*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Wannan shafin na d'aukeshi sunkutukum na kyautar da shi ga members na *RAZ NOVELLA da kuma MU SHA KARATU...NA RAZ.* Nagode k'warai da soyayya. ILYSVM._
18~ Ranar litinin da sassafe Ikram ta shirya kamar yanda Momy ta umurceta, kai tsaye kitchen ta nufa, ta samu har Naana ta dafa mata indomie da k'wai tun da dama ta san bata shan tea. D'aukowa ta yi bayan ta fito dining ta zauna tana ci. Tana cikin ci ne Khalid ya fito sanye yake cikin suites bak'i da fari, ya sha kyau sosai kamar ba shi ba.
Plate d'in indomie d'in ya d'auke ya ce "Kanki kika sani ko?"
"Kai da indomie bata dameka ba? Ni dai ka bani ka shiga ka ha'do tea dan Allah."
"An k'i a baki d'in, sai dai ki had'o min ko kuma na hanaki kema."
Ba dan ta so ba ta tashi ta had'o masa tea d'in, bayan ta bashi ne shima ya bata nata abincin suka zauna.
Misalin k'arfe tara suka gama, daidai nan kuma Momy ta fito.
Har k'asa Ikram ta gaisheta kamar yanda ta saba sannan ta mik'e ta zauna ta ce "Momy kin ga har mun gama shiri da wuri ko?"
"Ehh na gani fa Ikram, sai ki tashi ku tafi dan bana so lokaci ya k'ure, kin san na kira Principal d'in ta ce a kaiki da wuri, dama alfarma ce na nema, saboda term ya yi tsakiya a k'aida ma ba'a d'aukar students yanzu, da yake k'awata ce ya sa ta yarda, kuma makarantar ta yayanta ce."
"Ok momy, bari mu tafi to, sai mun dawo." Ikram ta fad'a bayan ta mik'e tsaye.
Kud'i Momy ta mik'a mata ta ce "Ungo wannan, ai ba'a tafiya babu kud'i saboda tsaron laruri, duk da dai ba zama zaki yi ba yau zaku dawo."
Karb'a ta yi, dubu d'aya ce ta ma Momy godiya sannan ta saka a jakarta. "Dan Allah Khalid banda gudu dan na san halinka, ka tafi a hankali tafiya sannu sannu kwana nesa, ka mata bayanin duka karatun Ikram da inda ta tsaya."
"Momy da dai kin bari na yi gudu da ita ko zawayi ta yi kad'an." Ya fad'a yana murmushi cikin zaulaya.
"Ni dai na fad'a maka, a kiyaye dan Allah." Ta fad'a.
"To insha Allahu, bari mu tafi sai mun dawo." Suka fice su biyun.
***
Tafiyar kimanin awa biyu ta isar da su Birnin Kebbi, kai tsaye hanyar Expert International Academy suka nufa. Ba wani lungu sosai makarantar ta ke ba, hakan yasa dan da nan suka isa.
Sai da securities suka masu tambayoyi kafin suka barsu su shiga, nan ma Khalid ya siyar da hali, cikin lokaci kad'an mutanen suka saba da shi.
Ofishin Principal suka nufa kai tsaye, bayan ya yi parking suka fito, ciki suka shiga nan ma sai da securities suka masu bincike, saboda makarantar tsadaddar makaranta ce sai 'ya'yan wane da wance kawai ke ciki, daga garuruwa masu nisa iyaye suke kawo yaransu.
Bayan sun shiga sun samu principal zaune tana 'yan rubuce rubuce, kai ta d'ago saboda jin sallama da ta yi. Baki bud'e ta amsa sallamar tare da fad'in "D'ana Khalid yanzun nan kau na ke tunanin zuwanku a raina, saboda Hajia ta fad'a min kun taho amma na jiku shiru. Sannunku ku zauna ga wuri nan."
Zama suka yi kuwa bayan sun gaisheta ta amsa cike da sakin fuska.
"Sannunku ya gida ya Hajiyar ta ke?"
"Lafiyarta k'alau Umma, ta ce mu gaisheki."
"To madalla, Isuhu!" Ta k'walawa wani kira.
Da hanzari ya shigo cikin girmamawa ya ce "Na'am ranki ya dad'e."
"A basu lemu, ka turo min Shazali idan ka kawo lemun."
Wurin fridge ya nufa kuwa sai rawar jiki ya ke. Coke d'aya sai fanta d'aya ya d'auko ya ajiye a gaban su Ikram sannan ya fita waje, babu jimawa sai ga Shazali ya iso yana fad'in "Ga ni ranki ya dad'e."
