*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
(NWA)
201812~ Suna fita suka ci karo da wata aminiyar Umma mai suna Talatu, ganinsu rik'e da kaya nik'i nik'i yasa ta fad'in "me zan gani haka Rumana? Ina zuwa da kaya har a ka?"
Har Umma ta bud'e baki zata mata bayani Ikram ta ce "tsayawa yin bayani zai iya sakasu janyo ra'ayinmu daga tafiya." Hakan ya sa Umma yin shiru tare da ci gaba da tafiya. Saurin jawo Ikram Talatu ta yi, "Ikram me kike fad'i haka? Ina kuke k'ok'arin zuwa ne ma wai?"
"Dan Allah Mama Talatu ki yi hak'uri ki k'yalemu." Ta fad'a.
"Ba zan k'yaleku ba Ikram, ku fad'a min inda zaku tafi saboda hak'k'in zaman tare ne, ko ba komai yanda na ke da Rumana ai ya ci a ce idan ma tafiya zata yi ta sanar dani, ba wai kwatsam in ga ta tafi ba, kenan ma idan da Allah bai kawoni ba yanzu sai dai kawai na ji labari ko?"
Tsayawa cak Umma ta yi, ba tare da ta waiwayo ba ta ce "zamu bar garin nan ne, zamu koma inda babu dangin iya bare na baba, inda zamu iya zama ba tare da an gorantawa 'yata ko an tsangwameta ba, inda idanma tsanar ce za'a tsanemu da hujja, ko ba komai basu sanmu ba, ba wai nan da sun sanmu amma suke wulak'antamu ba." Ta kammala maganar da rawar murya tana k'ok'arin yin kuka.
Da hanzari Talatu ta iso inda Umma ta ke, rungumarta ta yi ta ce "waye ya fad'a miki bama sonku Rumana? Me zaisa ku tafi inda ku kanku baku san ina zaku je ba? Kun san irin rayuwar da zaku fad'a ne? Kun san halin da zaku jefa kanku a ciki? Rumana ki auna maganar nan a mizani ki gani, ya dace ku bar garin man? Haba mana, haba dan Allah, idan ma Ikram ce ta baki wannan shawarar to kar ki biye mata saboda ita yarinya ce, bata san me zai iya faruwa a gaba ba, ke kuwa fa?"
"Mama Talatu da kin yi hak'uri da maganganun nan saboda kawai kina b'annar yawunki ne, idan mun hak'ura mun zauna, a gidanki zaki ajiyemu? Kin san dalilin tafiyarmu? Ko ban fad'a miki ba na san kin san irin zaman da muke a cikin gidan can, to akan me? Kaina aka fara haifar 'yar shegiya? Ace na tare da kai shi zaina maka wannan muguwar k'iyayyar?" Kuka ya kufce mata.
Ajiyar zuciya Talatu ta sauke ta ce "na san komai Ikram, amma ni na amince ku dawo gidana ku zauna, wallahi har cikin zuciyata kuma na amince d'in, kar ku ji komai, da dai ku tafi inda ku kanku baku sani ba ai gwara ku zauna a nan d'in."
Kai kawai Umma ta gyad'a alamar rashin amincewa, "Talatu kin manta irin tsanar da mai gidanki yama Ikram? Kin manta yanda Ikram ke yawan kawo min k'arar yaranki akan goranta mata rashin uba? Da zarar muka koma gidanki abin k'ara ta'azzara zai yi, kin ga kuwa an yi ba'a yi ba ke nan."
"Duk na san wannan Rumana, amma ai gida nawa ne ko? Nawa ne da kud'ina na ginashi ba na babansu ba ne, sannan kuma ban ce shi zai ciyar da ku ba. Yara kuma ai ba su suka haifi kansu ba haifarsu na yi."
Ikram cikin kuka ta ce "ki yi hak'uri Mama Talatu, ba wai mun k'i amincewa ba ne, amma alk'awari ne muka d'aukarwa kanmu cewa yau zamu bar garin nan ba ma sai gobe ba, idan akwai wani laifi da muka miki b'oyayye da sananne ki yafe mana, kin san D'an Adam ajizi ne."
Kuka ita ma Talatu ta fashe da shi, da k'yar ta iya saita kanta ta ce "tabbas na san an guma maku da yawa, kuma tun da har kuka yanke wannan hukuncin to abu yayi nisa, na yafe maku nima kuma ku yafe min. Ungo wannan." Ta fiddo kudi daga aljihun skirt d'inta, "kud'inki ne dama na zo na kawo miki, na wurina da na wurin Hansatu, ga wannan kuma sai ku k'ara ku biya kudin mota." Ta mik'a wa Ikram.
"Mun gode k'warai Mama Talatu, Allah ya baki ladar ya saka miki da alkhairi." Ikram ta fad'a kuka sosai ta ke yi.
"Ameen Ikram, Umma Rumana Allah ya k'addara saduwa." Da sauri ta bar wurin dan bata son ganin tafiyarsu. Su kansu kuka su ke sosai, basa son tafiyar amma kuma basu da wani zabi da ya wuce hakan, ko ba komai wata k'ila zasu samu sassauci a wannan lokacin.
Tafiya kad'an suka yi suka samu mashin guda d'aya, d'an dakatawa ya yi har aka samu cikon daya sannan suka ce ya kaisu cikin garin Kano inda zasu samu tashar mota.
Ni Amrah na ce "to Goggo Indo sai ki zuba ruwa a k'asa ki sha, yau dai su Ikram sun bar miki gida ki sakata ki wala, amma kuma ki sani, duk yanda mutum ya ke yana da rana, kar ka tab'a rainashi saboda baka san ranar da zai maka ba!"
******
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.