta nuna Haidar da yatsa dan bata fa'din sunanshi.
    "Ina ruwanka da ita? Ko kuwa halin wulak'ancin naka da ake fad'i shi ne zaka fara a cikin gida? To wallahi kar na ji kuma kar na kuma gani. Ikram dai k'anwarka ce, dan haka ka kula da kyau ka kuma kama kanka. Shi dama babba in dai bai kama girmanshi ba to tabbas raini na tattare dashi a wurin k'annensa. Fin shekara Ikram ta ke zaune damu, ban ta'ba jin ko sa-in-sa ta shiga tsakaninta da d'an uwanka ba, saboda me? Saboda shi ya kare girmansa. Sam! Wannan halin naka ba daga garemu ka sameshi ba. Halin da mutum baya tab'a zama mai tawakkali, tun daga rasuwar k'anwarka ka tsiri hali da d'abi'un da ba naka ba."
    Sosai ran Haidar ya k'ara baci, tsaye ya yi har yanzu bai ce komai ba.
    Ikram cikin k'arfin hali ta ce "Momy dan Allah ki yafe min, wallahi it wasn't my intention. Tun a hanya Yaya Haidar ya ke fad'a min maganganu a waya son ransa kawai dan Ya Khalid ya ce min na d'auki wayarsa na ce yana tuki. A kan me Momy? Me na masa? Me nama Yaa Haidar da zan cancanci wannan tsanar haka? Kwata kwata fa yau muka fara had'uwa.." Duk'ewa k'asa ta yi kuka sosai ya ci k'arfinta.
    Kukan nan da ta ke ba k'aramin d'agawa Khalid hankali ya ke ba. Lallai mai haku'ri bai iya b'acin rai ba.
    Har k'asa ta duk'a ta rik'e hannun Khalid a hankali. Wani irin yanayi ya shiga mai wuyar fassarawa, ita kuwa ko a jikinta tun da ba da wata niyya ta yi ba.
   "Calm down yayana, ina saboda ni ne ka tayar da hankalinka har haka? In danni d'in ne to ka yi dariya please! Komai ya wuce kuma ka ba yayanka hak'uri."
    D'ago kanshi ya yi fuskar nan cike da damuwa, idonshi ya yi jajur kamar wanda ya kwana yana kuka. 'Wannan yarinyar wace irin zuciya gareta haka?' Ya tambayi kanshi.
   Murmushi ta masa had'e da d'aga kanta alamar 'ehh'.
   Bai san sanda shi ma ya yi murmushin ba ya mik'e tsaye kawai ya bar d'akin.
   Shima Haidar d'in d'akinshi ya nufa zuciyarshi cike da tsanar Ikram, ga takaicin abin da d'an uwansa ya masa, Khalid da ko bak'ar magana bata tab'a shiga tsakaninsu ba, shi ne kawai mai yaye masa damuwarsa a ko wane lokaci. Ji ya yi a zuciyarsa lallai bai ma Khalid adalci ba. 'To ko dai Khalid son yarinyar nan ya ke?' Ya tambayi kanshi. Rashin samun amsa ya sa kawai ya kawar da maganar, a zuciyarshi kuma tunani ya ke kamar ya santa, sai dai ya kasa tantance inda ya santa d'in, saboda ya san shi likita ne, ba abin mamaki ba ne dan san fuskarta tunda kullum ganin mutane daban daban su ke.

****
    Tun da ta shiga d'aki wani kukan ya sake kufce mata, lallai akwai babban aiki rayuwa a cikin wannan gidan.
    Kayan jikinta ta cire ta d'aura towel sannan ta shiga wanka, bata jima ba ta fito bayan ta d'auro alwala.
     Shiryawa ta yi tsaf cikin wata bak'ar atamfa java mai manyan zanen ganye red da green.
    Bata shafa ko powder ba barin a sa ran zata yi wata kwalliya.
    Ko d'an kwali bata tsaya ta d'aura ba ta sauko k'asa tare da k'irk'iro murmushi da taga Momy.
    Fuskar momy a sake ta ce "Ikram har an shirya?"
    "Na shirya momy." Ta fad'a tare da zama k'asa kusa da momy.
    Jawota momy ta yi ta kwantar a cinyarta ta d'an warware parking d'in da ta yi tana sosa mata gashinta.
    Wani irin dad'i ta ke ji sosai sai labarin makaranta ta ke bata. Sun yi nisa a labarinsu Ikram ta ce "Momy dan Allah ki yi hak'uri abin da ya faru d'azu."
    D'an 'bata fuska ta yi ta ce "Me fa? Wani abu ya faru ne?" Tana k'ok'arin basar da maganar.
     "Momy ina nufin abin da nama yaya Haidar, duk da baki nuna damuwa ba na san baki ji dad'in abin ba."