Makullin mota ta bashi ta ce "a siyo masu ko doya da nama ce, dan Allah a yi sauri, daga Sokoto su ke." Ta bashi kud'i.
Bayan ya tafi ta juyo garesu ta ce "Hajiya ta ce zaka min bayanin yanayin karatun nata ko?"
"Ehh Umma, ta tsaya a SS3 ne, amma Momy ta ce a kaita ko SS2 saboda karatun k'auye ne ta yi kuma kin san yanayin karatun, ba wani mai kyau sosai ba ne, tun da babu kulawa." Khalid ya fad'a cikin natsuwa kamar ba shi ba.
"To babu damuwa, dama ta min transfer na registration fee d'in, dubu d'ari da hamsin, yanzu za'a kawo mata Uniforms da house wears d'inta, sannan kuma na mata bayani ce wa no need of provision here, amma idan an yi ra'ayi za'a iya siya mata, saboda komai ana basu a nan."
"Ok, idan an kawo sai mu tafi, next week insha Allahu za'a kawota."
"To babu damuwa Khalid, ina d'an uwanka likita ya ke?" Ta tambayeshi.
"Ya tafi UK zai yi wani course, amma ba ma dad'ewa zai yi ba, ina jin ba zai wuce shekara d'aya ba." Ya bata amsa.
"To madalla, kai kuma fa a ina ka tsaya a karatunka?"
"Na gama degree ina service ne yanzu haka."
"Abu ya yi kyau, lallai yara sun girma, Feenah ma da tana raye ai kuwa na san da ta isa ta gama Secondary ko?"
"SS3 ne yanzu ta ke a k'aida." Ya fad'a.
"Allah sarki! Allah ya mata rahama ya toni asirin wanda suka zalunceta."
Suna cikin firar ne Shazali ya dawo hannunshi rik'e da ledoji ya ajiye a gaban su Khalid sannan ya fita. Bai kai ga fita ba ta kirashi ya dawo.
"Store za'a je a d'auko Uniforms na mata, a d'auko size 3 ina ga su zasu mata, sai ka d'auko house wears pink na Amrah house, suma size na uniform d'in, ko wane 2 sets za'a kawo."
"To ranki ya dad'e." Ya fad'a had'e da fita.
Bai jima ba ya dawo rik'e da kayan a cikin babbar leda ya basu.
Kad'an suka ci sannan suka mata godiya tare da tafiya cike da so da k'aunar matar, saboda tana da kirki sosai bata da wulak'anci kamar yanda wasu matan su ke idan suka samu d'aukaka.
Sai kusan sallar la'asar sannan suka isa Sokoto, da murna da farin ciki Ikram ta shiga gida, Momy ta samu tana salla hakan yasa itama ta shiga d'aki domin gabatar da tata sallar.
Bayan ta gama ta yi wanka ta sako k'ananan kaya ta fito, zaune ta samu Momy, kallonta ta yi ta mata fara'a sannan ta k'ariso inda ta ke, "Momy har mun dawo, an gama komai sai zuwa kawai, matar tana da kirki ta ce a gaisheki."
"Ai haka Hajia Hinde ta ke, ba dai kirki ba, alfarma kuwa sai dai idan ban nema ba."
"Allah sarki, ga uniforms d'in nan ga kuma house wears, na ji Yaya Khalid ya ce wai nan da next week za'a kaini."
"Zaman me zaki yi har next week? Ai gobe ko jibi za'a kaiki ma, tun da dai an gama komai ai babu abin da za'a tsaya jira."
Shiru Ikram ta yi na d'an lokaci, dan ta san zata yi kewar gida sosai ba kad'an ba, barinma Khalid da kullum suna tare, yana zaulayarta.
"Tashi ki zuba abinci ki ci, na tabbatar akwai yunwa a tattare da ke."
Ikram ta ce "Wallahi momy bana jin yunwa, Umma ta sai mana abinci a can har muka taho mota da sauran."
"To masha Allahu, gobe idan Allah ya kaimu sai mu je a miki siyayya, jibi kuma zan kaiki da kaina."
"Momy ai ta ce fa ba sai an sai komai ba, sai dai wai idan an yi ra'ayi ne kawai." Ikram ta fad'a.
"Ehh na san hakab tsarin makarantar ya ke, amma ni dai na fi so ki tafi da komai naki, in yaso na can din sai ya zama extra."
Murmushi Ikram ta yi sannan ta ce "To sannu da kokari Momy." Ita ma Momy murmushin ta mata.
