*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
(NWA)
2018_Gareki masoyiyar *RAZ* Asiya Maman Nabil. Hakika sakonki ya iso mana kuma mun ji dadinsa. Ga amsar tambayoyinki: Ta farko, sakon ya zo mana, kin shiga ranmu muma kuma muna kaunarki. Na biyu, bamu kammala littafin *MASARAUTARMU* ba bisa wani dalili, amma insha Allahu muna daf da ci gaba da kawo maku shi. Da fatan sakon zai isar miki. Mun gode._
11~ Ba'a wani d'auki lokaci mai tsawo ba aka sallaci Mallam, nan da nan aka kaishi gidanshi tabbatacce.
Kuka sosai Ikram ke yi, banda Ummanta da har yanzu ko d'is d'in hawaye babu, sai kukan zuci, wanda ya fi na hawaye ciwo.
Goggo kuwa zaune ta ke sanye da hijabi tana karb'ar gaisuwa, sai kuka ta ke wanda zan iya kiransa da kukan munafurci. Danginta suna bata hak'uri had'i da nasihu kala kala akan juriya da hak'uri.
Ikram da Ummanta tare su ke zaune, su kam babu dangi sai dai abokan arzik'i, wata k'awar Umma ce ke masu nasiha da "duk kan mai rai mamaci ne, haka zalika duk mai rai sai ya dandani mutuwa. Ku yi kuka ba zan hanaku ba saboda ku rage zugi a cikin zukatanku, sai dai kuma kar kuyi kuka mai hade da kururuwa irin wanda addinin musulunci ya hanemu, manzon Allah (SAW) ya kawo mana wani hadisi cewa; ana yi wa mamaci azaba da kukan wanda su ke raye. Mallam Mahmoud mutumin kirki ne, kowa ya shaidesa akan kyawawan halaye, babu wanda zai bud'e baki ya yi tir ko Allawadai da ko d'aya daga cikin halayensa. Addu'a kawai zaku masa tare da fatan ku yi irin mutuwarsa, wadda babu wahala sosai wurin ajalinshi, sannan kuma ku yi fatan samun irin shaidar da ya samu, saboda shaidar mutane ma tana da matuk'ar muhimmanci. Yanzu addu'arku ita ce ya fi buk'ata ba kukanku ba, saboda kukan babu abin da zai amfaneshi, addu'arku kuwa babbar kyauta ce a gareshi, ta hanyar haka ne kawai zaku iya biyansa a kan abin da ya maku kafin ya rasu."
Murmushin karfin hali Umma ta yi ta ce "mun gode sosai Ramatu, Allah ya baki ladar."
"Ameen" duka matan wurin suka fad'a.
Can na kuma hango Goggo sai murje murje ta ke k'asa tana kuwwa da k'arfi tana fad'in "ka dawo garemu mallam, muna k'aunarka ba zamu juri rashinka ba. *kai ne gatanmu* (novel by Sodangi) ka dawo garemu."
Abinku ga dangi duk jahilai, sai ma masu tayata ta samu, sai da suka hantse da kukan gulma sannan suka daina.
Sosai su ke samun abincin sadaka amma Goggo bata ba Ikram, sai dai idan ta ba Ummanta su ci tare, tun yanzu sun fara fuskantar tsangwama daga gareta bama a yi nisa ba.
Bayan an yi sadakar uku kowa ya watse, sai dai da'id'aikun mutane wanda basu samu damar zuwa ta'aziyya ba sai daga baya.
Baki d'aya rayuwa ta fara jagule masu, abincin da zasu ci ma wahala ya ke masu, daidai da ruwa wannan sai Ikram ta fita ta jawo, saboda wata irin rijiya ce ke a k'auyen mai zurfi sosai, sannan kuma ko yaushe akwai layi, dama can k'auyen masu wahalar ruwa a ke, Mallam ne ya ke zo masu da mai ruwa duk sati ya biya kud'i a juye masu, to wannan karen duk 'yan zaman makoki sun b'arnatar da ruwan.
