*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Ina kuke members na *inspiring stories?* Yau shafin naku ne kyauta saboda ƙaunar da kuke wa littafin. Na gaishe ku sosai da sosai._
64~ A kasalance Ikram ta fito daga motar, Husnah ma ta biyo bayanta wadda ita kanta tana fargabar wannan rana.
Bayan sun shiga ciki suka ci karo da mutane wanda har ma sun fi na jiya yawa, kai tsaye ɗakin Khalid suka nufa amma basu samu momy a can ɗin ba.
Ɗakinta ta nufa inda danginta su ke, ta ga momy zaune cikinsu suna fira da wanda su ke ɗan jin hausa.
Murmushi Ikram ta yi tare da gaishe su. Momy ta ce "Me ya faru ƴata? Ko in zo ne?"
Zuwa ta yi ta zauna a jikin momy ta ce "Babu komai, ganin momyna kawai na zo."
Da fara'a momy ta ce "Na ji daɗi sosai autata. Ya kika baro su?"
"Lafiya lau momy. Barin tashi mu tafi momy. Zaku je dinner kuwa?" Ikram ta faɗa tana murmushi.
"Ai dole ki yi murmushi. Ban je kamu bane zan je dinner? Allah ya kyauta min. Sannan kuma dama ina son kiranki in faɗa miki, dan Allah kar ku yi dare sosai wurin dinner'n nan Ikram. Kar ku wace ƙarfe goma a tashi, kinga ƙarfe takwas sai ku tafi."
Husnah ta yi caraf ta ce "Ai dama Mama ta ce ba zata barmu mu yi dare bamu tafi ba."
Ikram ta ce "Ehh haka ta faɗa. Ba zamu yi ba insha Allahu momy. Na manta in ce miki ƙawayenmu fa duk sun iso jiya. Yanzu haka muna can tare wasu sai gobe wasu kuma sai jibi zasu koma."
Momy ta murmusa ta ce "To madalla abu ya yi kyau. Ki gaishe min su duka dan Allah. Akwai wata matsala?" Momy ta tambaye ta.
"Babu matsalar komai momy." Ikram ta faɗa haɗe da miƙewa ta ce "Mun tafi Momy. Sai Allah ya kaimu gobe kuma mu da nan."
Da fara'a momy ta ce "To Allah ya kaimu."
Ficewa suka yi suka nufi bakin mota Ikram ta tada suka fice daga gidan.
A mota Husnah ta dubi Ikram a tsanake ta ce "Tun ɗazu wani abu ke damuna Ikram. Shiisa kika ganni haka duk jikina ya yi sanyi."
Ikram na jin haka ta faka motar daga gefen tiki ta fuskanci Husnah ta ce "Ina jinki ƙawata, me ya faru?"
Husnah ta ce "Ikram sam abin da kika yi, ko kuma in ce kike kan yi bai kamata ba."
Cikin mamaki Ikram ta ce "Me ke nan Husnah?"
Dafa kafaɗarta Husnah ta yi ta ce "Ikram abin da kika ma Miemie ne bai min daɗi ba. Ta ya zaki barta a cikin duhu bayan kuma bai kamata ki ɓoye mata ba? Ikram ko kin san irin matsayin da miemie ta baki a cikin zuciyarta? Kin san kuwa yanda ta ke jinki kamar ƴar uwarta ta jini? Mesa zaki munafurce ta? Mesa zaki ɓoye mata abin da bai kamata ki ɓoye mata ba? Ya kike tunanin Miemie zata yi yau idan ta ga wanda zaki aura? Wane irin matsayi zata ci gaba da baki a cikin zuciyarta? Ikram idan ke ce aka miki haka zaki ji daɗi? Wane mataki zaki ɗaukar mata? Zaki ci gaba da kula da ita kamar yanda kike kula da ita a baya? A gabanki kin sha jin yanda Miemie ke faɗin irin son da take ma Yaa Haidar, har ikirarin ta ke ba zata iya aurar wani namiji bayanshi ba, ba zata iya rayuwa ba a duk sanda ta tabbatar da ta rasa Yaa Haidar. Ki duba wannan zancen Ikram, ki lissafa ki ga abin da ya dace."
