*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Wannan shafin naki ne kyauta my dear *Stylish bch* Allah ya bar so da k'auna ya bada zaman lafiya amaryar Haris. Ikram da Haidar na gaisheki kyauta._
40~ Washe gari da sassafe Ikram ta fara shirin makaranta, tsaf ta shirya cikin doguwar rigar atamfa purple and yellow, kasantuwar purple ya fi yawa a atamfar yasa ta yafa yellow d'in mayafi tare da jaka da takalma duka yellow. Make up ta yi sosai saboda malamar make up d'insu ta ce daga yanzu duk sanda zasu je makaranta su tabbatar da sun yi kwalliya, ta nan ne za'a tabbatar da cewa lallai su 'din d'aliban make up ne kuma suna gane darasin yanda ya kamata.
Sai da ta sha selfie sannan ta nufi down stairs cike da natsuwa.
Zaune su ke su duka uku, Haidar fuskarsa d'auke da fara'a yana ba Momy labari. "Theater'n jiya da na yi was successfully momy. Yanzu haka mutumin har ya farfad'o dana baroshi."
Murmushi momy ta masa ta ce "To madalla, lallai abu ya yi dad'i. Allah ya 'kara lafiya ya taimaka."
Fira dai su ke sosai wadda ita kanta momy rabon da ta yi irinta da Haidar an jima, cike su ke da walwala Khalid sai barkwancinshi ya ke d'an tab'awa.
Bayan ta sauko k'asa ta tsuguna ta gaishe da momy tana murmushi. "Lafiya lau autata, an tashi kafiya ko?" Ta dafa mata kai.
"Alhamdulillahi momy, na shirya zan wuce." Ta fad'a had'e da mik'ewa.
"Kamar ya zaki wuce? Ba fa ki karya ba Ikram." Momy ta fad'a.
D'an du'kar da kanta k'asa ta yi ta ce "Babu komai Momy, zan nema in ci idan mun yi break, na makara ne wallahi."
Cuision momy ta d'aga ta d'auko dubu biyu ta mik'awa Ikram ta ce "Ungo ki k'ara mai na dubu d'aya, sai ki yi break da dubu d'ayar."
Karb'a Ikram ta yi ta mata godiya sannan ta juya ga Khalid da tun d'azu ya k'ura mata ido yana kallo, tsabar kyau data masa yasa ya kasa furta komai sai kallo kawai.
"Kai kuma me ka taka da ba zaka min magana ba yau?" Ta fad'a ciie da tsiwa.
Juya mata ido ya yi had'e da maimaita abin da ta fad'a. Ya k'ara da "Ina kallon kwalliyar aljannu ne."
Cikin k'uluwa ta ce "Ka fa san babu abin da na fi tsana sama da wannan kwaikwayon maganar naka. Yaro ka kiyayi make up artist dan na kusa zama young millonaire." Ta yi guntun murmushi.
Dariya Khalid ya yi sosai had'e da fad'in "Ahh lallai young millonaire, da dai young billonaire kika ce da abin ya fi armashi." Ya sake kecewa da wata dariyar.
"Whatever, ni dai na fad'a maka ka bi a hankali dan Ikram ta kusa zama babbar mai kud'i kuma celebrity." Ta masa gatsine.
"To Allah dai ya taimaka. Wai wacce ke son zama likita ce ke maganar zama a big make up artist. Zamu ga yanda wannan had'in doya da manjan zai kasance."
Tab'e baki ta yi ta ce "Komai na duniya ai sai idan mutum bai sa kansa ba, kuma ka rubuta ka ajiye, insha Allahu sai na zama likita, sannan kuma sananniyar make up artist, dan nan gaba k'ara wani karatun ma zan yi a kan make up, insha Allahu har school sai na bud'e nima ina koyawa wasu."
"Yauwa ke dama ina son fa'da miki, jiya da dare abokin nan nawa da ke da cafe ya kirani, wai an fara siyar da form d'in jamb, to ni sai na ga kaman ki yi matric zai fi sau'kin samun admission d'in medicine fiye da through jamb d'in nan, tun da yanzu jamb d'in ma kanta ba tabbas gareta ba."
"To duk yanda ka ce yaya, ni ka san ba wani sanin kan wannan abubuwan na yi ba. Bara na tafi kar na makara." Ta fad'a had'e da kama hanyar barin parlor.
Kamar daga sama ta ji ya ce "Ikram ba magana?"
Jin muryarsa ya sa ta k'i waigowa cike da mamaki ta ce "Ina kwana?" Kawai ta ficewarta.
Bai ji haushinta ba ko kad'an, saboda abubuwan da ya ringa mata a baya shi kanshi ya san zai yi waha ta mantasu, haka kuma idan har zata ringa tunasu to tabbas ba zata tab'a ganinshi da mutunci ba.