Abu wasa ba wasa ba rayuwa ta zame masu masifa, cikin lokaci kad'an Ikram ta fara sauya kamanni, ta rame sosai kamar ba ita ba, yo to dole Ikram ta rame, a yini da wuya su samu su ci sau d'aya, 'yan kud'ad'en da Ummanta ke bin mutane na sana'arta sun rik'e duk an hanata. Duk da wannan halin da suke ciki bai hana Ikram zuwa makaranta ba, saboda suna daf da fara zana jarabawar SSCE, nan da wata uku suke tsammanin farawa.
Ikram ce ta shirya da sassafe zata tafi makaranta, cikin shigar blue and white hijab, hijab din nata har ya zama light brown tsabar datti, to babu wadataccen ruwa barin kudin siyen sabulun wanki, ita kam ta amince da duk shigar da zata tafi in dai zata samu ta cika burinta na kammala Secondary School. Bayanta ma Ummanta bankwana ta fito tana kokarin fita Goggo ta fizgota da karfi har sai da tsohon hijabinta ya yage.
Juyowa ta yi cike da takaici ta ce "me kike yi haka Goggo? Me kike nema a wurina da zaki fizgeni har ki b'arka min hijabi?"
Da masifa Goggo ta ce "na ajiye kud'ina ne na duba ban gani ba, kuma ni dai na san babu wanda zai d'aukesu sai ke ko uwarki, ke na ma fi zarginki saboda tun da na ke da uwarki bata tab'a yi min sata ba. To ai ba abin mamaki ba ne dan kin yi sata, 'yar shegiya ai komai ma zata iya aikatawa."
Kuka ke k'ok'arin fito mata ta samu ta danneshi da k'yar ta ce "to Alhamdulillahi tun da dai kin fidda uwata, ni kuma na amince ni ce na d'auka, sai a yi yanda a ke so da ni, kya iya yin kuli kulin kubura da..." Bata k'arisa maganar ba Umma ta ce "ya isa haka Ikram! Kin san bana son rashin kunya ko?" Shiru ta yi daga nan, Goggo ta ce "bar ta ta idar mana, wallahi Ikram in har baki canza hali ba kina dab da barin gidan nan, tun da dai ba gadonshi gareki ba."
Ta bud'e baki zata yi magana ke nan Ummanta ta mata alama da ta fita daga gida. Fitar kuwa ta yi k'ok'arin yi amma Goggo ta sake finciko hijabinta, "babu inda zaki tafi sai kin fiddo min kud'ina, ko kuma na tara miki mutane, har da abin da baki yi ba duk na had'a na k'uk'k'ulla miki."
A wannan lokacin kam Ikram ko Kallon Ummanta bata yi ba dan ma kar ta tsayar da ita, "Goggo ki sani ina baki girma a bisa wasu dalilai, na farko saboda kin girmeni, na biyu kuma kin yi rayuwa da kakata, kin kuma raini Ummana tun tana yarinya. Amma naga alama kina neman ki kureni, to wallahi girman nan naki ya kusa ya zube kasa, kuma in har ya zube babu abin da zai iya kwasarshi. Kudi kuma na dauka, ki tara min mutane na ga idan su mutanen basu da hankali, ko zasu yarda da abin da basu da yak'ini a kanshi, babu wata hujja da ta tabbatar da hakan." Ta buga tsoki tare da janye hijabinta ta fice daga gidan saboda tana neman makara.
Ga Umma Goggo ta juyo, ta inda ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba, "kuma wallahi sai ta fitar min da kud'ina, dan na san babu wanda zai d'auka sai ita, gidan uwar wa ta ke samun kudin zuwa makarantar? Ai akwai alamar tambaya a wannan lamarin."
"Ki yi hak'uri Goggo, amma wallahi Ikram bata sata, bata tab'a..."
"To uwar son 'ya, ahh to ki gwada min cewa ni ban tab'a haihuwa ba saisa ban san ciwon 'ya ba. Aikin b'ur wai in ji tusa, ku'dina kuma sai an biyani komai tsiyar mutum ehe."
Wucewa kawai Umma ta yi bata kuma fad'in komai ba, saboda kalaman Goggo ba kad'an d'in ci mata rai su ke ba, musamman kiran Ikram da ta ke da b'arauniya, dama Mallam kafin ya rasu ya fad'a masu dole sai sun yi hak'uri da zaman gidan.