Tuni hawaye ya gama wanke fuskar Ikram, kuka ta ke sosai har da shessheka, ta kasa furta komai.
Husnah ta kama bakin hijabinta ta gogewa Ikram hawaye amma kuma wani na sake fitowa.
"Ikram ni fa ban yi wannan maganganun da ki yi kuka ba. Na yi su ne kawai dan ki canza taku, ki san yanda zaki yi da miemie tun wuri."
Da kyarmar murya cikin kuka ta ce "Husnah duk abin da kika faɗa min gaskiya ne. Sai dai kuma bani da wani zaɓin da ya wuce na ɓoyewa Miemie. Har ga Allah ina ƙaunar miemie har cikin zuciyata, ƙauna irin wanda zan ma ƴar uwata ta jini. Amma sanin yanda ta ke son Yaa Haidar yasa na ɓoye mata gaskiya, dan ban san halin da zata shiga ba. Ni wallahi kamar ma kar a yi dinner'n...." Ta faɗa bisa jikin Husnah tana kuka sosai.
Husnah ta kamata ta tayar ta ce "Ko a yi dinner ko kar a yi dinner dole ne miemie zata gane. Dan haka ni a nawa tunanin gwara ma duk abin da za'a yi a yita ta ƙare yau ɗin nan, kuma yabzu ma. Idan zaki iya da mun koma ki je ki tinkare ta da maganar, duk abin da zai faru gwara ya faru."
Da sauri Ikram ta ce "Ba zan iya ba, ba zan iya ba Husnah. Tun da can ban iya faɗa mata ba sai yanzu? Gwara dai ta gani da idonta kawai."
Kai Hsunah ta gyaɗa ta ce "Akwai gwarama sosai nan gaba. Allah ya kyauta ya jishe mu alkhairi."
Daidaituwa ta yi bisa kujerar sannan ta tada motar suka ci gaba da tafiya, ga idanuwanta sun mata luhu luhu kukan da ta sha.
Haka suka koma gidan su Miemie duk jiki a sanyaye.
Bayan sun fita daga mota suka fara cin karo da Miemie da ta tarbo da wasu ɗawayensu da suka iso daga Burnin Kebbi.
Da gudu ta iso ga su Ikram tana masu oyoyo ta ce "Nima yanzu na dawo daga tarar su Ayeesherh Muhd...." Bata ƙarisa ba saboda fuskar Ikram da ta yi jajur, abunku ga mutum jar fata.
A razane ta ce "Me ya faru da ke Ikram?"
Sosai Ikram ta ke jin tausayin Miemie, hakan yasa wani kukan ya sake wanke mata fuska.
"Yaa Salaam! Ikram lafiya? Me ya faru?"
Rungumar Ikram ta yi tana ɗan bubbuga mata baya ta jata suka nufi side ɗin babansu har da Husnah.
Suna isa a falo suka zauna bisa doguwar kujera, nan ta ci gaba da tambayarta ko lafiya amma Ikram ta mata shiru.
Husnah ce ta ƙirƙiro murmushi ta ce "Nasiha fa su momy suka mata, yanda zata kula da mijinta da..." Ta yi shiru daga nan.
Murmushi Miemie ta saki ta ce "Ce min zaki kukan murna ne. Ni wallahi har hankalina ya tashi. Haba baby kuka yanzu ma kika fara, sai gobe kin ga da gaske dai barin momy zaki yi ki tafi gidan Ali gadanga ƙusar yaƙi."
Husnah ta ce "Nima dai abin da na ringa faɗa mata ke nan a cikin mota. Ki ga yanda fuskarta ta yi jaa dan Allah, yanzu surutu zaki jaama kanki cikin ƙawaye, kin san dai halin mutane. Dan Allah ki daina kukan nan."
Miemie ta ce "Husnah ku zauna a nan har sai fuskarta ta ɗan daidaita. Na san abin da zan faɗa masu can ɗin. Zuwa azahar insha Allahu zan kawo maku abinci. Duk abin da zaku yi ku yishi a nan." Ta fita tare da turo masu ƙofar ɗakin.
