22

1.2K 73 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

22~ Tafe su ke daga School area ita da Miemie, rik'e ta ke da cup da cokali miemie kuma ta rik'o ledar corn flakes wanda ya kusa k'arewa.
    "Na matsu mu isa hostel d'in nan wallahi, yunwa na ke ji." Miemie ta fad'a.
    "Ke k'awata, wace irin yunwa kuma? Duka fa da break ne muka sha corn flakes." Ikram ta fad'a.
    "Uhm, sai ki yi fa, in dai ni ce, Allah duk abin da zan ci in dai ba mai nauyi ba ne to aikin banza ne. Kin ganni nan ko indomie bata rik'e min ciki ban d'auketa wani abinci ba. Ai ki bani tuwo ko shinkafa kawai, sai ko gari da k'anzo, duk wani gayu a barshi kawai. Ni na fi ganewa gargajiya." Miemie na gama fad'in haka Ikram ta d'an yi shiru, saboda tunowa da ta yi da rayuwarta ta baya. Ta ci k'anzo sosai, haka kuma ta ci gari kamar ba gobe, har sai da suka gundureta.
    "K'awata me ya faru kika yi shiru?" Miemie ta tambayeta.
    "Babu komai wallahi, na tuno da wani abu..." bata k'arisa maganar ba sanadiyyar wata banka da aka kai mata har sai da ta kai k'asa. Tana fad'uwa kuwa duka mutane suka saka dariya a daidai gate d'in hostel.
    Kasa tashi ta yi sai da miemi ta kamata ta mik'ar da ita tsaye, wasu irin siraran hawaye ne suka fito mata. Ganin ba zata iya k'watarwa kanta fansa ba ya sa miemie cire hijabinta ta d'aure a kug'u tare da finciko wadda ta bangaje Ikram.
     "Sholie ashe ma ke ce, wai ke wace iriyar bak'auyar yarinya ce? In banda k'auyanci miye na ki na damuwar mutum d'aya? Ita bata damu da ke ba, amma ke kin d'auki damuwarta kin d'aura a ranki. Miye haka ne? Ko dan kin ga bata magana? Allah hawainiyarki ta kiyayi ramarta! Ki kama kanki tun kafin na miki abin da sai kin yi kuka, kin ji na fad'a miki." Ta sakar mata hijabi. "Ku kuma na dawo gareku. Babu ko kunya kun wani washe baki kuna dariya. Ku baku ko kishin ganin 'yar uwarku mace ta fad'i k'asa amma kuke ta wani dariya? Ko da ya ke tunda wacce kuke tsoro ta aikata abin dole ku yi. Daallah ku ja can jakan banza!" Ta ja Ikram da k'arfi suka tafi.
    Abin mamaki babu wacce ta iya fad'in komai, duk da yake kuwa cewa ba wai mate d'insu kad'ai ba ne, har da 'yan SS3, da yake indai wurin masifa ne to miemie ba daga baya ba, ana tsoronta ta wannan dalilin, daga ita har smart, kuma sai Allah ya had'asu tare da Ikram, itama fa d'in kawai tana k'yalewa ne, dan bata so wani abu ya taso har Momy ta ji ta aikata wani abu na rashin jin magana, bayan kuma sai da ta mata nasiha kafin ta taho.
     "Ikram na sha fad'a miki cewa sai kin canja hali, rayuwar makarantar nan ta sha banban da inda kika yi, sun cika son rani idan ba'a yi taka tsan-tsan da su ba."
     "Miemie ke nan, ni kaina fa bana son raini, ina tuna wani abu ne kawai ya sa na ke raga masu."
    "Ke dai ake ji, ni wallahi halayenki suna min yanayi da na yayata, ita ma haka ta ke, tana zaune sai ayita guma mata kuma ta kasa aikata komai, mijinta kuwa komai yi mata ya ke, babu kalar k'etar da baya mata. Ke a k'arshe ma muguwar cutar nan da ake gudu ya jajib'o mata. Ita kishiyarta da ya ke mai kishin kanta ce sai raba aurensu aka yi, ita kuwa tana nan har yanzu, gata dai barrister ta iya kare wasu amma ita ta kasa kare kanta."
    "Allah ya kyauta." Ikram ta fad'a.
     "Ameen." Miemie ta ce a daidai isarsu d'akinsu. Bene suka hau, a daidai second floor suka had'u da smart zaune wata matron na mata kitson hannu. Ganinsu da ta yi yasa ta fizge kanta tana fad'in "oyoyo k'awayen albarka. Na yi missing d'inku wallahi."
     "Muma mun yi sosai, zazzab'i ya yi sauk'i ko?" Ikram ta fad'a.
