69

948 57 3
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Wannan shafin naku ne baki ɗaya masoya Ikram da Haidar. Ku yi haƙuri bisa yanda labarin ya zo maku. Na san da dama ba zasu ji daɗi ba, amma ku sani, ba ko yaushe ne reader ya ke samun yanda ya ke so a littafi ba. THANKS._

69~  Da sauri Momy ta kamo ta daga duƙewar da ta yi tana faɗin "Daina kukan ya isa haka. Na matuƙar jin daɗi da ya kasance ba'a ɗaura wannan aure ba. Tun da dai haka komai ya kasance sai mu taru mo godewa Allah. Tare da fatan Allah yasa hakan shi ne mafi alkhairi a gare mu baki ɗaya."
    Salim ya ce "Amin ya Allah. Ina ji nan da la'asar jirgin su Khalid zai sauko. Insha Allahu da kaina zan je in ɗauko shi."
    "To Allah ya nuna mana, Allah kuma ya sauke su lafiya. Yanzu abin da ya kamata mu je asibitin da Miemie ta ke mu duka. Duk da na san Mamanta ta sanar mata, amma yana da kyau mu je har da kai ɗin." Ta nuna Haidar alamun shi ta ke nufi. "Da kuma ke Ikram. Ki roƙi yafiyarta a kan abin da ya faru. Sannan a tsara yanda komai zai kasance. Idan za'a jinkirta ko nan da sati ɗaya ko biyu kafin nan an gama gyara ɗayan gidan da ke kusa da wancan ɗin (Wanda aka ma Ikram jere.) Kafin nan ƙila suma sun shirya. Ke kuma ba za'a fasa kaiki wancan gidan da kayanki su ke yau ba. Insha Allahu kuma yau ɗin nan za'a kaiki babu fashi."
    "To shi ke nan Momy. Mu tafi ko?" Haidar ya faɗa.
    "To amma Momy ya zamu yi da mutane? Na san dole hankalin kowa zai dawo gare mu." Ikram ta faɗa bayan ta share hawayenta.
   Momy ta ce "Babu ruwanmu da kowa, tun da dai mai faruwa ta faru. Kowa ya san abin da ya faru."
   Fita suka yi tare suka isa waje, can nesa da gidan inda motar Marwan ta ke suka ƙarisa yana tsaye jikin motar yana waya da Khaleesat.
   Suna isa ya yi saurin tsinke wayar sannan buɗe masu motar da remote. Haidar ya zauna gaba, Ikram da Momy kuma baya.
   Sosai hankullan mutane suka dawo kansu, amma basu bi ta kan kowa ba kawai Marwan ya tada motar bayan Haidar ya faɗa masa inda zasu je.
   Momy ta ce "Oh! Marwan ashe abin da ya faru ke nan."
   Ɗan murmushi ya yi ya ce "Wallahi kuwa Momy. Dama wani baya auren matar wani, haka kuma wata bata aurar mijin wata. Allah ya riga ya tsara duk haka abubuwan zasu kasance. Sai gashi an gama events ɗin biki duk a matsayin Haidar ne ango. Lokaci gida kuma an samu sauyi. Allah Yasa hakan ne mafi alkhairi Ya kuma basu zaman  lafiya mai ɗorewa."
   "Ameen." Momy ta faɗa sanann cikin zaulaya Marwan ya ce "Ikram shi ke nan yanzu Haidar ya zama surukinki ko?" Ya yi dariya.
   Bata ce komai ba sai dai ta yi murmushi wanda har haƙoranta suka bayyana. Haidar kuwa dukan wasa ya kai masa ya ce "Kai dai wallahi baka jin magana. Wai ina ma sojojinka su ke ne?"
   "Oho masu. Ba tare da kai na ke ba ko yaushe? Suna gida mana. Ai ko sun ce zasu rakani sai in ce nima zan iya kare kaina." Suka tafa shi da Haidar suna dariya.

