31

1K 66 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Na sadaukar da wannan shafin ga Aryeesher muhd, Safura Garba da baki d'aya 'yan *mu sha karatu..na RAZ.* Na gaisheku sosai da sosai, kamar ma kun fi kowa son *SHI NE SILA.* Na gode k'warai da gaske, Allah ya bar k'auna. Ku saka a ranku cewa #anatare._

31~  Ikram bata daina kallonshi ba har sai da ta ji ya ce "Ikram yaushe kika zama haka? Yaushe kika fara tara lambar wayar maza a wayarki?"
    Kasa furta komai ta yi, saboda yanayin da ya ke ciki bata tab'a ganinshi haka ba.
    "Bash Osca?" Ya fad'a bayan ya sake duba sunan da ta yi saving a wayar.
    "Ikram ba dai Bash Osca mayaudari wanda na sani ba. Kin kuwa san ko waye shi d'in? Kin san adadin matan da ya yaudara ya ma ciki? Da alama dai baki sani ba tun da har kika iya d'aukar kiranshi a wayarki. Idan ma baki sani ba yau ki sani, Bash Osca mayaudari ne na k'arshe, kuma komai salihancin yarinya sai dai idan bata fara soyayya da shi ba, sai ya karkatar da ita da munanan halayensa. Dan haka bari ma ki gani." Ya bud'e bayan wayar. Batirin ya zaro sannan ya ciro layin ya kakkaryashi ya ce "Zan siya miki new sim, babu ke babu Osca in dai har na isa da ke Ikram." Ya tada motar suka ci gaba da tafiya.

****
    Bash Osca kuwa sosai ya ke mamakin wannan al'amarin, tabbas ya yarda da maganar Ikram na cewa bata da saurayi, amma kuma me? Ga wani nan yana ikirarin shi zai aureta, to me ke faruwa? Ya d'aukarwa kansa alwashin ba zai tab'a barin rayuwar Ikram ba, zai ci gaba da bibiyarta har sai lokacin da ya tabbatar da cewa da gaske tana da wanda zata aura d'in sannan zai k'yaleta, idan kuwa ya gane babu wani wanda zai aureta to shi zai aureta ko ta halin k'ak'a. (Ni kuwa Amrah na ce lallai Osca akwaika da k'arfin hali.)
    Jibo bayan Bash ya bashi labarin abin da ya faru ya ce "Dan Allah Bash to ka fita harkar yarinyar, da alama k'arya ta maka dama, shine sai asirinta ya tonu."
    "Jibo ke nan, kai kamar baka san ko wanene Bash Osca ba? Ba zan tab'a rabuwa da Ikram ba ya kamata ka san da haka. Nine mijin Ikram kuma dole sai ta aureni." Ya sake latsa kiran Ikram amma sai ya jita a kashe.
    "Da alama tilastata ya yi koma waye. I've trust Ikram, na san ba zata tab'a fa'da min k'arya ba. Na yarda cewa bata da saurayi kuma bata ta'ba yin soyayya ba."
   Dafa kafad'arshi Jibo ya yi ya ce "Ta ya zaka iya gane haka? Ka fi kowa sanin halin 'yan matan yanzu. Barin Ikram kyakkyawa ajin 'karshe, kai baka ga yarinyar zubin Indiyawa da larabawa gareta ba? Ka kuwa san dole ta yi samari ba ma saurayi d'aya ba. Ka yi kuskure tun da har ka yarda cewa bata da saurayin."
    Murmushin takaici Bash ya yi ya ce "Na fi kowa sanin halin matan yanzu kam. Amma Ikram ta banbanta. Kai Jibo! Wallahi sai na auri Ikram, ka ji na rantse, kuma sai na yi bincike a kan ko waye ya karb'i wayar, idan har na ganoshi sai ya san cewa ni ya ma wulak'anci, har ya ke tutiyar in har ban rabu da matarshi ba sai ya wula'kantani, to kafin shi ya wula'kantani ni zan wula'kantashi." (Tir k'ashi! Na fada a raina.)