     "Zazzab'i kam ya yi sauk'i sosai, har ma na maku girki. Mama bari na je zan dawo sai mu ci gaba." Ta fad'a tare da binsu suka nufi d'akinsu.
     Bayan sun zauna ne Miemie ke ba smart labarin abin da sholie ta ma Ikram da kuma yanda mutane suka hau yi mata dariya. Sosai ta ji haushinta, ta kuma k'uduri aniyar idan sholie ta zo ita ma sai ta wanketa tas da soso da sabili.

*****
     Momy ce ke ta kai da kawowa, shige da fice saboda gobe visiting. Ta yi waya da Hajia Hinde ta bata Ikram suka gaisa, sannan ta tambayeta abin da ta ke so ta kawo mata idan zata ziyarceta.
    Misalin k'arfe goma na safe ta gama komai, har da miyar kaza ta soya mata, ta mata dambun naman sa da sauran abubuwan da d'alibi zai buk'ata.
    Khalid ne ya fito sanye cikin k'ananan kaya, bak'in jeans ne da jar t shirt plain, pick up bak'a ya saka ta channel. Sosai ya yi kyau. Ya sameta zaune a kan d'aya daga cikin kujerun falon tana jiransa.
   Ganinsa da ta yi yasa ta fad'in "Kai yanzu Khalid zamu yi tafiya shi ne ka rasa kayan da zaka sako sai k'ananan kaya? Tafi ka canzasu yanzu ina jiranka."
     K'yak'k'yaftu ya ringa yi da ido, bai tafi ba sai cewa da ya yi "Allah momy ba wata matsala. Ni fa Government property ne (corper), in dai zan yi tafiya da ID card d'ina babu abin da zai faru. Kwantar da hankalinki kin ji? Ina missing d'in d'an uwana ne shisa na saka rigarsa." Ya mata murmushi.
     "Allah ya shiryeka Khalid, wallahi ka rainani, ka gano wurin kwanana." Ta fad'a tare da gyad'a kanta.
    "Momy ke nan, dama ai na san inda kike kwana, ba a d'akinki ba ne, a kan gadonki?" Ya fad'a yana dariya.
    Bata fad'i komai ba sai murmushi da ta yi, ita kanta idan Khalid ya yi wani abun bata da yanda zata yi da shi, halin zaulaya kam ya riga ya auresa.
     Kayakin ya hau kwashewa yana kaisu mota. Sai da ya kwashe duka sannan ya kira Momy, bankwana ta ma mai aikinta sannan suka kama hanyar Birnin Kebbi.
 
***
    Tsaitsaye su ke a daidai inda aka tanadar masu domin ranar visiting, suna zama wurin ne saboda duk wacce danginta suka zo su ganta, tun da fili ne babba, babu wuya mutum ya ga d'an uwansa.
     Ikram ta ce "Na matsu na ga momyna, na yi kewarta sosai ita da Ya Khalid."
    Da fara'a k'unshe a fuskar miemie ta ce "Ai kam nima na matsu na ga wannan Ya Khalid wanda kullum kike damunmu da shi."
    Smart ta ce "Ehh mana, barinma yanda ta ke fad'in d'an son a yi wasa da dariya ne."
    Suna cikin wannan maganar ne miemie ta hango yayarta rik'e da hannun y'arta. Fizge hannunta ta yi daga hannun Ikram da ta rik'e, a guje ta isa inda ta ke.
    "Ya Kareema, Oyoyo!" Ta fad'a had'e da d'aukar 'yar yarinyar.
     "Khairat 'yata, inyee, yarinya ta girma." Murna fal a fuskarta.
    A daidai nan su Ikram suka iso inda su ke. Gaishe da yayar miemie suka yi da fara'a Ikram ta mik'a hannu zata karb'i Ummul-khair, k'in zuwa ta yi har tana neman yin kuka.
     "Khairat fa akwai k'yuya, idan bata san mutum ba bata tab'a zuwa wurinsa." Miemie ta fad'a tana kallon khairat da fara'a.
     "Yaya Kareema ya aiki?" Smart ta tambayeta.
    "Aiki Alhamdulillahi Halimatu, ya karatu? Ya kuma masifar miemie, hala tana nan tana yi?"
    "Ya Kareema wannan zamanin fa yi min na maka ne, idan halin mutum hak'uri to yana ji yana gani za'a cuceshi, mutumin yanzu bai san abin arzik'i ba." Smart ta fad'a tare da tab'e bakinta.
