50

1K 51 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

50~  Haidar ne tafe yana tuƙi cikin kwanciyar hankali. Waƙar da Ikram ta saba ji ko yaushe ya kunna yana ɗan bi a hankali. Wani irin shauƙi ya ke ji yayin da ya ke sauraron waƙar. A haka har ya iso bakin gidan television na garin Sokoto.
   Kai tsaya ciki ya nufa, nan ya faɗa masu abin da ya ke so a masa. Kuɗin da zai biya suka faɗa masa nan take kuwa ya basu.
   Gaba ya yi suka mara masa baya da motarsu wadda ta ke ƙunshe da wasu daga cikin kayakin aikinsu.
     Misalin goma na safe ya isa gida. Ikram dai ko makaranta bata tafi ba dan tana son ganin abin da Haidar zai yi.
    Yana isowa yasa su Shehu suka fitar da ƴan fashin ƙofar gida suka ɗaure su a jikin falwaya a yanda suken a haɗe basu tsaya rabasu ba.
     Nan fa mutane ƴan unguwa suka fara zagaye su har da almajirai kowa da abin da ya ke faɗi game da mutanen, duk da taƙamaimai har yanzu basu ji dalilin da yasa aka ɗaure su hakan ba.

***
   Bayan Haidar ya shiga ya fito da su momy, sai sojoji biye da shi ya iso waje wurin ƴan jaridar.
    Kunna kayan aikinsu suka yi sai ga Khalid kanshi naɗe da bandeji duk jini da hannuwanshi na jini kai ka rantse da Allah ciwukan gaske ne.
    Nan fa aka haskashi da camera a gaban ƴan fashin sai sojoji zagaye da shi nan ya fara koro bayani. "A daren jiya ne wasu ƴan fashi suka shigo har cikin gidanmu cikin ɗakina, inda suka same ni suka fara duka, ina tambayarsu ko da abin da suke nema a wurina amma suka shaida min da basa son ko sisina, rayuwata kawai su ke so. Duk da abin ya bani tsoro amma a haka na daure na tambaye su abin da na masu yasa su ke neman hallakani amma suka ƙi faɗa min. Allah ya sa akwai sojojin da ke gadinmu wanda ba kowa ne ya san dasu ba, sai gasu kwatsam Allah ya jefo, nan fa suka samu damar harbin wani a hannu wanda har ya saita bindigarsa zai harbe ni, Allah yasa da tsawancin kwanana. Ga dai ƴan fashin nan zaku ji daga bakinsu."
   Miyar da saitin cameran aka yi gare su, inda Ogan nasu cikin rawar murya da tsoro ya fara koro bayani. "Kwanaki muna zaune ne Alhaji Kallah ya kirani a waya,  saboda dama na saba yi masa aiki ni da yarana. Bayan na ɗauka ya ce yana son ganina, na ji daɗi sosai saboda na san samu ne tun da har ya ce na same shi a guest house ɗinsa.
    Ko da muka je ya ce mana akwai wanda ya ke so mu kawar, amma ba a ranar ba saboda za'a iya zarginshi idan muka tafi ranar. So ya ke mu kashe shi kuma mu ɓatar da shi baki ɗaya, saboda a baya yasa an sace shi amma bai san ya aka yi ya kuɓuta har ya dawo gida ba. Ya mana bayani cewa wai kuɗaɗensu na gado da yawa suna hannunshi, kuma kusan duk ƙarfin dukiyarsa ma tashi ce, har ma da wanda su kansu su Khalid ɗin basu sani ba. Wai shi ne Khalid ɗin ya je ya ce kuɗinsu su ke so. Shi ne ya ke so kawai a kawar da shi tun da shi ya fi zaƙewa, shi kuma yayan nashi idan ya sake tayar da maganar shima sai mu aikashi lahira, ya san daga nan mahaifiyarsu ba zata sake maganar kuɗin ba shi ke nan ya yi nashi. Naira miliyan ɗaya ya bamu saboda wannan aikin kawai, sai gashi Allah bai sa zamu mori kuɗin ba..." Kuka ya ci ƙarfinsa.
    Nan fa mutanen da suka zagaye wurin suka hau mamakin kalaman mutumin. Lallai mutanen yanzu abin tsoro ne, Khalid kam ya tsallake rijiya da baya baya.
    Haidar ya karɓi micro phone ɗin shima ya fara nashi bayanin. "Ina fatan mutane sun saurari bayanan ɗaya daga cikin ƴan ta'addan da Alhaji Kallah aminin mahaifinmu ya turo gidanmu domin su kashe ɗan uwana ko in ce su ɓatar da shi. Wannan sai ya zama ishara ga mutane su daina nuna yardarsu ɗari bisa ɗari ga mutane. Alhaji Kallah sai ka zama cikin shiri, domin kuwa sammaci na nan zai zo gare ka, ka fiddo mana kuɗinmu sannan ƴan sanda su san yanda zasu yi da kai."
    Black ne ya karɓa shima ya yi nashi bayanin. "A duk bayanan da suka yi babu ƙari ko kaɗan, kaf abin da suka faɗa babu abin da ba'a yi ba. Kuma babu maganan ƴan sanda a wannan maganan, magana hannun sojoji ta ke, dan haka mu muke da daman aiwatar da abin da muka ga dama ga Alhaji Kallah, su dai su shigar da maganar kotu ya basu haƙƙinsu sannan mu karɓa maganar." Ya miƙawa mutumin micro phone.
   Kashe kayan aikin suka yi sannan suka yi bankwana da Haidar, ya masu godiya sosai sannan suka tafi, su kuma suka koma cikin gida, inda Haidar ya ba sojoji kuɗi amma fir fir suka ƙi karɓa, black ya ce "Oganmu ya turo mu mu maka aiki kyauta ba dan kuɗi ba. Kuma yau gashi mun yi mun gama zamu tafi. A duk lokacin da wata buƙata ta taso wadda kuka san zamu iya yi maku amfani kawai ku kiramu. Insha Allahu zamu ci gaba da taimakonku bakin ƙarfinmu, saboda babu abin da Oga Marwan baya mana na kyautatawa, shiisa duk sanda wata buƙata tashi ta tashi mu ke aiwatar da ita bakin ƙarfinmu."
    Hannu Haidar ya basu suka gaisa sannan ya ƙara yi masu godiya sosai, shi da kanshi ya basu motarshi suka tafi da ƴan fashin a ciki, da niyyar zai zo da kanshi ya karɓa motar ko dan ya yi wa Marwan godiya duk da kullum yana masa a waya.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now