41

978 58 0
                                        

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Wannan shafin sadaukarwa ne ga my dear *Asma'u Umar,* you mean alot to me, thanks for being there for me. ILYSM_

41~  Zaune ta sameta Khairat kwance a cinyarta tana d'an bubbuga bayanta. Da fara'a ta tarbi Ikram tare da bata izinin zama, sai da ta zauna sannan ta gaisheta ta amsa cikin sakin fuska.
    "Me ya faru, Khairat ba lafiya ne?" Ikram ta tambayi Kareema.
    "Wallahi kuwa Khairat ba lafiya, ita dama haka zazzab'inta ya ke, ga 'kurajen baki da ya ke sakar mata, saisa ma ban je Office ba yau." Ta bata amsa tana d'an 'kara tab'a jikin Khairat da ya yi zafi rau.
   Cike da tausayi Ikram ta ce "Allah sarki! Allah ya baki lafiya Khairatuwata. Sannu kin ji?"
    "Ya kika baro gidan? Su momy lafiya su ke ko?" Kareema ta tambayeta cikin kulawa.
    "Lafiya k'alau ta ke, bama ta san zan zo ba ai na san da ta bayar da sak'o an kawo miki. Yaya Kareema kar dai a gaji da ni, wani taimakon na ke nema please."
    Murmushi Kareema ta yi ta ce "Ba zan tab'a gajiyawa da ke ba Ikram, kema d'in ai k'anwata ce kamar miemie."
    "To na gode k'warai. Dama a kan maganar wanda suka sace Yaa Khalid d'in nan ne..."
   Tun bata gama ba Kareema ta ce "An kamasu ne?"
    "Ba'a kamasu ba Yaya, shawara dai na ke so ki bani ta hanyar da zan bi wurin gano ko su waye da kaina ba sai 'yan sanda sun saka hannu ba, dan kar ma su b'ata min plan."
    "Hmm! Akwaiki da 'kok'ari Ikram, zuciyarki mai kyau ce wallahi. Insha Allahu kuwa zan baki shawara duk sanda wani abu ya shige miki duhu. Yanzu dai ke wa kike zargi?"
    D'an shiru Ikram ta yi na wani lokaci kafin ta ce "Bana zargin kowa saboda Yaa Khalid bashi da abokin fad'a, saisa ma kika ga na zo dan neman shawararki."
    Shirun itama ta yi na wani lokaci kafin ta ce "Ko a cikin abokananshi bakya ganin akwai wanda zai iya yi masa haka?"
    "Gaskiya bana tunanin akwai yaya Kareema." Ta bata amsa.
    "To ko bak'ar magana baki tab'a jin ta shiga tsakaninshi da wani ba?"
   Nan ma dai shiru ta yi kamar tana son tuno wani abu sai dai kuma ta kasa tuna koma menene.
    "Yanzu dai ki je ki 'kara nazari sosai, nan da kwana biyu sai ki kirani mu had'u, insha Allahu zaki samu nasara kar ki ji komai, ke jaruma ce." Ta mata murmushi, ta k'ara da "Kyanki a ce ki zama barrister."
     Murmushi Ikram ta yi ta ce "Ai science na karanta, kuma likita na ke burin zama."
    Murmushi itama Kareemar ta mata ta ce "Hakan ai yana da kyau, duka dai taimakon al'umma ne. Allah ya taimaka ya baki sa'a."
    "Ameen yaya Kareema. Bari na wuce ni dai." Ta mi'ke, dafa jikin Khairat ta yi ta ji zafi sosai, ido bud'e ta ce "Yaya Kareema an kai yarinyar nan asibiti kuwa?"
    Mirmushin k'arfin hali ta yi ta ce "Ban kaita ba Ikram.."
    Da mamaki Ikram ta ce "Saboda me?"
    "Akwai maganin da ta ke sha dama."
   Kai kawai ta jinjina tare da yi ma Khairat fatan samun sau'ki ta tafi, Kareema ta so ta rakata amma ta ce ta gode saboda Khairat a jikinta ta ke.
    A parlor ta tarar da shi, sai da gabanta ya fad'i da wani irin kallo da ya ke binta da shi, cikin k'arfin hali ta ce "Kawu na tafi. Sai anjima." Ta yi saurin fita.
   Bin bayanta ya yi har ta k'arisa fita daga 'dakin, a compound kafin ta k'arisa inda motarta ta ke ya yi saurin cin gabanta. "Ya tafiya da sauri haka Ikram? Ko wani abu yayar taki ta miki ne?" Ya tambayeta.
