*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)54~ Duk da cewa bai gano gidajen ƴan majilisun ba amma hakan bai bashi damar tambayar Smart ba, saboda surutunta ya yi yawa, tun ɗazu daurewa kawai ya ke.
Wani mutumi ya tambaya bayan sun fita Gesse, kwatanta masa ya yi yanda zai gane, babu wuya kuwa sai gasu wurin gidajen. Faka motarshi ya yi ba tare da ya ce masu ko uffan ba.
Smart ta ce "Yaa Haidar sai an ɗan matsa gidan nasu yana daga gaba."
Tada motar kuwa ya yi ya nufi ta inda ta masa nuni ɗin.
"Ya yi nan." Ta faɗa da sauri dan yana neman zarcewa.
A daidai ƙofar gidan ya faka nan suka hau fita daga motar, Miemie ce ta buɗe booth ta fiddo ƙulli biyu na kayan sannan suka nufi shiga gidan.
Babban gida ne flat nan suka doshi bakin ƙofar da zata sadasu da cikin gidan.
Da sallama suka shiga su duka, wata kyakkyawar mata ce zaune sanye da wani jan material a jikinta. Har ƙasa suka duƙa suka gaishe ta da fara'a ta ce "Sadiya...sannunku da zuwa. Ku isa ɗakin nasu suna ciki."
Kai tsaye suka doshi ɗakin su Candy, babban ɗaki ne mai irin ƙananan gadajen nan guda biyu kamar na ƴan yara, wanda da ka shiga ne farko Munay da sauri ta rungume ƙawarta tana faɗin "Ƙawata Ashnur..." Itama Ashnur ɗin ta rungume ta da farin ciki, alamun dai dama can ƙawaye ne.
Khadija Candy data duƙufa rubutun novel ɗin *Khadijatu* ta ɗago kanta jin hayaniyar su Ashnur. Ganin ƙawayenta yasata sakin murmushi ba tare data shirya ba.
"Abun dai kamar a mafarki. Smart su waye na ke gani haka wai?"
Smart ta ce "Nima dai haka na faɗa Candy. Ke sauri mu ke jiranmu a ke. Ga wannan ke da Ashnur." Ta miƙa mata ledojin guda biyu. "Kayan saka ranar Ikram ne. Idan an fitar da ashobe sai in turo miki hotonshi ta watsapp."
Da murna Candy ta karɓa tare da kiran Ashnur don ta zo ta gani, zuwan kuwa ta yi itama ta hau murna.
"Bari mu tafi. Gidan su Hanee zamu je daga nan." Miemie ta faɗa.
"To mu je in rakaku. Kun gaisa da Mama ko?" Candy ta tambaye su.
Ikram ce ta bata amsa da "Mun gaisa a falo."
"To ya yi kyau." Ta zira hannunta cikin wardrobe ta jawo dogon hijabinta.
Gaba suka yi ta bisu a baya, Ashnur da Munay *Aminnan juna* suka mara masu baya.
Ledar ta miƙawa Mama ta ce "Mama ga wanann, kin ga amaryar nan." Ta nuna Ikram.
Duƙar da kai Ikram ta yi cikin kunya, Mama ta ce "Yaushe ne bikin?"
Sai a lokacin ma Candy ta tuna da basu faɗa mata yaushe ne bikin ba. Miemie ta ce "Ƙarshen April ne Mama."
"To Allah ga nuna mana lafiya." Maman ta faɗa cikin fara'a.
"Bara in rakasu gidan su Hanifa su kai mata Mama." Khadija ta faɗa.
"To a dawo lafiya. Ki gaishe da Hajiyar tasu."
Suka fita, har Haidar ya juya alamun su kawai ya ke jira su wuce.
"To ya za'a yi da wancan ɗan girman kan?" Husnah ta faɗa.
Harararta miemie ta yi ta ce "Yaa Haidar ɗin kike cewa ɗan girman kai?"
Dafe bakinta ta yi ta ce "Afuwan ƴanmata. To ba ɗan girman kai ba." Ta yi murmushi.
Ikram ce ta ce "Bari in ɗauko. Su nawa ne gidan?"
Khadija ta ce "Su biyu ne ƴanmata, sai kuma yayarsu ɗaya mai aure amma itama na san zata je. Sai ki ɗauko guda ukun."
Nufar booth ɗin ta yi nan ta jishi a rufe, bakin ƙofar ta koma ta ce "Yaa Haidar a rufe booth ɗin ya ke."