Miemie na fita Ikram ta kuma sakin wani kukan ta ce "Husnah ki ga yanda miemie ke rawar jiki duk dan ta faranta min rai amma ni ina burin baƙanta mata. Na shiga uku ni Ikram!"
Sosai Husnah ke rarrasarta, da ƙyar ta samu ta yi shiru sai ga Miemie ta shigo ta kunna masu kallo saboda su ɗan fidda kewa.
Film ɗin gugan ƙarfe ne a ke yi a African magic hausa, barkwancin da ake a cikin film ɗin yasa Ikram ta ɗan saki jikinta har suna ɗan fira da Husnah.
A haka har miemie ta kawo masu abinci, farar shinkafa ce sai miyar kayan lambu da kaza. A food flask ta sako masu sannan ta nufi dining area'n babansu ta kawo masu plate da cokulla, sannan ta ce idan suna da buƙatar ruwa da lemo su je su ɗiba a water dispenser, a frdige ɗinta kuma akwai lemu wanda zai ishe su, sanann ta fita.
A haka su Ikram suka ƙaraci zama part ɗin baban su miemie har aka yi la'asar, a lokacin ba laifi Ikram ta ɗan saki, amma fa ta ciki na ciki, tunani fal a zuciyarta na yanda zasu ƙare anjima.
Mislain ƙarfe biyar na yamma Miemie ta zo ta ce su koma can side ɗin haka nan, saboda har an fara ƙoƙarin yin make up kuma amarya bata dawo ba.
Sosai Ikram ta yi ƙoƙarin kawar da duk wata damuwar da ke addabarta. Da fara'a suka ƙarisa ciki.
A falo ta ga ƙawayensu da yawa sai fira a ke, wasu kuma wanda basu yi attending programs ɗin baya ba, suna kallon hotunan waya suna jin inama ace sun zo ɗin.
"Oyoyo ƙawaye na." Ikram ta faɗa da karfi yanda duk zasu ji.
Aikuwa sai murna da farin ciki, masu surutu na ma Ikram cancakwaton ta tafiyarta tun ɗazu sai yanzu ta dawo.
Miemie ta ce "Duk haƙurin da na ke baku a kan momy ta tsayar da ita shi ne sai kun mata shegen surutun tsiya?"
Wata daga cikin masu surutun ta ce "Ohh, haka fa. Na manta ai."
Murmushi Ikram ta yi ta ce "To sannunku da zuwa fa. Ya ban ga an hau shirye shirye ba? Allah ko Momy ta ce kar mu wuce ƙarfe takwas bamu tafi ba."
Husnah ta ce "Tun da dai da wuri za'a tashi ma ai gwara mu ƙoƙarta tafiya da wuri yanda zamu samu cashewarmu a wadace."
Ƙawayen suka saka shewa alamun sun gamsu da maganar da Husnah ta masu.
Nan fa suka hau shiri babu kama hannun yaro, Ikram kuma ta nufi ɗakin da Juwairiyya da Khaleesat su ke ta basu haɗuri a kan jinta da suka yi shiru.
Make up ta ma Juwairiyya mai kyau sannan ta ma Khaleesat ma, sosai suka yi kyau sannan ta ja kit ɗinta, Husnah kuma ta ɗauki tarkacen kayansu ita da Ikram wanda zasu saka, a lokacin ana ta kiraye kirayen sallar magrib.
Kai tsaye part ɗin baban su miemie suka wuce, dama key yana a hannunsu, mama kam har yanzu bata dawo daga gidan momy ba, wai idan akwai aiki su yi, amma ta tayar da momy ta bayar da komai za'a yi, na ɗaurin aure gobe, da kuma na mother's day.
Sai da Husnah ta fara yin sallah sannan suka hau kwalliya, dama Ikram ta yi wankanta tun sanda ta ke kuka ɗazu.