***
     Bayan sun isa asibitin suka sauka, Ikram ta ɗan yi gaba sai momy biye da ita. Daga bayansu suka ji an ce "Ikram!"
     A tare suka waiga, Mama suka gani fuskar nan tata a sake. "Masu hidimar biki ne suka baro bikin suka yo nan?" Ta faɗa bayan ta ƙariso tana murmushi.
    Cikin dattako momy ta ce "Wallahi ko, to ya muka iya? Ai ciwo ya kauda komai. Kuma shirmen da Ikram ta tafka dole ne ta zo ta ba Miemie haƙuri."
    "Haba Maman Ikram, dan Allah ki daina wannan maganar. Nima yanzu isowa ta ke nan na sauka daga napep na hange ku. Har an ɗaura auren ne?"
    Momy ta ce "An ɗaura kam. Sai ɗaurin aure ya canza akala."
    "Ke dai bari Hajia. Haka Allah Ya ke naShi lamarin ai. Idan ya tsara abu duk dabararka baka isa ka sauyashi ba. Wai ashe Miemie Haidar ta ke so duk zaman nan ban taɓa sani ba. Yayarta ce kawai ta sani kuma har ciwon nan da ta ke sun ɓoye min gaskiyar lamarin."
    "Mu ƙarisa ciki dai mu dubata da jikin." Momy ta faɗa.
    Haidar da Marwan ne suka iso suka gaishe da Mama cikin girmamawa. Tare suka ƙarisa cikin asibitin ta inda female ward ya ke.
    Ikram ce ta yi gaba da sauri ta shiga ɗakin. Miemie na zaune Kareema ta tasa mata abinci gaba ta tilasta mata sai ta ci. Dama kuma mai aikinta ce ta kawo masu abincin ta koma gida.
   Tana ganin Ikram ta kau da kanta gefe tare da zaro cokali daga bakinta tana neman ƙwarewa.
   "Sannu Miemie." Ikram ta faɗa a hankali haɗe da zuwa daga can bayan kujerar da Kareema ta ke.
    "Yauwa." Kawai ta faɗa a taƙaice.
    Sallamar momy da mama suka ji. Da sauri Kareema ta amsa sallamar tare da miƙewa daga kujerar ta basu wuri.
    Momy ta ce "A'a yi zamanki wallahi. Ga tabarma can zan zauna a kai."
   Kareema ta ce "A'a momy wallahi ki zauna. Mama sai ta zauna a bakin gadon."
    Zama kuwa momy ta yi sannan ta ce da Miemie "Aminatu sannu ko? Ya ƙarfin jikin?"
     "Jiki alhamdulillah!" Ta faɗa cikin dashasshiyar murya.
    Cike da tausayi mama ta kalli ƴarta ta ce "Ashe abin da ya faru ke nan kuka ɓoye min. Sai ga Haidar ɗin da kanshi ya zo ya labarta min komai. Baku kyauta ba ko kaɗan! Ai abokin kuka ba'a ɓoye masa mutuwa."
   Shiru suka yi su duka kamar wanda ruwa ya cisu. Can sai ga Haidar da Marwan sun iso suma.
   Sannu da jiki suka ma Miemie amma ta kasa amsawa, sai kallon Haidar ta ke cike da so da ƙauna tana ayyana abubuwa da dama game da shi. Sai dai kuma ta saka a ranta cewa ya zama dole ta fitar da ƙaunar da take masa ta ƙarfi da yaji ko bata so. Tun da dai yanzu ya zama mijin wata. Itama zata dage da addu'a har Allah ya kawo mata wanda zata so fiye da Haidar ɗin.
     "Miemie ga angonki nan fa yana miki ya jiki." Mama ta faɗa tana murmushi.
    'Angona?' Ta faɗa a zuciyarta.
   Kallon Haidar ta yi sannan ta kali Marwan. 'Wa su ke nufi?' Ta sake tambayar kanta.
    "Kina mamaki ko? Haidar na ke nufi. Gashi nan angonki ne." Mama ta sake faɗi bayan ta dafata.