     "Ai ke kam Yaya Kareema halinki sai ke, a haka ne kike son na yi koyi da halinki? Allah ba zan iya ba, kowa ya je ya rainani. Amma a haka fa? Kowa shakkun tab'oni ya ke, babu mai son ya tab'ani dan sha yanzu magani yanzu na ke, daga ni har smart. Amma kin ga wata 'yar uwarki nan." ta gwada Ikram. "Ita ma ha'kuri gareta kamar ke, saisa kowa ya rainata, daga zuwanta aka fahimci halinta, aka d'auki raini kuwa aka d'ora a kanta. Har juniors d'inmu ma sun rainata."
     "Yar albarka ke nan, haka ake so Ikram, kar ki bi ta wannan k'awayen naki. Mahak'urci mawadaci ne, mai hak'uri ya kan dafa dutse har ya sha romonsa.." bata ko k'arisa maganarta ba Miemie ta ce "Allah ni kam sai dai kar na sha romon in dai na dutse ne. "
    "Allah ya shiryeku to." Ta fad'a bayan sun iso mazauninsu. Smart ta ce da Ikram "mu mu koma kar a zo mana kuma ba'a ganmu ba, miemie ki shimfid'a kafet d'in na san zai ishemu mu duka kafin mu dawo." Suka kama hanyar tafiya.
        Suna isa kuwa Ikram ta hango Khalid hannunshi rik'e da babbar leda, sai d'ayan hannun da cooler. Momy kuma ta rik'o k'aramar cooler da hannu d'aya, sai hand bag d'inta a d'ayan hannun. Da gudu kuwa Ikram ta isa inda su ke, cooler'n hannun momy ta karb'a ta ajiye k'asa sannan ta rungumeta cike da farin ciki. Ta ma rasa abin da zata yi, dariya zata yi ko kuka? Sosai ta yi kewar momy'nta.  Sai yanzu ma ta kula da Khalid da ya yi sak'ak'a yana kallonta.
     "Yayana na kaina. Ashe tare kuke?" Ta fad'a tana masa dariya tare da jiran amsarsa.
      "Dama ina zaki san da ni kina wannan haukan? Ke a dole kin ga uwa ko? Allah ko ki saketa ko na kwad'a miki ledar nan."
     Dariya tayi har da shewa. "D'an bak'in ciki, kai yanzu ko irin tarbar nan ma ta ka nuna ka yi kewata babu?"
     "Kewarki a ina? Waye ya fad'a miki na yi kewarki?" Ya fad'a.
      "Kai Khalid fad'a mata gaskiya. Kai ne fa kullum baka da magana sai ta Ikram, tun yaushe kake fad'in zaka zo ka ganta ina baka hak'uri har ranar visiting? Shi ne yau ka ganta kake wani basarwa ko?" Momy ta fad'a tana masu dariya.
      Murmushi ya yi shima, "momy wasa fa na me miki, wannan naughty girl d'in ce zan yi kewarta?"
     A daidai nan smart ta iso, gaishe da momy ta yi sannan ta ce "ke ni ai ban san tahowarki ba, Ina can ina kllon su sholie ashe har kin gudo? Sannunku da isowa momy." Ta fad'a tana murmushi.
     "Momy wannan ita ce halimatu, k'awayena da na baki labarinsu a waya, aminatu kuma tana can da family'nta. Wurinsu zamu je yanzu."
     "Allah sarki! Sannu 'yata. Ya karatu?"
     "Lafiya k'alau momy. Ya Khalid ya hanya?" Ta fad'a had'e da kallon Khalid tana murmushi.
      "Ke ku kuma duka haka kuke? Inna lillahi! Yara jiki kamar ana d'iba ana miya dashi? Kai ku fad'a min gaskiya, ko dai namanku ake yanka ana maku girki kuna ci?"
       Dariya sosai smart ta yi har da dafe ciki. "Kai dan Allah ya Khalid, abin da ma zaka fad'i ke nan?" Smart ta fad'a.
      "Kad'an daga aikin wannan mugun ke nan." Ikram ta fad'a tare da tafka masa bugu a baya.
      Su duka suka saka dariya. Kai tsaye suka nufi inda miemie ta ke. Suna isa kuwa miemie ta yi saurin tashi tsaye fuskarta d'auke da murmushi.
       "Sannunku da isowa. Uhm, kun ga Ikram baki ya kasa rufuwa." Miemie ta fad'a.
     "Ehh na ji dai, ai da ya ke ke naki bakin ya rufu." Ta bata amsa.
       Bayan momy da khalid sun zauna Kareema ta gaishesu. Kallon Khalid da ta yi ya sa ta tuna wani abu, ko miye oho. Basarwa ta yi ta ce "kun sha hanya, kuma daga Sokoton kuke ne?"
    "Wallahi kuwa daga Sokoto mu ke, baby." Momy ta kama hannun Ummul-khair.