Bai tankata ba kawai ya buɗe sannan ta koma ta ɗauko.
Babu nisa gidan, nan da nan suka isa gidan su Haneefa Usman.
Bayan sun shiga da sallama suka iske ƴan matan biyu da yayar su Hanee mai aure, sai manyan samari biyu, wanda da alama duk yayyensu ne.
Haneefa ce ta fara ganinsu da murna ta miƙe tana faɗin "Ahhhh, ku ne da kanku? Sannunku da zuwa." Da murna ta yi maganar.
"Ahh sannunku da zuwa. Ku zauna mana." Wata mace ta faɗa wadda da alama ita ce mai auren.
Zama suka yi, wani namiji irin masu surutun nan ya ce "Ƙawayenmu sannunku da zuwa. Ƴan mata kin yi kyau." Ya kalli Ikram ya mata murmushi.
Gyaɗa kai kawai ta yi, amma wannan bai ishe shi ba sai da ya dawo kusa da ita ya zauna.
Ruwa Hanee ta kawo masu sannan ta zauna murna fal a ranta.
"Kun ga wannan ita ce Aunty Lubie, wannan kuma Aunty Hauwa." Ta nuna masu yayyen nata.
"Aikam mun gane Aunty Lubie dai, Aunty Hauwan dai ce bamu gane ba." Ikram ta faɗa.
Miƙa masu ledoji ukun suka yi sannan suka masu bayanin ko na menene. Haneefa ta ce "Kuma gashi umma bata nan bare ku gaishe ta."
"Babu komai ai, idan ta zo kya gaishe ta. Sauri mu ke ne jiranmu a ke." Miemie ta faɗa.
Bankwana suka ma su Aunty Lubie sannan suka fice, abin kirki suka samu Haidar ya matso da motar har wurin gidan su Haneefa.
Bankwana suka yi da su Khadija Candy kowa ya nufi gidansu.
Daga nan suka ci gaba da bin gidajen ƙawaye suna kai masu kayan, kuma abin mamaki ko kaɗan Haidar baya takurasu, duk inda suka je sai ya gansu, ko kaɗan kuma ranshi baya ɓaci, idan ma dai ya ɓaci to baya nuna masu. Sanda ya tabbatar zasu buƙaci abinci, da kanshi ya kaisu Rahama eatery, kowa ita ta zaɓi abin da ta ke so aka kawo mata, shi kam wai dan kar su rainashi ko abincin bai ci ba, sai da suka gama aka mashi total dubu huɗu da ɗari biyar, zarowa kawai ya yi ya biya sannan suka kama hanyar wani gidan.
Sai yamma liƙis sannan suka gama, lokacin har magrib ta kusa suka sauke Smart da Munay, godiya suka masu sosai sannan suka kama hanyar Sokoto Birnin Shehu.
Sai kusan ƙarfe takwas suka isa, Miemie na faɗin ya kaita gida amma ko saurararta bai yi ba kawai ya wuce gidan Momy. Horn ɗaya mai gadi ya buɗe gate, parking space ya nufa ya faka motar sannan ya jefawa Ikram key ɗin ya ce "Ki miyar dasu gida, ni na gaji." Kawai ya wuce abinsa.
Murmushi Miemie ta yi ta ce "Ina son irin haka."
Ikram kuwa bata ce komai ba sai ɗaure fuska da ta yi.
Husnah ta ce "Ai ina ga kaman mu yi salloli ko? Babu magrib babu isha."
Miemie ta ce "Hakane kam. Idan mun yi sai mu tafi gidan."
Ikram ta yi murmushi ta ce "Your wish is my command."
Suka fita daga motar tare da ƙarisawa cikin gida.
Momy ce zaune ita da Khalid suna firar rashin dawowar su Ikram ɗin. Momy na faɗin "Miƙo min wayata dai in kira Ikram ko lafiya suka jima har haka."
Kafin Khalid ya miƙo mata wayar Ikram ta ce "Lafiya lau mu ke, gamu Allah ya mana dawowa." Ta saki murmushi.
Itama momy murmushin ta yi ta ce "To barkanku da dawowa. Amma dai kam kun yi dare sosai."
Bayan Ikram ta zauna ta ce "Momy mun sha aiki wallahi. Buɗe motar da sauka kanshi wani babban aiki ne."