****
      Komawar su Ikram gida momy na zaune ta rafka uban tagumi ruwan hawaye na tsiyaya daga idanuwanta. A rikice Ikram ta isa inda ta ke, hawayen ta fara share mata da gyalenta tana fad'in "Momy me ya faru? Na shiga uku! Kuka momy, me aka miki? Ko Hajiyar ce?"
    Kasa magana momy ta yi sai wani hawayen da ke zarya a kumcinta.
    Da gudu Ikram ta nufi b'angaren su Khalid, baya d'akin sai dai ta ji alamar motsin mutum a toilet, hakan ya bata damar zarcewa d'akin Haidar, zaune ya ke shi kuma da laptop a hannunsa yana latsa. Jin ta shigo d'akin a rikice ya sa ya ajiye laptop d'in cikin maganarshi mai natsuwa da izza ya ce "Ke lafiya kika shigo min d'aki? Ko kin yi d'imuwa ne? Ga d'akin abokin naki can ai."
    Mamakin Haidar ta ke, magana dalla dalla kamar baya son yi, yanzu ma ai da sau'ki tun da har ya iya jera mata guda uku a had'e, wanda ko momy'nsu da wuya ya ma haka, baya ma zama yin fira da ita sai idan ta kama dole.
    "Tun da baki tashi magana ba sai kita tsayuwa ai." Ya yi tsaki had'e da ci gaba da latsar laptop d'insa.
     "Yaya.." ta yi shiru tana sauk'e ajiyar zuciya.
    Banza yayi da ita ko kallonta bai sake yi ba.
    A 'kufule ta juya zata bar d'akin sai kuma ta tuna a halin da ta iske momy. Daurewa ta yi ta juyo kanta k'asa ta ce "Ga momy can tana kuka, na rasa abin da ya ke damunta, kuma na tambayeta amma ta k'i fad'a min.." tun bata rufe baki ba ya yi saurin mik'ewa tsaye yana salati. "Momy'n? Me ya faru da ita? Ya salaam!" Yama rigata fita daga d'akin ita da ke bakin 'kofa.
    A rikice ya isa 'dakin tun daga nesa ya fara fad'in "momy me ya faru da ke?" Har ya iso daidai kujerar da ta ke ya yi turus a k'asa ganin yanda idanunta suka canja launi zuwa jaa.
    Hannunta ya ri'ke yana fad'in "Momy dan Allah ki fad'a min me aka miki?" Idanuwanshi shima sun yi jajur kamar wanda ya sha kukan.
    Daidai shigowar Ikram 'dakin itama ta zauna kusa da Haidar.
    Sun fi minti goma suna mata magiya a kan ta fad'a masu abin da ya ke damunta amma ko magana ta kasa. "Me ke faruwa ne?" Khalid ya fad'a tun daga nesa a daidai shigowarsa d'akin.
    "Yaa Khalid a haka muka samu momy, kuma mun yi mun yi ta fa'da mana abin da ya ke damunta amma ta k'i magana." Ikram ta fa'da cikin kuka.
    Shima zaman ya yi a kusa da su. Sai a lokacin momy ta d'ago rinannun idanuwanta ta ce "Yanzu Sameera ta bar gidan nan..." sai kuma ta yi shiru.
    Jin haka yasa Khalid fa'din "Me ta zo yi momy?"
    "Wulak'anci ta min sosai Khalid, wai Goggoji ta fad'a mata ina ri'kon Ikram, in har ta wuce kwana biyu bata bar gidan nan ba sai ta lalata rayuwarta. Bana son a lalatawa Ikram rayuwa, kuma bana son Ikram ta bar gidan nan dan ban san halin da zata fa'da ba. Na d'auki Ikram tamkar 'yar da na haifa da cikina. Ban san mesa ba mutanen nan su ke takurawa rayuwata, tun ina amarya babu wani farin ciki da na samu sai ko wurin mijina, yanzu ma da babushi sun hanani na sake. Ya zan yi ne Khalid?"
    A zuciye Khalid ya ce "Wai su mutanen nan ba zasu k'yalemu mu sake ba? Sun takura a kan sai an basu gadon Hajia wanda kud'in ma basu fito ba, a cikin dukiyarki kika sa na cire na kai masu na kuma kafa hujjoji. To miye nasu ya rage a rayuwarmu? Ko sun manta cewa mu muka gaaji wannan gidan ba Hajia ba? Saboda haka muna da damar aje duk wanda muka ga dama a ciki."
    "Haka ne Khalid, amma ni na yanke shawarar Ikram zata koma gidan k'awata Hajia Balare, komawar na wani lokaci ne ba wai zama zatai ta yi ba, Allabishi daga baya idan komai ya nitsa sai ta dawo. Bana son komai ya samu rayuwarta.."
    Tun bata rufe baki ba Haidar ya mik'e tsaye, guntun tsaki ya yi kafin ya ce "Wannan abin ai momy ke kika miyar dashi babban abu har kike b'arnar ruwan hawayenki. Wallahi babu inda Ikram zata je, tana nan gidan zama daram. Kuma maganar sawa a lalata mata rayuwa mu zuba mu gani! Shege ka fasa." Ya fice daga d'akin.
     Kallon mamaki Ikram ta masa, ashe dai shima d'in yana da kirki? Kai! Ba dai kirki ba, an dai ci sa'arsa ne kawai saboda abin ya shafi momy'nsa.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now