65

942 50 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Na gode ƙwarai ga wanda suka neme ni dan jin ko lafiya suka jini shiru? ba sai na tsaya ambato sunayen ba saboda suna da yawa. Allah ya bar zumunci, ina yinku sosai da sosai._


65~  Mutanen wurin na matsawa su miemie na isa wurin, da fara'a ta ke kallon amaryar ƙawarta har yanzu kallonta bai kai ga ganin ko waye angon ba.
   Miyar da kallonta ta yi ga angon, wa zata gani? Haidar ta gani fuskarsa ba yabo ba fallasa yana magana da wani abokinshi Saddam.
   Ƙara murje idonta ta yi wai a tunaninta ko ba dai-dai ta kalla ba.
   Tuni Ikram ta tsure ganin irin kallon da miemie ke ma Haidar na alamar tambaya.
     Kasa ko da motsi ta yi tana jin wani irin yanayi mai wuyar misaltawa.
    Da ƙyar ta samu ta fita daga wurin, tana fita ta haɗu da Marwan, dakatar da shi ta yi domin har yanzu bata gama gasgata abin ba, ji ta ke kamar dai ya tsaya wurin ne a madadin ango, wata ƙila angon wani laluri ya hanashi zuwa.
   Bakinta kawai ta ke motsawa amma ta kasa furta komai, ganin haka yasa Marwan cewa "Ƙawar amarya lafiya?"
    "Lafiya..amm..dama, wai Yaa Haidar ne angon Ikram?" Ta faɗa tana ƴan kame-kame.
    Cikin fara'a Marwan ya ce "Kema bata sanar da ke ba ke nan. Muma ɗin ai hakan ne a ɓangarenmu, Haidar bai faɗa mana ba sai da muka gane da kanmu. Ahh lallai fa Ikram bata kyauta ba, duk hidimar bikin nan wai baku gane ko wanene angon ba?"
    Miemie da tun sanda ya bata amsar da ta ke so ta fita hayyacinta bata kuma sanin abin da Marwan ke faɗi ba. Baki ɗaya ta faɗa can wata duniyar wadda ba ita ta kai kanta ba, tunani ne kawai ya kaita.
   Marwan kam yana gama magana ya shige ciki abinshi, dan a tunaninshi ai ba wani abu ba ne.
   Ita kuwa Miemie da ta koma tamkar mutum mutumi kasa motsawa ta yi, ta fi ƙarfin minti biyar a haka, kuma ta yi sa'a babu wanda ya zo gittawa, habkalin kowa na ga shagalin da ake yi, banda Ikram da Husnah wanda tun sanda suka ga fitar miemie hankalinsu ya tashi.
    Da ƙyar ta iya saita kanta, wani irin nannauyan abu ta ji ya tokare mata zuciya, sai dai kuma ta rasa ko menene, ta kuma rasa abin da zata yi wannan abun ya fita.
   A hankali kamar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ta ke taku, tun da ta bar wurin ko waige bata yi ba har ta isa harabar Hotel ɗin.
    Tsayawa ta yi cak sanadiyyar juyawar da ta ji kanta yana mata, wani mutum da matarshi wanda da alama matafiya ne suka shigo cikin hotel ɗin, ganin miemie ta yi tsaye a tsakiyar hanya yasa ya yi saurin taka burki da ƙarfi saboda sam bai kula da ita ba, haka kuma bai yi tsammanin wani zai tsaya a wurin ba tun da hanyar wucewa da mota ce.
    Duk da irin cin burkin da ya yi bai sa ko kaɗan Miemie ta motsa ba, ga ta dai lafiya lau a tsaye, idonta a buɗe ta ƙurawa wuri ɗaya kallo, amma kuma bata motsi.
    Matar ta ce "To, waccen ko makauniya ce?"
    Cikin takaicin mijin ya ce "Idan makauniya ce ai ba kurma ba ce, bayan na taka burki ai na yi horn. Sannan kuma ki ga kayan da ke jikinta, ga kuma sauti na tashi tun daga wajen hotel ɗin, da alama biki su ke fa."
