62

856 51 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

62~  A gajiye liss suka koma gida, a lokacin har an yi sallar magrib a wasu masallatan.
    Suna shiga Mama ta ce "Sannunku da isowa. Mu ai tun ɗazu muka dawo."
   Ikram ta ce "To sannu fa Mama, Allah na gaji ba kaɗan ba."
   Mama ta ce "Allah sarki! Ai Ikram dama haka abin ya ke, amarya ta gaji wannan. Sai ki samu ki ɗan watsa ruwa sannan ki kwanta da wuri. Kar ki biye ƙawayen nan naki su hanaki bacci."
   Murmushi suka yi su duka, sannan suka ahige cikn ɗaki, Juwairiyya da Miemie ne suka wuce ɗakin Kareema, sai Ikram, Husna da Khaleesat kuma a nan ɗakin miemie suka tsaya.
   Salloli suka fara gabatarwa banda Ikram da tana shiga ban-ɗaki da nufin yin alwala ta ga baƙon lamari ya iso mata.
    Fasa alwalar ta yi kawai ta yi wanka sannan ta fito ɗaure da pink towel wanda suka haɗo cikin kayan lefenta.
    Tana fitowa ta warware yalwataccen gashin kanta, bakin madubi ta isa ta fara shafa mai sannan ta feshe ko ina na jikinta da turaruka kala kala.
     Husnah na gama sallah ta ce "Ikram sallah fa? Kin san magrib ƙaramin lokaci gare ta, da kin bari har ki yi sallar sannan duk abin da zaki yi ki yi."
    Murmushi Ikram ta mata ta ce "Na ɗauki hutu ƴan mata."
     "Hutun aure?" Miemie ta tambaye ta.
    "Hutun sallar dai. To ina nufin baƙona na wata wata ya zo." Ta yi dariya a hankali.
    Zama Miemie ta yi ba tare da ta shirya ba ta ce "Iyee! Lallai wannan baƙo bai kyautawa ango Aliyu ba. Gaskiya sai na kai ɗararsa wurin ango dan ya sani tun yanzu kar ma ya siyo kazar siyan baki."
   Dariya suka sake su duka, ita kanta Khaleesat ta ɗan fahimci inda zancen ya dosa, saboda a ɗan zamanta da su tana ɗan tsintar maganganu na hausa wanda ba za'a rasa ba.
     "Ni kam ai daɗin hakan na ji. Allah da na gani baku ji yanda raina ya yi fari ba." Ikram ta faɗa tana sharce gashinta.
     Husnah ta ce "Ke banza ce ai, baki san irin haka saurin samun ciki ake ba?"
     Baki Ikram ta tunzuro ta ce "Hm uhm! Waye ya faɗa maku zai yi ciki? Ni fa ustaziya ce."
     Har bib-biyu Miemie da Husnah ke mata, Miemie kam haske ta ta yi da fitilar wayarta duk hasken da ke akwai a ɗakin ta ce "Dan Allah mu ga fuskarki sosai. Baki ma da kunya yarinyar nan."
    Ikram ta ce "Kuna ganin kamar da wasa ko? To ba ma a ɗaki guda zamu ringa kwana ba, shi yana ɗakinshi nima ina nawa ɗakin."
   Kai kawai Husnah ta gyaɗa tana dariya ta ce "Irinku masu cika bakin nan kun fi kowa azarɓaɓi, wata ƙila nan da wata tara cif sai haihuwa."
   Dukan wasa Ikram ta ɗika mata. Suka ci gaba da dariyarsu har isha'i ta yi suka gabatar da ita.
    Tun ƙarfe tara Ikram ta kwanta bayan ta saka kayan bacci wai zata yi bacci, aikuwa su miemie suka ce basu san da wanann ba. Hanata baccin suka yi da zaulaya da barkwanci har kusan sha biyu na dare sai ga kiran Haidar ya shigo a wayar Ikram.
    Cike da mamaki ta sake duba sunan mai kiran nata *Yaa Haidar* ta gani a bayyane hakan yasa ta yi saurin ɓoyewa dan kar miemie ta duba sunan, tun da har yanzu Miemie'n bata koma ɗakin da zata kwanta ita da Juwairiyya ba, ita kam tuni ta yi bacci abinta.
    Sake kira ya yi a karo na biyu, Husnah ta ce "Ikram kina ji fa wayarki na ringing."
   Guntun tsaki ta yi haɗe da ɗauka ta kara a kunne.
    "Ke sai kin gama jan aji sannan ki ɗauki wayar?" Ta jiyo muryar Haidar ta daki kunnenta.
     "Ba fa jan aji ba ne. Wayar bata kusa da ni ne." Ta faɗa cikin murya ƙasa ƙasa.
    "To ya yi kyau. Ki kai wa momy wayar ina ta kiranta shiru bata ɗauka ba. Kuma na san ba barci ta yi ba." Ya faɗa wanda ko kaɗan ba hakan ba ne, gama wayarshi da momy ke nan ta shaida mashi da su Ikram sun koma gidan su miemie da zama, shi kuma yana son jin muryarta shiisa ya shirgo wannan ƙaryar.
    "Ni fa Yaa..." Ta yi saurin doɗe bakinta daga nan saboda kallonta da miemie ta yi.
   Saurin ƙirƙiro murmushi Ikram ta yi ta ce "Yallaɓai ina gidan su Miemie fa. Nan muka koma da zama saboda mutane can ɗin. Yaa Haidar ma ya bar gidan tun shekaran jiya. Ka san yaa Khalid dama ya tafi Qatar karatu."
   Shiru ya yi dan bai san inda zancen nata ya dosa ba.
   Sake jin muryarta ya yi ta ce "Ai nan ɗin ma lafiya lau. Ka san ƙawayen nawa akwaisu da kula. Kar ka damu zasu kula maka da ni. Good night Zaujee." Ta kashe wayar cike da takaicin ahin da ta yi, sai dai kuma bata da zaɓin da ya fi haka.
   Miemie ta ce "Ai da kin sani ki banishi in bashi labarin abin da kika faɗa ɗazu."
   Ikram ta ce "Allah ya fiki ai, muguwa." Ta mata gwaliyo.
   Husnah ta ce "Kai ni dai fa na fara jin bacci. Oya, miemie koma ɗakinku, ki kashe mana wutar daga nan."
   Miƙewa miemie ta yi ta ce "Dama nima baccin nake ji ai. Barin tafi sai Allah ya kaimu."
    "Saura kuma a tashe ni sallar asuba tun da dai an san hutu na ke." Ikram ta faɗa bayan ta kwanta daga tsakiyar gado.
    "Allah zaki ja in tashe ki tun kiran sallar farko. Kuma dolenki ki tashi sanda kowa zai tashi yarinya." Tana faɗin haka ta kashe masu wutar tana dariya ta fice.

SHI NE SILAH!حيث تعيش القصص. اكتشف الآن