Ko da ta koma d'akinta kuka ta fasa da k'arfi, saboda dama dan bata so Ikram ta ji kukanta ya sa ta ke b'oyewa. Kuka sosai ta ke, sai a yanzu ta ke kukan rashin mahaifinta, mahaifinta kuma gatanta. Ta rasa mahaifiya tun kafin ta san miye duniya, mahaifinta da ta tashi gabanshi, ya bata kulawa tare da gwada mata tsantsar soyayya shima gashi babu shi. Basu da kowa a halin yanzu, basu da mai kula da su, daidai da abincin cinsu wahala ya ke masu. "Bamu aje uwa ba barin uba a garin nan, babu dangin iya babu na baba, banda zallar azaba babu abin da muke tsinta a wannan garin. Ya zama dole mu barshi, duk da ban san inda zamu je ba amma dole mu tafi, mu tafi inda zamu iya rik'e kanmu tare da kula da rayuwarmu. Gwara mu je inda ba'a san asalin Ikram ba barin a ci gaba da goranta mata." Tana gama fad'in haka ta kuma fashewa da wani kukan mai sauti wanda har sai da Goggo ta ji ta shigo dakin.
"Idan kika ja cutarki ta tashi kin ga babu ruwana, rufin asirinki ki yi shiru dan ba zan iya asarar ko sisina na kaiki asibiti ba. Kuma wallahi yau dole a san na yi, saboda dole ki zab'a, ko dai Ikram ta fito min da kudina ko kuma ta bar gidan nan, na san zai yi wuya ki barta ta tafi ita kadai, to zaki iya kwasar tsommokaranki ki bita ga hanya nan."
"Ko baki fad'a ba Goggo dole yau zamu tafi mu bar gidan nan." Ikram ta fad'a tare da k'ok'arin shigowa d'akin. Kallon mamaki Ummanta ta bita da shi, wannan karan kam bata yi k'ok'arin hanata ba, ta ci gaba da fadin "wulakancin da kike mana ya ishemu haka, gashi kuma dama ba wani abu muke tsinta a cikin gidan ba, da me zamu ji? Da talauci ko kuwa da masifarki? Zamu tafi inda babu wanda ya sanmu, zamu gina wata sabuwar rayuwar a can." Ummanta ta ce "kuma ina mai tabbatar miki da cewa Ikram sai ta zama abin alfahari, ba ga ke kadai ba ma ga kowa insha Allahu, saboda tana da kyakkyawar zuciya kuma mai tsafta, irinsu ne Allah ya ke jin kansu musamman ma yanda ta tashi babu gata tun tana yarinya, ba ga 'yan wajen ba ba ga na gida ba. Na goyi bayan ikram, yau zamu tafi, yanzu ma ba sai anjima ba."
Suka hau harhad'a kayakinsu har da wanda ba wankakki ba. Sosai Goggo ta yi mamaki, saboda bata tab'a tsammanin haka ba, ko ba komai ta san basu da kowa a rayuwarsu. "To ku tafi d'in mana sai me? Ni daga ma na k'ara samun fili a cikin gida? Kun ga sai na saka 'yan haya, kud'i duk bayan wata d'aya. Ehh ku tafi Allah raka taki gona." Ta fice daga d'akin.
Babu wanda ya kuma fad'in komai sai had'a kayansu da suke yi, babu jimawa kuwa suka gama had'a komai, Ikram ta cire Uniform d'inta da suka yi sharkaf da ruwa, da kuma b'arkewa da hijabinta ya yi wanda shi ne silar fasa zuwa makaranta ta dawo gida.
A ka suka d'ora wasu kayan, wasu kuma a hannu suka fito daga d'aki. Goggo na tsaye sai rera wakar habaici ta ke ko a jikinta, basu ko koma ta kanta ba suka fita daga gidan.*******
Ku d'aure 'damararku masu karatu, yanzu labarin *shi ne sila* zai fara, saboda har yanzu bai zama silar ba...lol.
Na gode k'warai masoyana da irin kulawar da kuke bani, musamman *Mu sha karatu na RAZ,* Safura Garba na gaisheki lodi lodi.
@wattpad: PrincessAmrah

YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.