Momy ta ce "Sai haƙuri ai. Miemie da Husnah sai ta zo ta miyar da ku gida ko? Ku fara bani lambar iyayenku in kira na basu haƙurin rashin dawowarku da wuri."
Babu musu suka bayar da lambobin, nan momy ta kirasu ta basu haƙuri, duka amsa ɗaya suka bata da babu komai.
Bayan sun yi salloli Ikram ta fito sanye da hijabi zata miyar da su. Khalid ya ce zai rakasu saboda idan zata dawo ita kaɗai ce kuma gashi dare ya yi.
Taren kuwa suka tafi, Ikram na tuƙi sai Khalid zaune a gaba. Husnah da Miemie a baya sai firar yanda rarrabar tasu ta kasance su ke.
Bayan sun sassuke su suka kama hanyar dawowa gida, a nan Khalid ke ba Ikram labarin yanda aka yi da Alhaji Kallah da Umari.
"Ashe wai bayan an kama Umari ɗin, da kanshi ya faɗa masu wai yana da taɓin ƙwalwa, Hajia ma ta je ta bayar da shaidar hakan, ni kuma da yake sanda na je wurin Alhaji Kallah na bugi cikinsa ya bani labarin wai haukar ƙarya ce, kisan kai suka yi a Italy shine ya saki kuɗi aka ƙyale shi, wai dalilin dawowarshi Nigeria ke nan lokacin gama karatunshi bai yi ba.
Shi kuma Alhaji Kallah da kanshi ya yi confessing (ya tonawa kanshi asirin duk mugayen abubuwan da ya yi.) Shiisa sojojin suka sauƙaƙa masa suka turashi kotu, a can aka yanke masa hukuncin ɗaurin rai da rai a gidan yari, saboda yasa a yi kisan kai, ga kuma sace ni da yasa aka yi kwanaki, sannan kuma ya so ya taushe haƙƙin marayu. Umari ma hukuncin kisa aka yanke masa, saboda shima da kanshi ya tabbatarwa kotu cewa ya yi kisan kai a ƙasar Italy. A taƙaice dai kin ji yanda aka yi da mutanen biyu, sannan kuma duk wata dukiyarsu ashe namu ne, da kanshi ya faɗa har gidan da ya ke ciki. Tausayin Hajia yasa muka yafe masu gidan kawai, saboda babu inda zasu zauna, idan muka tashe su, ga kuma innocent Rabi'a."
Jinjina kai Ikram ta yi ta ce "Hakan ya yi kyau ai. Ka ga sai ya zama ishara ga mutanen gaba."
A daidai nan suka iso gida mai gadi ya buɗe masu gate suka faka motar.
A falo momy ce kaɗai tana kallon shirin Agent Raghav, kasantuwar duk ranar lahadi da ƙarfe takwas a ke farashi.
Hayaniyarsu momy ta ji ta ɗan murmusa har suka ƙariso.
"Momy mun dawo." Ikram ta faɗa. "Wash Allahna! Yunwa na ke ji kuma ba ta abinci ba."
Dariya momy ta yi ta ce "Dama har wata yunwa ke akwai wadda ba ta abinci ba?"
"Ehh wallahi momy. Bana son komai amma kuma yunwa na ke ji."
"Ahh ba yunwa kike ji ba kam. Je ki fridge ki duba ina ji akwai nutri milk sai ki sha, amma ba zaki kwanta haka da yunwa ba." Momy ta faɗa.
Da sauri kuwa ta miƙe ta nufi fridge ɗin a daidai shigowar Haidar wurin ya biyo ta ƙofar kitchen, kuma shima nutri milk ɗin ya zo nema, gashi kuma ita ke nan guda ɗaya ta rage.
Ko da ta buɗe fridge ɗin ta ɗauko shima ya zira nashi hannun zai ɗauko sai wayam ya ji babu komai. Kallon ta hannunta ya yi sannan ya ɗauke kanshi ya ce "Babu wata?"
Ɗauke nata kan ta yi itama ta ce "Ehh." A taƙaice.
Falo ya nufa ba tare da ya sake furta komai ba, sai dai kuma ya bata tausayi kasantuwar bai ci komai ba tun da suka tafi ruwa ne kawai abincinshi, dama nutri milk ɗin ce kawai ya ke sha idan dare ya yi, saboda shi kanshi ma ya ke siyowa duk wata.
