*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)51~ Alhaji Kallah na zaune a babban parlor'nshi sai Hajiya matarshi, Umari da Rabi'atu duk suna zazzaune suna ta fira, inda Alhaji Kallah ranshi fal dan yanzu ya tabbatar da an gama aiwatar masa da abin da ya ke so. Yana son tabbatar da hakan ne yasa ya ɗauko wayarsa da niyyar ya kira Khalid. Latsa kiran nashi kuwa ya yi sai gashi bugu biyu ya ɗauka.
"Hello-salamu alaikum." Khalid ya faɗa cikin yanayin annuri.
Shiru Alhaji Kallah ya yi na tsawon lokaci ya kasa furta komai tsabar mamaki.
"Kawu ya gida ya iyali?" Ya jiyo Khalid ya jefo masa wannan tambayar.
Da rawar murya ya ce "A..uhm..lafiya lau su ke. Kuna lafiya?" Wata irin zufa ta keto masa.
"Lafiya garas kamar yanda ka ke kawu. Na san dai dama ka kira ne dan ka ji babu abin da ya faru da ni ko?" Ya saki wani shu'umin murmushi.
"To babu abin da ya faru dani ɗin. Lafiya ƙalau na ke." Ya yi bayyananniyar dariya.
Yama rasa abin da zai faɗa, 'to me wannan yaron ya ke nufi?' Ya tambayi kanshi. Kafin ya samo amsar tambayar ya sake ji ya ce "Kawu da alama dai duk yau baka kalli Sokoto tv ba. Dan Allah ka kunna yanzu idan kana gida, idan da hali ma har su Umari duka ka tattarasu su kalla. Akwai wani gagarumin abin da ya faru ne mai ban al'ajabi, na tabbatar kaima sai ya baka mamaki."
Nan ma dai shiru Alhaji Kallah ya yi yana mamakin ko wane abu ne ya ke so ya kalla a gidan tv na sokoto.
"Kar ka ji komai fa kawu, ba wani abu ba ne. Kawai dai abin ne akwai ɗaure kai. Dan Allah ka kunna yanzu, zan kiraka bayan minti talatin sai ka bani labarin duk abin da ya faru. Gobe kuma zan zo har gida ni da baƙina mu gaishe ka." Yana kaiwa nan ya katse kiran sai dariya ya ke. Dama a hands free Khalid ya saka, momy da Haidar duk suna saurarenshi.***
Yana gama wayar ba tare da ya tankama kowa ba kawai ya kunna tv. Yana kunnawa duka hankalin sauran ma ya dawo ga kallon.
Tun a head line ya ga an rubuta 'yanzu za'a kawo maku maimaicin shirinmu na mako, wato shirin _Abin mamaki_ wanda muka kawo ɗazu da misalin ƙarfe sha ɗaya na safe. Zaku saurari labaran ne daga bakin Fatima Bello Bala wacce kuka fi sani da Zarah bb.'
Sake da baki Alhaji Kallah ya ke jiran wane abin mamaki ne wannan za'a yi? Saboda duk sati a kan yi wannan shirin, wanda ake kawo manya manyan abubuwa wanda zasu bama kowa mamaki.
Wata kyakkyawar budurwa ce aka nuno ta sha veiling da pink ɗin mayafi ta fara bayani.
"A yau ne aka gayyaci waƙilanmu inda suka ɗauko mana wani rahoto wanda ya ba kowa mamaki. An kama wasu ƴan fashi da makami ne sun je gidan wani tsohon Attajiri Marigayi Alhaji Mohammadu, inda suka samu ɗaya daga cikin ƴaƴan gidan suka daka sosai sannan suka nemi hallakashi. Ga dai bayani daga bakinshi."
Nan fa aka nuno kaf abubuwan da suka faru har da bayanan da ƴan fashin suka yi. Daga sama kuma aka maƙala hoton Alhaji Kalla wanda ya sha babbar riga fuskarshi ta bayyana sosai, duk wanda ya ga hoton sai ya gane ko waye. Aka rubuta 'A yanzu haka dai maganar a hannun sojoji ta ke, inda ƴan sanda suka nemi a barsu da maganar amma sam suka ce basu yarda ba, yanda suka fara case ɗin da kansu to da kansun zasu rufe shi. Suna dai jiran kotu ta ƙwatarwa marayin haƙƙinsu kafin su fara aiwatar da nasu aikin.'
Tun da aka fara bayanin Alhaji Kallah ya kasa ko da motsi, zufa kawai ta ke ratso masa ta ko wace gaɓa ta jikinsa duk da raɓar AC'n da ke tashi a ɗakin. Tuni ya cire hular kansa ya kama fifita da ita, wani irin zazzaɓin tashin hankali ya taso masa.
Kallo sosai matarshi ke binshi da shi tana gwadashi da yatsa, tama kasa furta komai.
Umari ne ya yi ƙarfin halin faɗin "Kaima dai Abba ka yi kuskure, ai ba'a ba wawaye irin wannan ayyukan, inda ka sani ka sani na samo maka gwarzaye wanda koda za'a kashe su ba zasu taɓa tona maka asi..."
"Dalla rufa min baki." Alhaji Kallah ya faɗa cikin borin kunya. "Waye ya faɗa maka mutum yana tsallake ƙaddara? Dama can sai asirin nawa ya tonu ko da ace kai ka kawosu ɗin."