    Cike da 'kosawa ta ce "Ni babu abin da ta min." Tana yi tana tafiya har ta k'arisa inda motarta ta ke.
   "Da alama dai Ikram bata son yin magana da ni, dan Allah mana ki saurareni." Ya fad'a da wani shu'umin murmushi.
    Banza ta masa tana k'ok'arin rufe mota.
    "Dan Allah ki saka min lambarki a nan mana, akwai muhimmiyar maganar da nake so mu yi da ke ne." Ya fad'a had'e da mik'a mata wayarsa.
     'Kara tsuke fuskarta ta yi ta ce "Dan Allah ni dai ka 'kyaleni na tafi. Ina da abin yi."
    Ci gaba da naci ya yi a dole ta karb'a ta saka masa ko dan kar Kareema ta fito ta samesu a haka, sai da ya kira ya tabbatar daidai ta saka masa lambar sannan ya tafi yana mata godiya sai murmushi ya ke.
     Tada motarta ta yi had'e da yin reverse ta fita daga gidan cike da jin haushin wannan bawan Allah, ita wallahi tausayin Kareema ma ta ke, dan sam bata yi sa'ar miji ba.
    Kai tsaye gida ta nufa, bata samu kowa a parlor ba ta zarce zuwa d'akinta, kayan jikinta ta rage sannan ta d'an kwanta saboda ta gaji, wankan ma sai da ta huta sannan ta yi.
    K'arar text message ta ji a wayarta, guntun tsaki ta yi ha'de da fiddota daga cikin jakarta. Duba text d'in ta yi nan ta ci karo da transfer ta dubu goma daga wata number.
    "Who is that?" Ta tambayi kanta.
   D'aga kafad'a ta yi ta ce "Zan miyar dashi ne, wata k'ila mistake ne."
    Kud'in ta miyar ga lambar da aka turo mata d'in, amma da mamaki sai gasu an sake turowa.
    "A'ah, wai waye ne wannan?" Ta sake tambayar kanta.
   Kafin ta samo amsar tambayar ta ji an korata da lambar, sai da ta kusa tsinkewa sannan ta d'aga da sallama.
    "Ikram..." Ya fad'a a hankali.
    Da jin haka ta gane ko waye, cikin takaici ta ce "Miye?"
    "Ikram ki bi a hankali dan Allah, ni fa da alkhairi na ke nufinki." Ya fad'a had'e da guntun murmushi.
    "Alkhairin me? Dan Allah mallam ka shafa min lafiya." Cike da tsiwa ta yi maganar.
    Burgeshi ta yi duk da haka ya ce "Zan shafa miki lafiya Ikram, amma dan Allah ki tsaya ki saurareni."
     "Ina jinka." Ta sake fad'i cikin fad'a.
    "Ba zan b'oye miki komai ba, tun ranar da na fara ganinki na ji kin kwanta min a rai, na ci burin had'a auratayya da ke, ki amince min dan Allah, aurenki na ke son yi."
    Tun da ya fara maganar ta ke tunanin ta hanyar da zata fara yi masa rashin mutunci.
    Dakewa ta yi cike da masifa ta ce "Mallam ina shawartarka da tun wuri ka fita harkata, ni ban iya cin amana ba, banda abinka ina ni ina kai? Yaya Kareema na d'auketa tamkar yayata ta jini. Kana tunanin zan iya cin amanarta in auri mijinta ne? Allah ya kyauta min." Ta buga tsaki, tana jinshi yana 'kok'arin magana amma ta dakatar da shi ta hanyar fad'in "And finally, kar ka sake kirana a waya." Ta kashe wayarta cike da takaicin wannan bawan Allah'n, shi ko ma kunya bai ji ba, lallai maza ba kowane ya ke da kunya ba.
     Kamar an ce ta tsinke kiran sai gashi wannan wadda ta kirata d'azu ta sake kiranta, d'auka ta yi ta ce "Idan kin san magana zaki min a kan bayar da number'na please kar ma ki min."
    "Am sorry ma, mutumin yana wajena right now, wai yana son magana da ke ne urgently.." matar ta fad'a cikin hausarta da bata gama gwanancewa ba.
     "Please leave me alone, ki fad'a masa kar ya sake zuwa shagonki." Ikram ta fad'a. Bata ji muryar matar ba sai ta namiji ta ji ya ce "Dan Allah Ikram ki saurareni, wallahi magana ce ta k'aruwa, idan har kika tsaya kika saurareni zaki ji dad'i.."