     Ajiyar zuciya matar ta sauke ta ce "Barin tafi wurinta, tabbas akwai damuwa a tattare da ita." Ta buɗe motar ta fita. Shima mijin fita ya yi yana kiran matar a kan ta rabu da ita kawai su bi ta gefe su wuce amma bata saurare shi ba ta isa inda miemie ta ke.
     "Baiwar Allah! Lafiya kika yi tsaye a bisa hanya?" Matar ta tambayi Miemie.
     Bata ce komai ba sai kaɗa kanta kawai da ta yi wanda ya tabbatar masu da cewa ba kurma ba ce.
   "Akwai damuwa ne? Dan Allah ki faɗa min, in da taimakon da zan miki sai na miki."
    Sai a lokacin ne Miemie ta samu kuka ya fito mata, da sauri ta faɗa jikin matar tana faɗin "Mesa zata min haka? Mesa ta ɓoye min? Mesa bata bayyana min ba? Mesa take nunar min da babu wanda ta tsana sama da shi sai daga baya in ga shi ne angonta?" Kuka sosai ta ke yi dafe da zuciyarta da ta ke jin wani irin raɗaɗi, ga wannan nauyayyen abun har yanzu ya ƙi gushewa.
     Cike da tausayi matar ta ce "Yi haƙuri kin ji? Yanzu dai mu je mota sai ki mana kwatancen gidanku a miyar da ke." Ta jata suka nufi mota har da mijinta.
    Baya ta buɗe mata suka zauna tare, tana rungume da ita har yanzu sai faman rarrashinta ta ke, ita kuwa miemie ji ta ke kukan kanshi raɗaɗi ya ke ƙara mata a zuciya.
    "Ikram na yarda da ke amma abin da zaki saka min da shi ke nan? Ki auri mutumin da na ke ji ba zan iya rayuwa ba tare da shi ba? Ikram duk ɗaukar da na miki a zuciyata ashe ke ba haka kika ɗauke ni ba? Innaa lillahi wa innaa ilaihi raji'un!" Ta ringa kaɗa kanta a hankali.
    "Ki daina kukan haka nan kin ji? Ina ne gidan naku?" Mijin matar ya faɗa dan shi kanshi ya tausayawa Miemie a halin yanzu.
    "Kar ku kaini gida, dan Allah ku je ku yar da ni duk inda kuka ga dama. Ban ga sauran amfanin da rayuwata zata min ba, ƙawata aminiyata ta yaudare ni, kuma ta rasa wanda zata yaudare ni kanshi sai mutum mafi muhimmanci a gare ni."
    "Kar in kuma jin kin faɗi haka. A kan me? Namijin? Uwa ma ta rasa ɗanta ta haƙura barin ke dan kin rasa saurayi? Saurayin ma wanda bai damu da ke ba tun da har ya iya auren wata ba tare da kin sani ba? Ki faɗa mana gidanku yanzu."
      "Ina so in nisanta da gidanmu ne. Ku kaini gidan Yayata to, amma ba zan je gida ba." Miemie ta faɗa tana kuka.
    "A kan me ba zaki je gida ba?" Matar ta tambaye ta.
    "Saboda wani dalili da na barwa kaina sani. Na gode ɗwarai da taimakon da kuka min, amma dan Allah ku sauke ni a nan ni zan kai kaina gidan yayar tawa."
   Matar ta ce "Ba fa zamu sauke ki a nan ba. Ki faɗa mana sunan unguwar yayar taki mu tambaya a kaimu, saboda numa baƙi ne babu inda muka sani a garin nan."
      Sunan unguwar ta faɗa masu har yanzu kanta na bisa cinyar matar bata daina kuka ba har suka iso unguwar su Kareema, da ƙyar ta iya tashi zaune tana gwada masu hanyar da zasu bi har suka iso gidan Kareemar suka shiga ciki da motarsu bayan mai gadi ya buɗe masu gate.

SHI NE SILAH!Onde histórias criam vida. Descubra agora