Sai da Ikram ta fara yi ma Husnah make up ɗin, saboda ta ce itama yau kwalliyar ikram ta ke so. Sosai Husnah ta yi kyau fiye da yanda idan ita ta ma kanta.
Bayan ta saka kaya Ikram ma ta saka nata sannan aka hau yin kwalliyar.
Yau kam light make up aka ma Ikram, saboda ita ta ce bata so yau wai tun da dare ne. Glitters kawai aka shafa mata a saman ido, kalar royal blue sannan aka shafa mata eye liner wadda ta fiddo da oval shape na idon Ikram. Bakinta kuwa kalar newd zalla aka mata wanda ya kwanta sosai, sannan aka ɗan shafa mata lip gloss mai shining a bakin.
Wani material ne aka ma wedding gown ta ji da faɗa, wadda idan aka saki rigar zata iya maimaita tsawonta har sau uku bisa ƙasa. Kalar royal blue ce da silver material ɗin, wanda baki ɗayanshi aka bishi da wasu irin flowers silver, kai ka ce dama can haka abin ya ke.
Head ɗinta royal blue ne, wanda ya ji haɗaɗɗen naɗi har ma ya fi na jiya yin kyau. Sarƙa da abin hannunta duk royal blue ne, sai ƴar purse da takalminta kuma silver colour.
Baki ɗaya Ikram ta gama tafiya da imanin ita kanta Husnah data shiryata ɗin. Saboda yau har da eye lashes Husnah tasa mata duk da ta nace bata so amma Husnah ta tilasta mata.
Husnah ma ta saka nata ankon wanda net ne silver zallah har head ɗin da zasu saka ma silver ne babu surki.
Sai da suka sha hotuna kamar kullum sannan suka fita daga side ɗin suka rufe, a lokacin har mama ta dawo ta fara azalzalar Miemie a kan ta je ta cewa su Ikram su fito haka nan, har takwas ta wuce.
Suna fitowa suka nufi side ɗin su miemie, kowa ya shirya dama su kawai a ke jira.***
Hotuna suka yi sosai kafin Ikram ta latsa kiran Marwan ta shaida masa cewa sun shirya su duka.
Marwan ya ce "Kai amarya tun yanzu za'a tafi dinner'n? Da dai an bari irin ƙarfe goma zuwa sha ɗaya sannan a tafi." Cikin zaulaya ya yi maganar.
Ikram ta ce "Ka rufa min asiri. Momy ma fa ai ta so a ce tun ɗazu muna can har an fara."
Marwan ya ce "Nima wasa na ke miki, haba waye zai so a ce ƴan mata na wurin party har tsakiyar dare? Ai ko mun yarda na san ango ba zai yarda ba ko dan amaryarsa."
Ikram ta ce "Kai dai ake ji yanzu. Mu kam ku hanzarta ku ɗauke mu dan bama son jira."
"Iyyee, lallai amarya ta ango. Ko da ya ke, amarya fa bata laifi ko da kin kashe Khalid ƙanin ango."
Yana faɗin haka Ikram ta ji wani irin bugun gaba da sauri da sauri, wanda da ƙyar ta iya controlling kanta. Har ga Allah tana kewar Khalid ba kaɗan ba, sai dai shi ɗin da alama ma ya manta da ita, tun da gashi tun da ya tafi ko sau ɗaya bai taɓa kiranta ba.
"Amarya kin yi shiru." Marwan ya faɗa. "Gamu nan zuwa yanzu. Ki ce masu su zama cikin ready nan da minti goma insha Allahu zamu iso. Sai ki zaɓi ƙawarki ɗaya wadda zaku shiga cikin mota tare da angonki."
"Uhm." Kawai ta faɗa haɗe da kashe wayar.
A ranta kawai ta yanke shawarar ita da Husnah zasu shiga, tun da ita ce ta san sirrinta, ta kuma san hanyar da zata iya taimakonta. Khaleesat da Juwairiyya kuma dama can su biyun kawai suka saba, dan haka sai ta ma Miemie ko Smart magana su samar masu mota su biyu.