Mik'ewar ya yi shima ya ce "Momy bara na yi wanka, sai k'yamar jikina na ke." Ya yi murmushi.
"To ka hanzarta sai ka dawo ka karya." Momy ta fad'a tare da miyar masa da murmushin.
D'akinshi ya nufa ya rage d'aga ita sai Khalid, hakan ya sa Momy fad'in "Ya kamata ka shaidawa yarinyar da kake nema ta fad'i gidansu cewa za'a turo nan da sati biyu insha Allahu. Na yi magana da Alhaji Kallah na masa bayani cewa ka fitar da mata turawa kawai ta rage, ya ce min babu damuwa zai zo gidan gobe, sai mu yi maganar baki da baki. Yayanka ma na yanke shawarar wadda zan had'ashi da ita, na tabbatar yarinyar ba zata k'i zab'ina ba sai dai ko daga shi, idan daga shi d'in ne kuwa ko ya ki ko ya so sai ya aureta, dan ba zan zirasa masa ido ina ji ina gani ya tsofe min a gida babu iyali ba."
Guntun murmushi Khalid ya yi ya ce "Kin zab'a masa mata momy? To idan fa baya sonta?"
"Sai ya koya sonta d'in. Hukunci dai na yanke kuma ya yanku. Na had'ashi aure da Ikram!" Ta fad'a a daidai shigowar Haidar cikin d'akin.
Da k'arfi Khalid ya mik'e tsaye, ido bud'e bakinshi sai rawa ya ke ya kasa furta komai, kallo kawai ya ke bin momy da shi, sam ya kasa saita kanshi, wani irin yanayi ya ji wanda bai tab'a jin irinsa ba, k'afafun nashi sun ma kasa d'aukar gangar jikinshi, da k'arfi ya fa'da bisa kujera gabanshi sai tsananta bugawa ya ke.
Kallon mamaki momy ta bi Khalid da shi. "Kai! Lafiyanka? Ko akwai damuwa ne?"
Cikin inda inda Khalid ya ce "Babu..." had'e da dafe kanshi da ke barazanar fashewa.
"Kar ka min k'arya Saifullahi, tabbas akwai damuwa idan da wani abu dan Allah kar ka b'oye min..." momy ta fad'a.
K'ir'kiro murmushi ya yi wanda iyakarshi a baki ya ce "Kawai dai ina tunanin maganar da kika fad'a ne, ganin yanda Yaya Haidar da Ikram basa jituwa, ta ya zasu yi rayuwar aure cikin soyayya? Abu da kamar wuya." Ya goge zufar da ke keto masa duk da rab'ar air conditioner'n da ke d'akin.
Jin abin da ke faruwa ya sa Haidar ya yi saurin juyawa ya koma d'akinshi, dan dama bai d'aga labule ba hakan yasa basu san da wanzuwarshi ba. Ya ma rasa halin da ya ke ciki, bak'in ciki ne ko farin ciki? A zahirin gaskiya baya son Ikram, sai dai kuma halaccin data masa ya sa ya ke burin kyautata mata, ya ke jin tana burgeshi a halin yanzu. Kanshi ya dafe yana tunani 'Menene mafita? Mesa momy zata min haka? Mesa ta ke son dole sai ta min aure kamar wani k'aramin yaro?' Ya kama murzar sumarshi da duka 'yan yatsunshi.
A parlor kuwa baki d'aya wuta ta d'aukewa Khalid, jikinshi sai rawa ya ke kamar wani mai zazzab'i, jikinshi kuwa ya yi zafi rau, idonshi ya yi jajur kamar jan gauta.
Naanah ce ta zo ta ce "Khalid ga doyar na gama soya maka, a kawo nan ko dinning d'in zaka je ka ci?"
Cikin wata irin murya k'asa k'asa ya ce "Barshi kawai na gode."
Da mamaki ta ce "Kamar ya a barshi? Kai fa ka ce na soya maka doya da k'wai kuma na san kana sonta sosai. Me ya faru ne?"
"Kaina ya ke min ciwo sosai kuma da alama ya sakar min zazzab'i." Ya fad'a muryarshi na rawa kamar mai son yin kuka.
Cikin tashin hankali momy ta ce "Ba dai inda suka buga maka bindigar ba ne ko?"
Murmushin k'arfin hali ya yi ya ce "Da alama dai shi ne, bara na koma asibiti dama yau suka ce na je." Ya mik'e a hankali.
Da k'yar ya iya yin tsayuwar dan komai na shi ji ya ke ya tsaya cak da aiki. Cikin tausayi momy ta ce "Subhanallahi! Gaskiya kam ya kamata ka koma, kar ka manta to ka tafi da motar yayanku mai tint."