    "Dan Allah Mama kar ki yi abin da ba shi ba ne kawai dan ki faranta min rai. Na sani Yaa Haidar ya riga da ya min nisa sai dai kallo kawai. Idan ma kun faɗi hakan ne dan ku faranta min rai to na gode." Ta kuma fasa kuka.
    "Me ya yi zafi haka Miemie? Duk abin da Mamanki ta faɗa miki gaskiya ne. Da shi aka ɗaura miki aure yanzu." Momy ta faɗa.
    Sosai ta ke mamakinsu. Yanzu kam ta yarda. 'To amma kuma su biyu ya aura ko me?'
    A ɓoye ta yi maganar amma bata san ta bayyana ba. Da murmushi Marwan ya ce "Ba ku biyu ya aura ba. Ke kaɗai muradinki ya aure ki. Da yake tun asali ita Ikram ɗin ba sonshi ta ke ba Momy ce kawai ta haɗasu. Ashe Khalid ta ke so shima kuma ita ya ke so amma babu wanda ya faɗawa ɗan uwanshi. Shi ne lokaci guda komai ya sauya, ita aka ɗaura mata aure da Khalid ke kuma da shi Haidar ɗin."
    Ido buɗe ta ke kallon Marwan tana jin maganar tashi kamar a mafarki. Sosai ta ke jin wani irin yanayi wanda ta kasa gasgata ita ce ko ba ita ba ce?
      "Yanzu haka ke matar Dr. Aliyu Haidar ce, one and only daga ke babu wata." Ya doki kafaɗar Haidar yana dariya, saboda in dai wurin zaulaya ce Marwan ba daga baya ba.
      Dariya suka ɗauka su duka ɗakin, banda Ikram da Miemie da suke ta satar kallon junansu.
     Da ƙyar jiki babu ƙwari Ikram ta iso gare ta tare da sunkuyawa ƙasa ta yi kneel down. Kama kunnuwanta ta yi duka biyun ta ce "Na sani ni mai laifi ce a gare ki Miemie. Amma har ga Allah ba da niyya na yi ba. Na rasa ta hanyar da zan fara faɗa miki ne. Dan Allah ki gafarce ni, and ki manta da komai, lets build a new life together (mu gina sabuwar rayuwa tare)." Ta riƙe tafukan hannayen Miemie bayan ta saki kunnuwan nata.
    Da sauri cikin kuka Miemie ta sauko daga bisa gadon ta kama Ikram ta tasar, bisa gadon ta zaunar da ita kusa da Mama sannan itama ta zauna.
    Runtse idonta ta yi ta ida matso ruwan hawayen da ke cikin idon ta ce "Wannan hawayen da ya fito na miki al-ƙawari shi ne na ƙarshen fitowa a kan wannan abin da ya faru. Ba wani abu kika min ba Ikram sai dai kawai na ji haushinki a kan ɓoye min abin da kika yi, bayan kuma ni na ɗauke ki da matsayi babba a zuciyata, wadda babu abin da na ke ji zan iya ɓoye miki da ya shafi rayuwata. Komai ya wuce har abada!" Ta sakar mata murmushi.
    Tafi aka ɗauka duka ɗakin har da Momy da Mama, da kuma Marwan da ke ta taɓo Haidar yana murmushi.
     "Na ji daɗi sosai amaryar Yayana. Allah ya baku zaman lafiya da zuri'a mai albarka." Ikram ta faɗa cikin zolaya tana dariya.
   Harararta Miemie ta yi ta ce "To amaryar ƙani..." Bata ƙarisa ba sanadin kallon momy da ta yi cike da kunya ta dafe bakinta tana dariya.
     Katse su momy ta yi da cewa "To yanzu Maman Miemie ya kike ganin za'a yi? Tun da dai baku shirya ba aka yi wannan lamari."