     "Ikram kanki ya b'aci da dundruff, daa kuma ban sanki da shi ba. Ko duk boarding d'in ce?" Momy ta fad'a tana k'ara bubbud'a gashin.
    "Momy ko zaman makarantar da muka yi na extension ai ya jawoshi. Wasa wasa fa mun dad'e a school." Ikram ta fad'a tare da sosa wani wurin alamun tana nufin momy ta sosa mata wurin.
     "Momy baki ce komai ba fa." Ta fad'a cikin shagwab'a.
    "To Ikram ni me zan ce? Fad'a ne tsakanin d'an uwa da 'yar uwa idan na shiga ma zan ji kunya." Ta yi murmushi.
    "Uhm, momy duk da rashin kunyar da na masa? Ko kina nufin na kyauta da abin da na yi?"
   Momy cikin k'osawa da maganar ta ce "Ikram ba zan ce kin kyauta ba, saboda rashin kunya bashi da amfani kuma kema ba zan so ganin k'aramarki ta rainaki ba. Amma shi ma Yayan naku bai kyauta ba, na tabbatar da inda ace bai miki ba kema ba zaki tab'a yi masa ba. Amma dan Allah gaba ki kiyaye! Ko wani abu na 'bacin rai ya miki ni ki sameni ki fad'a min kiga idan ban 'dauki mataki ba."
    Tashi zaune Ikram ta yi tare da d'aukar ribbon 'dinta tana 'kok'arin d'aure kanta ta ce "A yi hak'uri momy, insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba."
    "To ina fatan haka Ikram. Ai na san dama ba halinki bane. Yayanku mutum ne mai raha da son mutane yanda kika ga Khalid shima haka ya ke, amma daga baya ne ya koma haka kamar yanda na fad'a miki a baya, rashin Feenah ne ya miyar dashi haka, inda ace zaki koma masa tamkar Feenah da zai iya komawa asalin yayan naku."
    Baki Ikram ta tab'e, a ranta ta ce 'Ba kuwa zan ta'ba faranta masa ba. Kamar yanda ya bak'anta min, ya miyar dani marainiya shima haka nake fatan yaita zama har 'karshen rayuwarsa.' Ta yi wani shu'umin murmushi ta ce "Allah ya kyauta."
    "Amin." Momy ta fad'a fuskarta d'auke da murmushi.
   
****
     Khalid na kwance har yanzu zuciyarsa bata daina tafarfasa ba, motsin mutum ya ji babu ko sallama ya shigo, bai d'aga kai ba dan baya buk'atar kowa ya shigo a wannan lokacin.
    Ji yayi an dafashi a hankali ya juyo ya kalli yayanshi da ya k'ura masa ido yana kallo.
     "Haba bro! Kai yanzu fushi ka ke dani a kan wannan yarinyar 'yar k'auye?"
    Juya kanshi ya yi saboda takaicin kalmar da ta fito daga bakin Haidar.
    "Ka gafarceni idan na b'ata maka rai d'an uwana! In dai a kan wannan yarinyar ne bama zan sake shiga shirginta bama barin har na b'ata ma d'an uwana gudan jinina rai. Ko ka manta cewa kai kad'ai ka rage min yanzu? Na rasa Feena wacce har yanzu na kasa yafewa kaina a kan rashin gano wanda suka mata aika aika da na yi. Duk kud'ina kuwa na d'aukesu banza tun da sun kasa aikata min komai. Shisa na tsani kaina na tsani mutane baki d'aya in banda kai da momy. Ba wai intentionally na ke ma mutane wulak'anci ba, saboda abin da mutane suka ma Feenah..." ya yi saurin share hawayen da ke shirin fito masa.
    Tashi zaune Khalid ya yi ya kama hannun Haidar ya ce "Yaya wannan ba hujja ba ce wadda zata sa a ce wai ka tsani mutane. Mesa laifin wani zai shafi wani? Laifin mutane 'kalilan zai sa ka tsani duk mutanen duniya? Yaya wannan ba tunani ba ne, ka ajiye hankalinka ka k'ara tuna irin darajar d'an adam mana, Allah mad'aukakin sarki da kanshi ya ce 'Ya karrama d'an adam' sai kai ne zaka d'auki tsana ka d'aura masu? Ka canza tsari yaya!" Ya yi shiru daga nan.
    Shima yayan shiru ya yi kafin daga baya ya ce "Ni dai ka yi hak'uri a kan abin da ya faru kawai, ba wai wani dogon surutu na ke so ba."
    "Allah ya kyauta to. Shi ke nan ya wuce." Ya fad'a cikin halin ko in kula.
        Tashi ya yi daga nan ya nufi nashi d'akin, cike da farin cikin sun shirya da k'aninshi.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now