"To momy." Ya fad'a ha'de da ficewa, ba wai kanshi d'in ke ciwo ba, tsabar rikicewa da hukuncin da momy ta yanke ne.
Makullin motar ya d'auka ya nufi parking space, da k'yar ya ke tuki'n wanda bai san inda zai je ba, kawai dai abin da ya sani shi ne yana son ya keb'e inda babu kowa, wata k'ila zai samu ya fitar da hawayen da tun bayanin momy ya ke k'ok'arin fito masa amma ya kasa.
Ya yi tafiya mai nisa a cikin garin Sokoto, a junction d'in garin Illaila ya tsaya ganin duk mutanen da ke wurin hankalinsu bama kanshi ya ke ba, kiran fasinjoji kawai su ke. D'an matsawa ya yi inda babu mutane ya kashe motar. Hannunshi ya d'ora a kai tare da kad'a kanshi "Me yake faruwa da ni? Me momy ta fad'a ne? Ya Allah kasa mafarki na ke ba gaske ba ne. Allah ka tasheni daga wannan mummunan bacci mai k'unshe da mummunan mafarki." Sai a lokacin wani irin hawaye mai gumi ke fito masa, kasa controlling hawayen ya yi sai 'kara tuno shak'uwarshi da Ikram ta kusan shekaru uku ya ke, wai kuma yayanshi guda d'aya tal wanda ya fi 'kauna a duniya shi za'a aurawa Ikram.
Sosai ya ke kuka yana neman sassauci daga Allah. "Innaalillahi wa innaa ilaihi raji'un!" Ita ce kalmar da Khalid ke ta furtawa a hankali, kamar yanda addinimu ya koyar damu cewa a duk sanda kake cikin damuwa ko wata musiba ta sameka to ka furta wannan kalmar, Allah zai kawo maka d'auki, zai kuma sassauta maka damuwarka.
A hankali ya fara jin sau'ki a cikin zuciyarsa, wanda hakan ya bashi damar tayar da motarshi ya koma cikin mutane, ruwa ya ro'ka aka bashi dan bai fito da ko sisi ba, ya wanke fuskarsa sannan ya kama hanyar komawa gida.***
Da k'yar Haidar ya iya fitowa ya karya, shima d'in sai da Momy ta kirashi a waya sannan ya fito, ta k'udira a ranta cewa ba zata fad'a masa wacce ta had'ashi da ita ba dan kar ma ya yi rejecting, sai biki ya rage sati 'daya sannan ya san ko wacece.
***
Ikram kuwa daga makaranta wurin Barr. Kareema ta wuce, bata sameta ba hakan yasa ta kirata a waya don jin inda ta ke, tana gida ta shaida mata yau bata fita aiki ba. Kama hanyar gidan Kareema ta yi zuciyarta fal da farin cikin da ita kanta ta rasa ko na menene.
Kai tsaye gidan Kareema ta nufa, bayan ta yi parking ta k'arisa cikin gidan tare da d'aukar wayarta da ke ringing, bayan sun gaisa da mai kirantan ta ce "Ban gane wacece ba."
A 'daya b'angaren mai kiran tata ta ce "Na san ba zaki gane ba dama. Nice wadda kika ta'ba zuwa shagon d'inkina har kika yi mantuwa na kiraki."
"Oh! Na gane. Ya kike ya aiki?" Ikram ta fad'a dan sai yanzu ta gane ko wacece.
"Lafiya 'kalau, a ranar da kika zo bayan kin tafi wani mutumi ya shigo cikin shagona, ya nemi na bashi phone number naki amma na k'i na ce sai idan na tambayeki kin bada izini sannan, na manta ban tambayekin ba shi ne 'dazu ya zo wai ya muka yi da ke? I don't know what to tell him."
"Don't give him my number." Kawai Ikram ta fad'a had'e da tsinke kiran a daidai shigarta parlor'n Kareema. Kamar wancan zuwan da ta yi, yau ma Kareema bata d'akin sai mijinta zaune yana kallon mbc bollywood. Da sallama ta shiga hakan ya dawo da hankalin M. Lawal gareta. Kallo d'aya ya mata ya ganeta, da murmushi ya amsa sallamar ya ce "Yan mata kwana da yawa, yaushe rabon da in ganki?"
Fuskarta ta k'ara tsukewa ta ce "Wurin Yaa Kareema na zo, tana ciki?"
Da murmushi irin na 'yan duniya d'in nan ya ce "Ehh tana ciki 'yan mata."
Bata sake waiwayarshi ba kawai ta shigewarta d'akin Kareemah cike da takaicin hali irin na M. Lawal._A yi ha'kuri da wannan bamu da wuta ne. Na gode masu bibiyar wannan labarin._
*team Ikramhaidar*
*team Ikramkhalid*
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.