     Tun bai gama maganar ba ta ce "Minti d'aya tal na baka ka fa'di koma menene, idan kuma ba mai muhimmancin ba ne kar ma ka yi tsammanin zai iya sauraraka har tsawon minti d'ayan."
    Ajiyar zuciya ya sauke ya ce "Sunana Jibo, abokin Bash Osca.."
    Tun bai gama maganar ba ta ce "Ina jinka"
     "A kan maganar d'an uwankin nan da aka sace kwanaki, shi ne na ce ko zaki bincika ko da ha'din bakin Bash ne? Saboda dama ya ce sai ya d'aukar masa mataki, and ranar da muka ga sanarwar b'atarsa na masa magana ko shi ne ya saceshi? Babu dai wata tsayayyar amsa, tun daga ranar na ke neman inda zan samu lambar wayarki, Allah ya sa na ganki a bakin shagon wannan matar, shi ne na ke ta bin kanta ta bani lambarki ta hana.." Yana gama fa'din haka kawai ya kashe wayar tare da mik'awa matar wayarta ya bar wurin.
     "Hello.." Ikram ta fad'a jin shiru. Tabbatarwar da ta yi cewa ya kashe ya sata janye wayar daga kunnenta cike da al'ajabi. "Bash Osca? Me yasa to? Me yaa Khalid ya masa da zaisa a saceshi?" Ta tambayi kanta. "Ya zama dole kuwa gareni na yi bincike don tabbatar da gaskiya, idan har hakan ta kasance dole zan d'aukar masa mataki." Ta ma kanta murmushi had'e da mik'ewa ta nufi down stairs.
     Momy ta tarar zaune suna fira da Naanah, zama ta yi itama d'in ta ce "Momy yaushe kuka fito? Ai na dawo na tarar bakya nan."
    "Ehh Ikram ina d'aki ne, ashe kin dawo ban sani ba." Momy ta fad'a.
    "Na dawo fa momy. Yaa Khalid baya nan ne?" Ta tambayi momy.
    "Khalid na d'akinshi baida lafiya sosai Ikram, ciwon kai ne ya ke damunsa har da zazza'bi ya ke sakar masa, ina jin dai tun inda aka buga masa bindigar nan ne sanda aka saceshi. Kuma gashi kullum sai ya je asibiti amma babu wani ci gaba."
      Saurin mik'ewa Ikram ta yi tana fad'in "Innaalillahi! Shi ne kuma bai fad'a min ba?"
     "Wallahi kuwa Ikram. Ki je ki dubashi yana d'akinshi." Momy ta fa'da cikin yanayin tausayi.
     Da sauri kuwa Ikram ta nufi d'akin Khalid har tana cin tuntub'e.  Ko sallama babu ta shige d'akin, ta sameshi ya yi kwanciyar ruf da ciki yana bacci. A hankali ta taka har bakin gadon nashi, zama ta yi kusa da inda ya ke kwance ta d'an tab'a jikinshi. "Ya Salaam!" Ta furta saboda yanda ta ji jikin nashi ya masa zafi rau.
    "Yanzu Yaa Khalid ashe baka da lafiya shi ne baka fad'a min ba?" Ta fad'a ita kad'ai.
     "Sannu, bara na nemo ruwan sanyi na d'an shafe maka jikinka da shi, zafin har ya yi yawa." Ta fad'a had'e da mi'kewa ta nufi water dispenser 'din da ke cikin d'akinshi.
    A cup ta tsiyayo ruwan ta duba cikin kayan wankinsa, wata riga cotton ta d'auko ta nufo wurinshi. Ringa yayyafa ruwa ta yi a rigar tana shasshafe masa jikinshi da shi, sai da ta shafe ko ina dan dama babu riga a jikinsa sannan ta ajiye ta tsura masa ido. Wani irin yanayi ta ke ji wanda ba zata tab'a iya misaltashi ba, har ga Alllah ta jima tana k'aunar Khalid, sai dai kuma ta kasa gasgatawa sai yanzu da lokaci ya 'kure mata, lokacin da har ya riga da ya tsayar da matar da zai aura. Wani irin zazzafan hawaye ta ji yana ambaliya a bisa kyakkyawar fuskarta wanda ta kasa controlling d'inshi.
     Khalid da tun d'azu idonshi biyu tun shigowarta yana jinta ya kasa ko da motsi, da zarar ya tuno da cewa fa ita ce yayanshi zai aura sai ya sake shiga wani yanayi.