Daga nan suka ci gaba da fira sosai, Momy na mata nasiha yanda zata zauna makaranta, saboda ta san yanda makarantar ta ke k'unshe da yaran masu kud'i, sannan kuma ta mata nasiha cewa; ta san duk inda mata suka had'u zallarsu akwai yawan lesbian, musamman ma yanda abin ya zama ruwan dare yanzu, 'yan mata basu d'aukeshi komai ba face fashion, an miyar cewa sai wayayyiya ke yinshi, wacce bata yi kuwa bata waye ba.
Ikram ta d'auki nasihun momy sosai, ta mata alk'awarin insha Allahu zata kare mutuncinta.
Washe gari suka tafi Ruky Store momy ta mata siyayya sosai kamar ba 'yar makaranta ba. Akwati ma kanshi seti guda ta siya mata na trolley kamar kayan lefe, b'angaren provisions kuwa ba'a cewa komai sai godiya.
Da yamma lilis suka koma gida, kayakin suka hau shiryawa har sai da aka had'a komai sannan ta hau shirye shirye. Washe gari wurin k'arfe goma na safe suka kama hanyar Birnin Kebbi, Khalid ke tuk'a motar sai Ikram zaune gaba, Momy kuma baya ta zauna.
Suna tafiya suna d'an tattaba fira, Khalid sai zuba ya ke yana fad'in "Ai gwara ma ki tafi, dama banda damuna babu abin da kike yi, kin hanani sak'at kullum da inda kike fad'in na kaiki kamar wani driver d'inki. Allah yarinya ki shirya dan da kin dawo hutu mota zan koya miki ko nima ma huta."
"Kai dai Yaya na san zaka yi kewata sosai, momy ki min video d'inshi yana kukan missing d'ina."
"Allah ya kyauta min yarinya, ai yau zan sha kallo, auta zata rabu da momy abin zai yi dad'in kallo."
Dariya suka sa su duka motar. Fira su ke sosai cike da farin ciki da k'aunar juna.
K'arfe sha biyu da rabi ta kaisu Birnin Kebbi, sai da suka biya ta Karamchi super market momy ta k'ara yi wa Ikram siyayyar abin da ta manta bata siya mata ba, irin su chocolates, biscuites da sauransu. Ana kiran azahar suka shiga makarantar.
Office d'in principal suka nufa bayan an gama bibbincike kayansu, sun tayar ta tashi daga aiki saboda bata san da zuwansu ba, momy ta ce ba zata fad'a mata ba sai dai kawai ta gansu. Mai gadin office d'inta ne ya kaisu har staff quarters ya gwada masu gidanta, saboda ya shaida su Ikram su ne suka zo shekaran jiya.
Babban gida ne kamar ba staff q ba, ya sha ado da shuke shuke kala kala, bayan sun shiga gidan nan ma sai da suka tayar da wani mai gadin, shi ya kaisu har cikin gidan a lokacin Hajia Hinde ta gama salla tana cin abinci.
Ganin momy da ta yi ba k'aramin faranta mata rai ya yi ba, rungumar juna suka yi duk da ba wani mugun dad'ewa suka yi rabon su da juna ba, tun rasuwar Feenah ne basu sake had'uwa ba sai dai a waya.
"Sannu Hajia Salma, wannan zuwa haka na bazata." Hajia Hinde ta fad'a cike da murna.
"Wallahi kuwa Hajia Hinde, ai dama cewa na yi zan miki bazata, gashi kuwa na miki d'in." Momy ta fad'a fuskarta k'unshe da murmushi.
"To madalla, an yini lafiya ya hanya?"
"Alhmdulillahi, ya aiki ya fama da yara?" Momy ta tambayeta.
"Ana ta fama kam, an kawo 'yar tawa ne tun yau ko?"
"Wallahi kuwa, ai gani na yi tun da dai an gama komai zaman me zata yi, na ce da kaina ma zan kawota amana hannunki, dan Allah a kula min da ita sosai, duk da dai na san zaki bata kulawar kamar yanda zan iya bata. 'Yata ce, matsayin Feenah haka na d'auketa."
"Aikuwa insha Allahu zan bata kukawa mai kyau, ba zata tab'a kukan rashinki a kusa da ita ba."
Sosai momy ta ji dad'i, sun jima suna fira har kusan k'arfe biyar na yamma sannan suka fara haramar tafiya Sokoto.

VOUS LISEZ
SHI NE SILAH!
Roman d'amourshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.