Cike da mamaki Hajia ta ce "Amma dai an ji kunya wallahi. Ashe Alhaji dama abin da kake yi ke nan? Ban taɓa tsammanin haka kake ba. Mutanen da suka amince maka, suka yarda da kai tun mahaifinsu yana raye amma da abin da zaka saka masu ke nan? Ka bani kunya wallahi. Yanzu me kake so mu faɗawa mutane? Na tabbatar yanzu kowa ya buɗe ya ga wannan babban abin kunya daka aikata." Cikin kuka sosai ta ke maganar. "Allah kaɗai yasan mutanen da zasu zage mu, ni idan kai kaɗai ma za'a zaga abin da sauƙi tun da duk wanda ya jawo ruwa shi ruwa kan doka. Amma na tabbatar har da iyalanshi duka za'a haɗa a zage, saboda kowa ya san irin kyautatawar da Alhaji Mohammadu ya mana kafin ya rasu, ya jawo mu inuwa amma ka jefa iyalansa rana Alhaji. Ka faɗa min yanzu ya kake so mu yi? Sojoji fa suka shiga maganar ba ƴan sanda ba, idan su ne da an basu kuɗi maganar zata iya mutuwa. Gashi yanzu an yi ba wan ba ƙanin, babu kuɗin kuma bamu san abin da zasu maka ba." Ta ƙara fashewa da kuka tare da zama da ƙarfi bisa kujera ta dafe kanta.
Rabi'atu ma kukan ta ke sosai, yayin da Umari ya yi wuƙi wuƙi da idanu yama rasa abin yi.
"Duk ta baya ta rago, mai faruwa dai ta faru." Alhaji Kallah ya faɗa idonshi ya yi jajur kamar wanda ya sha kuka.
Kafin ya ankara wayarshi ta yi ringing, ko da ya duba ya ga Khalid ne ƙin ɗauka ya yi ya miyar kan kujera ya aje. Sai da ya kira sau uku amma Alhaji Kallah baya ɗauka, sai a na huɗu ne Hajia ta ɗauka ta saka a hands free ta ɗaura wayar a bisa centre table.
Dariya Khalid ya tulle da ita da ƙarfi sosai ya ce "Ina fatan ka ga komai Kawu Kallah." Da ƙyar ya yi maganar saboda dariya sosai da ya ke yi.
Kasa faɗin komai Alhaji Kallah ya yi. Khalid ya ci gaba da faɗin "Ka san haka Allah ke nashi ikon. Ka basu izinin su kashe ni kar ma su bari a samu labari game da gawata, da Allah ya tashi taimakonmu sai ba'a kashe ni ɗin ba. Alhaji Kallah ke nan! Kai kana tunanin kowa ne mai ƙaramar ƙwalwa kamarka?" Khalid ya ɗaure fuska kamar ba shi ne ya gama dariya sosai ba. "Sai da muka gama planning ɗin komai kafin na zo na tinkare ka da maganar dukiyarmu. Asirinka ne ya tonu cewa kai ne ka saka ɗanka Umari ya sace ni aka kai can gidan gonarka na kusa da Shagari. A tunaninku ko asirinku ba zai taɓa tonuwa ba. Sai dai kuma kun yi kuskure! Saboda ba kullum a ke kwana gado ba. Sannan kuma dare dubu na ɓarawo, rana ɗaya tal ta mai kaya. Dan haka ka saurari zuwanmu gobe ni da lauyanmu, idan ka bamu haƙƙinmu cikin ruwan sanyi to falillahil-hamdu, idan kuma baka bayar ba dole sai an je kotu to hakan ma dai ba damuwa ba ce." Khalid na gama faɗin haka ya kashe wayar.
Cike da takaici Hajia ta ce "Girma dai ya faɗi wallahi. Ka ga irin girman da yaran nan su ke baka su da mahaifiyarsu. Amma ka ji yanda Khalid ya ke faɗa maka baƙaƙen maganganu, kuma wallahi ko kaɗan ban ga laifinsa ba, dan idan ni ce ma abin da zan faɗa maka sai ya fi wanann ciwo. Ka ga sai ka zama cikin shiri, zai zo da lauyanshi a ƙwatar masu haƙƙinsu, sannan kuma ka yi zaman jiran sojoji, dan da alama abin ba zai yi kyau ba." Ta tashi ta nufi ɗakinta cike da haushin mijinta wanda ya kasance ɓoyayyen munafuki.
Rabi'atu ma bin bayanta ta yi tana kuka sosai, musamman yanda ta ke mutuwar ƙaunar Haidar, a yanda ta ke sonshi inda ace ta ji sanda mahaifinta ya saka a yi da sai ta yi yanda ta yi ta sanar da su gaskiya.
Umari ne ya iso inda mahaifinshi ya ke ya dafa kafaɗarshi ya ce "Kar ka saka damuwa a ranka Abba. Ina mai tabbatar maka da babu abin da zai faru da kai. Akwai wani plan in dai ka bishi to komai zai warware." Nan fa ya fara masa magana ƙasa ƙasa, wadda duk iya kokonton mai ɗaukar rahoton dole ta haƙura ta ƙyale su, saboda ta kasa gane abin da su ke faɗi, kawai dai ta san cewa wani mugun abin ne su ke ƙullawa.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.