     Hawayen Ikram ne suka ringa sauka a bisa bayan Khalid, da sauri ya motsa dan sam baya son Ikram tana kuka, bud'e idonshi ya yi ya tsura mata ido, itama tsura masa idon ta yi idonta ya yi jajur ta kasa fa'din komai.
    Murmushin k'arfin hali ya yi ya ce "Raguwar mace kawai, dan ina zazza'bi kawai shi ne kike kuka?"
      Cikin muryar kuka ta ce "Wannan zazzab'in naka ba kawai ba ne Yaa Khalid, ka ji kuwa yanda jikinka ya yi zafi rau?"
    K'ok'arin tashi zaune ya yi amma ya kasa, saboda jikin nasa ya masa tsami sosai. Da k'yar ya samu ya iya tashi ya ce "Ke wallahi babu komai na ji sau'ki ai, haka temperature d'in jikina ta ke dama, kin san blood 'o' negative jikin mutum yana yawan yin zafi." Ya k'arisa maganar da murmushi wanda iyakarsa bisa fuska kawai bai kai har zuci ba.
    Kai kawai ta gyad'a ba wai dan ta yarda ba, ta san yanda Yaa Khalid ya ke da k'arfin hali, da wuya a gane yana ciwo, wani lokacin sai idan ya warke sannan ya ke bada labari.
     "To yaa Khalid kana dai shan magani ko?" Ta tambayeshi.
     "Ehh na sha Ikram, please ki dama min kunu yanzu, na kasa cin komai tun jiya." Ya fad'a cikin k'arfin hali.
     Da sauri kuwa ta mi'ke had'e da fad'in "Yanzu kuwa Yayana." Ta masa murmushi cike da tausayinshi, ko da ace bata son Khalid to tabbas tana jinshi har cikin zuciyarta, shi ne mutum na farko wanda ya fara sakata dariya tun bayan sanda mahaifiyarta ta rasu, shi ne mutumi mafi muhimmanci wanda ya wayar da ita a lokacin da bata san miye wayewa ba. Ga uwa uba jininshi da ya ke cikin jininta, duk da dai ita kanta bata san da wannan ba, lokacin da ya bata jini bata a cikin hayyacinta.
      Cikin lokaci k'ank'ani Ikram ta dama masa kunun alkama, madara ta zuba da zuba sannan ta juye a falsk ta d'auki cup ta nufi d'akinshi, duk wannan hidimar da ta ke Haidar yana cikin 'dakinshi kuma yana kula da ita, sosai Ikram ke burgeshi saboda yanda ta ke kula da 'yan gidan baki d'aya.
    Ko da ta kawo ma Khalid kunun kad'an ya sha ya ajiye wai ya k'oshi. Cike da tausayi Ikram ta ce "Ka k'ara ko kad'an ne Yaa Khalid."
     Sake kurb'ar kad'an ya yi ya k'irk'iro murmushi ya ce "Na gode.."
    Itama murmushin ta k'irk'iro had'e da mik'ewa tsaye ta ce "Gashi nan na bar maka a flask, idan ka ji kana ra'ayin sha sai ka sha, na zuba komai a ciki." Ta fice tare da sakin wani zazzafan hawaye wanda ita kanta bata san sanda ya fito ba.

_Masu k'orafi duk sak'unanku sun iso gareni. Amma ina so ku sani, ko wane mutum da kuke gani yana da k'addararsa, sannan kuma ba kowane lokaci ne mutum ya ke samun abin da ya ke so ba. Kuma ma ai baku ga littafin ya k'are ba, har yanzu da sauranshi sosai. Ina mai tabbatar maku da cewa insha Allahu baki 'dayanku zaku ji dad'in k'arshen labarin, tun daga team Ikramhaidar har team Ikramkhalaid kowa sai ya ji dad'in k'arshen. To dan Allah ku yi hak'uri, ni mai burin farantawa kowa rai ne, fatana dai ku juri bibiyar wannan labarin, ina son isar da sa'kon da ke cikin labarin ne. Na gode kwarai masoyana, wanda suka bibiyeni ta private suna fad'in ra'ayinsu duk ina sane daku kuma na gode k'warai da kula dani da kuka yi, sannan kuma duk ban ga laifinku ba kan fad'ar ra'ayinku. Allah ya saka maku da alkhairi ya bar zaman tare._

*team Ikramhaidar*
*team Ikramkhalid*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now