    Mama ta murmusa ta ce "Haidar na barin gidan na kira babansu na shaida masa da yake baya gari. Shi kanshi ya ji daɗin al'amarin musamman da ya ji ciwon ƴarshi. Ya ce insha Allahu gobe lahadi zai dawo. Ranar litinin sai mu tafi Kano da ita a yo duka bin da ya dace. Kin ga da yardar Allah zuwa ranar asabar sai ta tare."
    Rufe ido Miemie ta yi cike da kunya. Tana jin wani yanayi mai daɗin gaske yana shigarta. Baki ɗaya ciwon ma ji ta yi ta warke. Sai wasa ta ke da hannun Ikram da ta kasa saki tun ɗazu.
    Momy ta ce "To Allah ya kaimu lafiya. Kafin nan itama sai a yi ƴan gyare gyaren duk abubuwan da suka dace a gidan. Ikram kuma yau za'a kaita insha Allahu. Angon nata yana bisa hanyar dawowa."
   Tsikaro Ikram miemie ta yi tana mata dariya. Ita kuwa ta sadda kanta cike da kunya.
    Miƙewa Momy ta yi ta ce "Ni bari in tafi. Na baro gida cike da mutane."
     Mama ta ce "Nima ai ba zaki barni ba. Tare za'a yi yinin bikin da ni kamar yanda na tsara." Ta saki murmushi.
   Kareema dai in banda murmushi babu abin da ta ke yi. Sosai ta ke jin daɗin abin da ya faru.
    Basu kai ga fita ba Mata da mijin nan da suka kawo Ikram da Kareema asibiti suka iso.
    Hannun matar riƙe da babbar leda da fara'a ta gaishe da su Mama.
    Kujerar da momy ta tashi Kareema ta jawo mata ta ce ta zauna.
   Bayan ta zauna ta miƙawa Kareema ledar hannunta da ke ƙunshe da kayan marmari, ta tambaye su ya mai jiki? Sannan ta ma Miemie murmushi ta ce "Da alama patient ɗin ta warke. Na ga sai murmushi ta ke."
    Kareema ta ce "Ba dole ki ganta tana murmushi ba? Amarya ce fa."
   Ido buɗe matar ta ce "Amarya? Yaushe aka ɗaura auren?"
    Kareema ta ce "Yau ɗin nan. Kuma da wancan ɗin da ta baki labarin zai auri ƙawarta. Kin ga ƙawar tata nan." Ta gwada mata Ikram. "Sai aka fasa, ashe itama ba son angon ta ke ba ƙaninshi ta ke so. Shi ne aka ɗaura da Miemie, ita kuma aka ɗaura da wanda ta ke so ɗin."
   Da murmushi matar ta ce "Ahh lallai abu ya yi daɗi. Kin ga abin da na ke faɗa miki ke nan jiya da kina kuka a gidan yayarki har ciwo ya tasar miki. Allah ya bada zaman lafiya miemie."
     "Amin..." Mama da momy suka haɗa baki wurin faɗi.
      "Mun gode da taimakonta da kuka yi fa. Allah ya saka maku da alkhairi." Mama ta faɗa tana masu murmushi.
    Momy ta ce "To baki faɗa mana sunanki ba. Kareema ko ta faɗa miki? Sai ki faɗa mana"
     Da sauri Kareema ta ce "Ai momy jiya yanda muke a rikice bamu samu damar tambayar suna ba. Itama ji ta yi na ambaci sunan Miemie shiisa ta riƙe."
    Da fara'a ta ce "Sunana Rabiatu. Mijina kuma Ahmad. *Matar Ahmad* kamar yanda mutane ke kirana da shi."
     Cikin murna Ikram ta ce "Kar dai ke ce *Matar Ahmad* da na ke jin labarinta a bakin Amrah?"
     Murmushi Rabiatu ta yi ta ce "Ni ce fa da kaina. Ashe kin san Amrah."
     Ikram ta ce "Sosai ma kuwa. Mamarta ce ƙawar Momy. Yanzu haka tana gidanmu wurin yinin biki ita da ƴan *RAZ NOVELLA* baki ɗaya."