      "Khairat baki iya gaisuwa ba ne?"
       Baki Khairat ta bud'e ta ce "Good morning....laahh Mami, bamu sha maganinmu na safe ba kin manta." Ko a jikinta yanda ta yi maganar.
      Kareema ji ta yi kamar ta nitse k'asa, surutun Khairat ya yi yawa, ta rasa yanda zata yi da ita. Kuma gaskiyanta ne, basu sha maganin ba, amma dama sai k'arfe sha biyu na rana ya kamata su sha, saboda jiya na dare ba da wuri suka sha ba, saboda sun fita ne sai late night suka dawo, maganin kuma an fi so ya daidaitu lokacin shanshi.
      "Khairat ai kin warke da zazzab'in ko? Ba zaki kuma shan maganin ba."
      Duk k'yuyar Khairat sai da ta rungume Ikram da ke kusa da ita. Cike da farin ciki ta ce "Aunt kin ga mami ta ce ba zamu sake shan magani ba. Kuma daa ta ce ba zamu daina sha ba har sai mun mutu."
     "Khairat akwai surutu. Allah ya shirya min ke." Miemie ta fad'a, saboda ita ta san inda zancen khairat d'in ya dosa, ikram ma ta d'an fahimta kad'an.
     Fira sosai suka ci gaba da ita, saboda family'n smart ma sun zo, ita dama 'yar nan cikin garin Birnin Kebbi ne, amma duk da haka basa zuwa mata visiting da wuri, saboda akwai 'yan uwanta da su ke wata makarantar, duk sai an jejje masu.
     Duk wannan firar da ake ita kam miemie hankalinta na kan Khalid, tunani ta ke inda ta sanshi, ko da ba shi ba to ta san wani mai kama dashi, kuma mai kama da shi d'in yana da muhimmanci sosai a rayuwarta.
     Ita kanta Kareema tana tunanin ta tab'a ganinshi. Amma kuma a ina? Ta tambayi kanta. Rashin samun amsar tambayarta ya sata saurin kawar da maganar tare da ci gaba da firarsu.
     Suna nan har aka yi azahar a nan suka yi, Khalid da wani yayan smart kuwa masallaci suka nufa, a lokaci kad'an har sun zama abokai.
       Sai yamma lik'is sannan suka fara haramar tafiya. Sai da momy da kareema suka yi musayar lambar waya, saboda d'an zaman da suka yi  tare har sun shak'u. Gasu kuma 'yan gari d'aya ne.
     "Maman Khairat mu zamu wuce, insha Allahu zan kiraki, zan zo har gida na kawowa jikata Khairat ziyara."
    "Ai momy ba ma zaki rigani zuwa ba, ni zan fara zuwa da yardar Allah." Kareema ta fad'a.
      "To 'yata, Allah ya baki iko. Allah ya miki albarka. Khairat ki gaishe min da Abbanki." Ta zaro kud'i 'yan d'ari biyar guda hud'u ta mik'awa khairat.
     "Abbana baya zuwa gidanmu sai ya ga dama. Amma bari duk ranar da ya zo zan gaishe miki da shi." Ta fad'a ko a jikinta tare da mik'awa momy kud'in da ta bata. "Mami ta hanani karb'ar kyauta from the stranger."
     Duk da mamakin da momy ta yi a maganar Khairat ta farko bai hanata murmusawa ba ta ce "am not a stranger, ai kin ga inata fira da maminki ko? Alamun ta sanni ke nan. Idan baki karb'a ba zamu b'ata." Ta d'an d'aure fuska.
    Kallon maminta ta yi sannan ta kalli momy, ta sake kallon maminta a karo na biyu. Murmushi kareema ta mata tare da d'aga mata kai alamar ta karb'a. Karb'a kuwa ta yi da godiya sannan suka tafi.
    Har da kuka Ikram ta yi, Khalid sai dariya ya ke yana kwaikwayon yanda ta ke kukan. Su smart kuwa dariya kawai su ke, inda sabo su kam sun saba da azo a barsu.
     Ana kiran magrib sannan suka kama hanyar komawa hostel. Hannayensu rik'e da ledojin da aka kakkawo masu. Zuciyar miemie cike da tambayoyi. Ta k'osa su isa hostel ta ma Ikram wannan tambayiyin.
      Ko wane irin tambayoyi ne zata mata oho. Nima dai biye na ke da su, na k'osa na ji wannan tambayar. Sai dai kuma kash! Ruwan birona ya k'are, dole sai na ruga da gudu na siyo wata sannan zan ci gaba.

****
   Nagode k'warai masoyana. Allah ya bar zumunci da soyayya.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now