shi ne silah page 7

1.1K 83 1
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

     Na Princess Amrah
              (NWA)
               2018

7~ "Tun ina yarinya 'yar shekara biyar Goggo Indo ta ke d'ora min talla. Duk da ya ke ina yin tallar ne ba wai dan nasan kanta ba, a lokacin bana fahimtar komai sai dai kawai na gane sai Mallam ya yi tafiya ta ke d'ora min tallar. Babban abin da ya ke tayar min da hankali shi ne yanda ko b'atar k'wandala d'aya na yi sai ta kama ni tayi min dukan tsiya, wani lokacin ma har da abinci ta ke hanani. Haka rayuwata ta ci gaba da tafiya har shekaruna suka fara yawaita. Duk lokacin da Mallam ya ke nan kuwa babu wani d'an so sama da ni, ta nunar da kula sosai a gareni.
    Wasa wasa har ya zamanto yanayin cinikin da na yo wa Goggo tou yawan abincin da zata bani ke nan.
    Samari kuwa duk wani na kirki da zai zo wurina sai Goggo ta koreshi, ta ce wai ba sa sakin kud'i ita ta fi son wanda zai bama 'yarta ku'di har ita ma ta samu. Sam wannan halin nata baya min dadi.
   Babban abin mamaki shi ne yanda Goggo ta ke nuna min hanyar da zan lalace k'arara amma ina kauce mata, ita kuwa hakan baya mata dadi. Ina ji ina gani ta hanani karatu duk da yanda na ke tsananin son yin karatu. Hatta da islamiya sai idan Mallam yana nan ta ke barina na je. Kullum sai talla, da safe ina wurinta cikin gida inda ta ke siyar da shinkafa da wake. Da rana kuwa zata d'ora min tallar aya da gyada, da yamma kuma idan na dawo kunun zaki ne zata dora min sai dare na ke dawowa.
    Haka rayuwata ta ke tafiya kullum cikin talla ko sassauci babu, idan har kuka ga ban je talla ba to rashin lafiya ne mai tsanani ya hanani zuwa, ko kuma mallam yana nan kamar yanda na fada maku.
    Tun samarin kirki suna zuwa wurina har ta kai ga sun daina zuwa sai dai na banza. Hakan ba karamin d'aga min hankali ya ke ba.
      Wata rana Mallam ya tafi Kano inda ya ke siyar da shayinshi, Goggo ta dora min tallar kunun zaki kamar kullum, na tafi kuwa gidan kallo inda na saba kaiwa duk dare saboda na fi samun ciniki in dawo da wuri gida yanda na ke so.
     Ina zaune inda jerin masu talla su ke ajewa wani saurayi mai suna Halle ya zo. Daidai inda na ke ya duk'o ya d'auki ledar kunun zaki d'aya yana min wani shu'umin murmushi ya tafi daga baki d'aya harabar gidan kallon.
     "Halle" na kira sunanshi da karfi amma ko waiwayena bai yi ba. Sanin halin Goggo in har na koma gida na mata b'ata sai mun sab'a da ita ya sa na damk'a amanar bokitin kunun ga k'awar kasuwancina na bi bayan Halle ina k'wala masa kira.
     Sai ya juyo ya kalleni sannan yayi murmushi ya k'ara sauri, ni kuwa k'ara binshi kawai na ke.
    Sai da ya yi nisa sosai sannan na juya na fita batunshi. Sai da na sayar da kunun duka sannan na kama hanyar gida, amma fa hankalina a tashe ya ke saboda zulumin abin da zan tayar a gida.
    A kofar gida na yi tsaye ina tunanin ina ma Mallam ya dawo a cikin daren nan, sai dai kuma ba mai yiwuwa ba ne saboda yau yau d'in nan ya tafi.
    K'in shiga na yi har sai da dare ya nitsa sosai na ji Goggo na kokarin fitowa hannunta rike da fitila, hakan ya sa na kara labewa jikin dakalin kofar gidan. Ina jinta tana kwala min kira amma na yi shiru ban ko tanka mata ba sai rawar jiki da na ke.
      Ta gaban dakalin ta zo wucewa aikuwa ta takeni da karfi na saki ihu tare da dafe wurin da ta takeni.
    Salati ta dauka tare da dafe bakinta tana fadin "Umma boyon me kike a nan? Tabbas baki da gaskiya tun da har kike boye boye, na sanki tun kina yarinya da zarar na ga kina irin haka tou babu gaskiya. Fada min b'ata kika min ko?"
     Cikin in ina na ce "ehh...a..a'a"
    A fad'ace ta ce "ki fada min gaskiya ko kuma na b'ab'ballaki."
    Baki daya jikina rawa ya ke na ce "Halle ne ya dauka na yi na yi da shi ya bani kudin ya hanani, har binshi na yi a baya amma bai bani ba. Na bari sai gobe tun da na ga gidanshi sai na je na karb'o..."
     Bata ko jira na gama maganar ba ta wanka min kyakkyawan marin da sai da ya gigitani. A fusace ta ce "kudin nawa ne kika baro a wurin Halle? Wallahi ba zan dauki asara ba, wuce mu tafi gidan nashi idan ma da gangar jikinki zai fansar min kudina na yarda." Tun daga lokacin da Goggo ta yi wannan maganar na ke kokontonta akan cewa mahaifiyata ce, saboda babu uwar da zata zabi haka akan mutuncin 'yarta sai dai dama idan ba uwar ba ce.