Bayan ya isa falon ta sauke ajiyar zuciya tare da bin bayanshi itama ta isa falon.
Zaune ya ke fuskar nan babu annuri, ya ci ya ɗoshi ma ya fuskarsa ta ke barin kuma yana jin yunwa?
Kamar ba zata iya ba kuma dai ta daure ta ce "Yaa Haidar gata ka sha."
Bai ko kalle ta ba duk da yana so ya ce "No, ki sha kawai."
Ta san yana so sarai hakan yasa ta sake maimaita "Karɓa ka sha, ni sai in dafa indomie."
Karɓa ya yi kuwa cikin sanyin murya ya ce "Thanks." Kawai sannan ya buɗe ya fara sha.
Khalid ya ce "Ana yi ina jin daɗi."
Momy dai murmushi kawai ta yi, a ranta ta ce 'Da alama sun fara fahimtar juna.'
Ikram kuwa kitchen ta nufa ta dafa indomie sannan ta fito riƙe da plate ɗin.
Tana zama Khalid ya matso kusa da ita ya ce "Nima zan ci." Ya ɗan kashe nata ido ɗaya.
"Sai ka zo ka ci ai, ka zata ko zan hanaka ne?"
Momy ta ce "Ƙarya fa ya ke baya jin yunwa. Yanzu babu daɗewa ya shigo da gasasshiyar kaza muka ci tare da shi. Kawai dan ya rabaki da abinki ne tun da ya ga kin ba yayanku nutri milk."
"Hmm." Kawai Ikram ta faɗa tare da fara kai indomie a bakinta.
Sai kusan ƙarfe goma sannan Haidar ya miƙe ya ce "Momy na gaji sosai wallahi, kuma gashi gobe akwai aiki."
Momy ta ce "Sannu. Sai ka je ka kwanta ai, yanda zaka ji daɗin tashi ka samu wadataccen bacci."
"Momy ina naga ta bacci yanzu? Wani research ne na ke son yi. Ina tunanin zan tafi wani course nan da wata uku idan Allah ya kaimu." Ya faɗa cikin muryar gajiya.
"Wane irin wata uku kuma? Ke nan daga yin aurenka sai ka bar matar kawai ka tafi wani course?"
Cikin murya ƙasa-ƙasa ya ce "Momy to ya zan yi? Sai ta yi haƙuri, idan kuma ba zata iya ba sai mu tafi tare. India ne zan je."
Khalid ya yi dariya ya ce "Shi ke nan an yi a dai-dai, sai ku yi honey moon ɗinku a can kawai."
Harararshi Haidar ya yi bai ce komai ba. Momy ta ce "To ita kuma karatun nata fa?" Sai kuma ta yi shiru, saboda a tunaninta har yanzu Haidar bai san wacce zai aura ba.
"Sai ta aje idan dole sai ta bini." Yana gama faɗin haka kawai ya bar ɗakin.
Gyaɗa kai momy ta yi ta ce "Allah ya kyauta maka. Kai wannan matarka na tattare da wahala. Ikram ƴata sai kin ringa kai zuciyarki nesa, shiisa ma na zaɓa masa ke a matsayin abokiyar rayuwarsa, dan na san zaki yi haƙuri da duk halayensa, tun da dai kin riga da kin fahimci komai dangane da shi, idan ka san halin mutum kuwa sai ka ci maganin zama da shi."
Shiru Ikram ta yi tana sauraren momy.
Kallon Khalid momy ta yi ta ce "Kar ka manta gobe idan Ikram ta dawo makaranta zaka kaita ta yo National Passport tun da ni ina da. Idan kun dawo da wuri daga nan sai ka binciko mana kuɗin Dubai ɗin nawa ne? Sai a yi visa kawai."
Khalid ya ce "To Allah ya kaimu momy. Barin tafi dai nima in kwanta, cikin magungunan nan da na ke sha akwai mai kashe jiki sosai."
"To Allah ya sawaƙe ya ƙare mu da lafiya baki ɗaya." Momy ta faɗa itama ta miƙe.
"Ikram kina nan? Ni dai bacci na ke ji."
Ikram ɗinma miƙewar ta yi ta ce "Nima barin tafi kawai. Akwai School gobe."
Kashe kallon ta yi sannan ta nufi ɗakinta tana miƙa alamun gajiya da kuma bacci da ta ke ji sosai.***
*Bayan sati biyu**Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid*

YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.