    Da murna Rabiatu ta kalli Ahmad ta ce "Aikuwa nima ba za'a barni a baya ba. Dole in je yinin bikin nan ko dan in haɗu da masoyana masu ƙaunar labarina."
    Murmushin soyayya Ahmad ya mata tare da jinjina mata hannu.
    Momy ta ce da Mama "Sai mu tafi ai ko?"
     Kareema ta miƙe ta ce "Nima ba zaku barni ba. Ko a hanya ne sai ku sauke ni in tafi gida in shirya zuwa yinin biki." Ta bi bayansu.
    Haidar da Marwan suka miƙawa Ahmad hannu suka gaisa sannan Marwan ya ce "To ku amare ya za'a yi? Ko zaku bi *Matar Ahmad* ne?"
    Da sauri Rabiatu ta ce "Ehh ku tafi kawai ma tafi tare. Ai an baki sallama ko Miemie?"
     "Ko basu bani ba tafiya zamu yi ko Ikram? Na tabbatar ƙawayenmu na can suna jiranmu." Ta kalli Ikram tana murmushi.
   Tafiya su Marwan suka yi. Suna tafiya Ikram da Miemie ma suka miƙe, tare da *matar Ahmad* suka tafi Miemie ɓoye da fuskarta dan bata so malaman asibitin su ganta su tsayar da ita. A haka har suka isa bakin motar Ahmad.

***
    Fira sosai su ke yi a cikin mota har suka isa gidan Momy da kwatancen da Ikram ke masu. A lokacin su momy sun riga da sun isa.
    Da farin ciki suka isa cikin gidan, mutane sai kallon su Ikram su ke, ana mamakin dama yanzu uwar amarya ta dawo. Ga kuma amarya ta dawo yanzu itama.
   A haka suka isa ɗaki. Ɗakin Khalid suka fara shiga, ƙawaye sai yi ma Miemie ya jiki su ke da fara'a ta ke amsawa. Sannan Ikram ta gwada masu Rabiatu ta ce "Ga *matar Ahmad* nan wadda ku ke jin labarinta. Ina jin Amrah ce kawai ta santa ko?"
    Da sauri Ashnur ta miƙe cike da murna ta rungume Rabiatu tana faɗin "Yau dai gani ga Rabiatu. Ni masoyiyarki ce ta haƙiƙa. Ina Ahmad ɗinki ya ke?"
     Ikram ta ce "Yanzu ya sauke mu ya tafi. Ai Rabiatu na nan har a kai amarya ko?" Ta kalli Rabiatu tana murmushi.
      Cike da wasa da dariya suka koma ɗayan ɗakin, dama tuni Miemie ta koma can har sun mata ya jiki.
     Nan ma dai Ikram ta yi introducing ɗin Rabiatu. Sun yi matuƙar farin ciki yayin da wasu suka tausayawa rayuwarta ta baya. Sannan suka jinjinawa haƙuri irin na Rabiatu, gashi lokaci guda ta ci ribar haƙurinta.
    Cikin kayan Ikram wanda Husnah ta zo mata da su ta ce Miemie ta zaɓi wanda ta ke so ta saka.
    Wani lace ne mai kalar hanta sai kwalliyar light blue. Gyalen kayan ta fiddo ta saka ras suka hau jikinta kamar dama nata ne.
   Bayan sallar la'asar masu kiɗan ƙwarya suka iso. Nan fa aka hau kiɗa babu kama hannun yaro. Ƙawayen amarya fitowa suka yi daga ɗaki suka dawo tsakar gida inda aka jera kujeru da manyan rumfuna.
     Nan fa aka hau cashewa sosai. Ikram dai aikinta kallo ne kawai tana dariya.

***
    Salim kuma ya tafi Airport tun ɗazu yana jiran saukowar jirgin su Khalid. Ƙarfe biyar daidai jirgin ya sauka a babban filin.



*Team Ikramkhalid*
*Team Haidarmiemie*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now