    Kuka sosai na ke ina fadin "wallahi Goggo Halle dan iska ne, shi ya lalata kawata Huzaimah, da zarar mace ta yarda ta bishi gudanshi komai zai iya yi mata, saisa ma da na bishi naga gida yake da shirin shiga kawai na juya na hakura da kudin, dan Allah ki yi hakuri idan Mallam ya dawo zan rokeshi ya bani naira biyar dinki na baki."
     Babu annuri a fuskarta ta ce "ki tona min asiri ke nan? Aikuwa da na raunataki. Zaki wuce mu tafi ki karbo min kudina ko sai na ji miki ciwo a wurin nan?"
    Jiki na rawa na ce "zan wuce mu tafi Goggo." Ta ja hannuna da tsiya muka nufi gidan Halle da ya gada wurin iyayenshi wanda banda iskanci babu abin da ya ke yi a cikin gidan, kuma ya gagari kowa da ke garin saboda yana da abin hannunshi, kafin babanshi ya rasu mai rufin asiri ne.
     Tafiya muka yi mai dan nisa kafin muka isa kofar gidan, na ja na yi tsaye sosai jikina ke rawa saboda tsoro, har ga Allah ina tsoron maza amma na fahimci sam Goggo bata guduna da su. Ita kam abin duniya kawai, in dai kan abin duniya ne koma me zai sameni ba zata taba damuwa ba.
    "Kika ja kika yi tsaye, ba zaki wuce mu shiga ba?" Ta fada.
     Shiga na yi jikina babu kwari, ita kuwa ta bini a baya har muka shige cikin gidan.
     Bayan na yi sallama ne muka sameshi zaune hannunshi rike da sigari yana zuka. Ganina da yayi yasashi sakin murmushi tare da mikewa tsaye yana fadin "kin biyoni ki karbi kudinki ke nan, kar ki damu har da k'ari ma zan miki akan wanda kika biyoni, ehh ka'ri da yawa ma kuwa."
     "Allah ya kyauta min, ni kudina na sani ka bani na tafi, tare na ke da Goggona."
     Murmushinshi ya miyar ga Goggo da ta saki baki tana dariya jin ya ambaci kudi. Gaisheta ya yi ta amsa kuwa sannan ta ce "ai ni ban san kai ne ta bama kununa bashi ba, inda na sani ai da ban taso k'eyarta ta karb'ar min ba, ko dan soyayyar da ka ke mata ai zan iya bar maka kyauta."
     Dama Halle ya san halin Goggo da son kudi, saboda yana zuwa siyan shinkafa da wake wurinta tun a lokacin ya nunar mata da yana sona ya mata kyautar kud'i amma ni na k'ishi.
     "Ahh to barin tafi, idan kun gama magana ta sameni a gida." Goggo ta fada tana kokarin fita.
    Kamo hannunta na yi a tsorace na ce "dan Allah Goggo kar ki tafi ki barni, wallahi Halle mugu ne, kar ki min haka dan Allah, ke fa uwata ce, ta yaya uwa zata so a lalata rayuwar 'yarta?" Da k'arfi ta janye min hannu tare da fadin "ka yi kokari ta dawo da wuri Halle, sannan kuma hannuna da girmanshi a bude ya ke kai kawai ya ke jira." Ta saki murmushi tare da barin gidan.
     Da karfi ya jawoni yana fadin "ina da kudi Umma, dama da gangan na d'aukar miki kunu dan nasan sai hakan ta faru, na dade ina sha'awarki amma tsabar taurin kai irin naki kin ki ki bani dama in dama, to yanzu gashi Goggonki da kanta ta bani dama zan kuma dama, ehhh zan dama kuwa." Ya jani da tsiya ya shigar da ni cikin d'akinshi.
       Wannan daren ne ya zame min bak'in dare, mummunan dare wanda har na kwanta damata ba zan tab'a mantawa da shi ba. Daren da na rabu da budurcina ba ta hanyar aure ba, budurci abin da ko wace mace ta ke alfahari da shi, ko wace mace ta ke burin ta kaiwa mijinta, ni kuwa sai sab'anin  haka. Babu ko imani barin tausayi Halle ya lalata min rayuwa. Nasha kuka da magiya amma bai k'yaleni ba har sai da ya biya buk'atarsa sannan ya miyar min da kayana shima ya miyar da nashi kayan.
     "Tashi ki tafi gida dare ya yi." Ya fada, ni kuwa tsabar takaici ko kallonshi ban yi ba banda kuka babu abin da na ke yi.
     Ciccib'ata ya yi da kanshi ya kaini gida, a bud'e gidan ya ke Goggo bata rufe ba tana zaman jiranmu. Ko da muka isa kuwa d'akina ta gwada masa ya shiga da ni ya kwantar bisa katifa, ina jinsu ya bata kudi amma ban san ko nawa ba ne, sai godiya kawai na ji ta masa cike da jin dadi.
    Tun daga wannan lokacin na ke tir had'e da Allawadai da uwa irin Goggo, uwar da ta zab'i abin duniya fiye da martabar 'yar da ta haifa...
@wattpad: PrincessAmrah

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now