Hakan kuwa aka yi, ta kira Husnah ta mata bayanin yanda suka yi da Marwan, ita kuma ta sanar da ƴan matan cewa ko wace ta shirya ga angwaye nan zasu iso yanzu.
Da zarar ka ga yanayin Ikram ka san bata cikin kwanciyar hankali, duk da irin kyaun da ta yi wanda tun da aka fara hidimar bikin bata yi kyau irin na yau ba. Tun ɗazu kuka ke son fitowa amma tana danne shi, saboda gudun zargi daga ƙawayensu.
Minti gomar kuwa na cika Marwan na kiran Ikram cewa su firfito, amma ita da wadda zasu tafi tare kar su fito yanzu, motarshi na can daga baya ya ɓoye dan kar kowa ya shiga, ango ne kawai a ciki.
Husnah ta sanar da su Miemie, nan kuwa suka tarkata ƙawayen duka kowa ta kama motar shiga. Har sai da wasu motocin suka tafi empty tsabar wadatuwar da suka yi, Marwan ne ya yi fafutukar samun masu motocin tun da dai Haidar ba wani sanin mutane sosai ya yi ba, sai ko likitoci.
Sai da kowa ya watse gidan ya yi tsit, a lokacin ƙarfe tara da rabi na dare, Marwan ya kirata ya ce ta fito gashi nan ya matso da motar ƙofar gida.
Fita suka yi ita da Husnah, sosai gabanta ke dukan uku uku, ji ta ke ranta na mata baƙi ƙirin.
A haka suka ma mama bankwana suka fita, wata motar ce daban ba ta jiya ba, wannan ta fi kyau sosai kuma ita bata da tint.
Da sauri Marwan ya fito ya buɗe ma Ikram motar, shiga ta yi a hankali bayan ta tattare rigarta ta zauna.
Tana zama sassanyar ƙamshin turarensa wanda ya haɗe da sanyin AC ya daki hancinta. Ɗago kanta ta yi a daidai lokacin da Marwan ya kunna hasken motar.
Kallon juna suka yi a tare, kowa na yaba kyaun da kowa ya yi. A tare kuma suka kawar da kansu, wanda dukkansu kunya ce dabaibaye da zukatansu.
Bayan Husnah ta shiga ta rufe ƙofar ne Marwan ya tada motar tare da nufar Karama Hotel inda za'a yi dinner'n.***
Suna isa kamar jiya Miemie ta nufo su, sai dai kuma kafin ta iso wata ƙawarta ta kirata a waya cewa basu gane wurin ba, da sauri ta ce da Smart "Je ki ce dan Allah kar su fito yanzu zamu sanar da shigowarsu sannan." Ita kuma ta nufi bakin gate ɗin hotel tana jiran isowar ƙawar tata.
Bayan Smart ta sanar da su ta koma ta faɗawa Dj da Mc, sannan ta dawo ta faɗawa su Ikram su fito gashi nan za'a kunna masu waƙar da zasu shigo. Miemie kuwa hallau tana can wanda ta ke jiran basu iso ba, har ta yanke shawarar zata tafi idan sun iso sun sake kiranta.
Nan fa masu videos da hoto suka taso suna nasu aikin, da waƙar *ranar kuke jira yau gata ta zo* ta Umar M. Sharif suka shiga da amarya da angon da kowa ya kasa cewa kowa uffan.
Bayan sun isa sun zauna ne masu hotuna suka zagaye su, Dj kuwa ya canza wata waƙar sai rawa ya ke shi kaɗai.
Ana cikin haka sai ga Miemie da ƙawar tata sun iso, miemie sai wangale baki ta ke ita a dole ana bikin babbar ɗawarta.
Tare da ƙawar suka kukkutsa wurin amarya da ango, suna isa Mc ya ce dan Allah masu ɗaukar hotuna su koma su zauna, domin ci gaba da shirye shiryen da suka kamata._To fa! Ko me zai faru?🤔 ku dai ci gaba da bibiyar labarin *SHI NE SILA!* insha Allahu zaku ji amsar komai._
*Team Ikramhaidar*
*Team Ikramkhalid*
ESTÁS LEYENDO
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.