*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_Wannan shafin naki ne *Haneefa Usman* tanx for the love and care, Ikram da Haidar na gaisheki._
37~ Sakin baki kawai ya yi yana kallon motar, bai k'ara ko taku guda ba sai gabanshi ke fad'uwa.
Ganin motar gadan gadan tana tinkaroshi yasa shi d'an rufe fuskarsa da wuyan rigarshi da ya d'an jawo har bisa fuskar.
Wata kyakkyawar budurwa ce sanye da medical glasses wanda ya masifar amsar fuskarta. Ta sha gayu har ta gaji, pink d'in material ne ta saka mai kwalliyar ash, hakan ya bata damar yin veiling da d'an 'karamin ash gyale.
Sauke gilashin motar ta yi had'e da zare glasses d'in fuskarta. "Sannu mallam." Ta fa'da cikin wata murya mai masifar dad'i.
"Yauwa sannu." Ya bata amsa tare da sakin wuyan rigar da ya rufe fuskar tashi.
"Dan Allah tambaya na ke." Ta sake fad'i a hankali had'e da d'an guntun murmushi, ga wani irin fitinannen k'amshi da ta ke bad'ad'awa.
"To Allah yasa na sani." Khalid ya fad'a bayan ya d'an matso daf da motarta a lokacin ita kuma ta fito.
"Mun yi mahad'a da wata Barr. Ne a area'n nan, ban san ko ka ganta ba, na yi late shi ne na ke tunanin ko ta jirani ban zo ba. Gashi kuma babu network a wurin."
Ajiyar zuciya ya sauke had'e da fad'in "Wallahi ban sani ba dan nima yanzu na zo wurin. Amma a ina ta ce miki zaku had'u?"
"A daidai sign board d'in can ta ce idan na zo na shigo kwanar." Ta bashi amsa.
"To ki jirata wata k'ila bata iso ba ne.." bai rufe baki ba sai ga mota ta doso wurin. Kallo d'aya ya mata ya tabbatar da Barr. Kareema ce. Murmushi ya saki bayan ya ganta.
Kusa dasu ta yi parking sannan ta fito. Da mamaki ta ke kallon Khalid, yanda ta ga ya koma lokaci d'aya kamar ba shi ba.
"Khalid! Kai ne?" Ta tambayeshi.
"K'warai kuwa ni ne Barr. Allah ya kub'utoni bayan an saceni." Ya bata amsa.
"Allah sarki! Aikuwa gida hankali ya tashi. Bincike sosai a ke har gidan tv an kai jajenka, 'yan sanda ma sunata bincike sosai. Amma su waye suka maka haka?"
"Nima kaina ban sani ba Barr. Allah dai kawai ya kub'utar da ni. Dama ke ce wannan baiwar Allah'r ta ke nema?"
Kallon budurwar ta yi ta ce "Ehh ni ce, na taho a hanya motata ta d'an samu matsala, da k'yar na samu ta tashi shisa ban iso da wuri ba. Sannu *Khadijatu."* ta fad'a had'e da kallon kyakkyawar budurwar.
Murmushi ta yi ta ce "Yauwa Barr. Yau dai Allah ya yi zamu ha'du, kullum sai dai magana a waya."
"Wallahi kuwa. Khalid ya za'a yi? Ko zaka jira mu gama magana sai mu tafi tare?" Kareema ta fad'a tana kallonshi.
"Babu damuwa Barr. nima d'in a inda suka kaini na ga motata amma kuma babu makullinta." Ya fad'a.
Cikin mamaki ta ce "Ashe ma ka san inda suka kaika. Tun da haka ne ai kamasu ba zai yi wahala ba. Sai a tura 'yan sanda kawai a gidan."
"Bana son na saka masu gidan a matsala ne. Wasu fulani ne su ke tsaron gidan gonar su suka taimakeni. Inaga kamar idan na d'auki wani mataki tun yanzu ban masu adalci ba. Na san tarkon da zan d'ana masu ta yanda za'a yi sauk'in kamasu. Kin san hausawa sun ce 'idan baka iya kama b'arawo ba shi zai kamaka'."
"Haka ne kam, kaima ka yi magana. Ka shiga motata ga makullin ka jirani, idan mun gama sai mu tafi." Ta mik'a masa makullin motar.
Karb'a ya yi ya bu'de motar ya shiga ya zauna, sosai ya ke mamakin wannan al'amarin, to wai su waye suka masa haka? Me su ke nema a wurinsa? Tambayoyin da ya ke jerowa kansa yana nanatasu ke nan tun sanda ya shiga motar.
Kareema da *Khadijatu* sun d'auki kusan kimanin awa d'aya zuwa da rabi suna magana kafin suka yi bankwana Kareema ta fito daga motar ta koma tata.
Khalid ya tuk'a motar suka kama hanyar Sokoto, sai a lokacin ma ya gane inda suka kawoshi 'din, ashe daf su ke da shiga garin Shagari.
"Mutanen yanzu sam wasu basu da imani. Ka ga wannan yarinyar da muka had'u? 'Yar Kano ce amma a garin nan su ke zama , yau saura kwana biyar aurenta, shi ne ta nemi lambata tun kusan sati d'aya da ya wuce wai tana son magana da ni oeraonaly, kuma bata san kowa ya sani. Na ce ta sameni a gida amma ta nace a kan bata son mu had'u a gida ita dai in taimaka mu keb'ance a bayan gari. To dama ko wani bincike ko tattaunawa zan yi da mutane a wurin mu ke had'uwa, saisa itama na ce mata mu had'u can d'in. Wai in fad'a maka so ta ke idan ta yi aure in zama lauyar mijinta, sun yi yarjejeniya cewa duka dukiyarsa zata koma a k'ark'ashin ikonta. Wai tana so in tsaya mata saboda komai ya saka sunanta, idan ta gama ta masa wayau ya saketa. Dan rashin imani wai zata raba dukiyar kashi biyar ta bani kashi 'daya daga ciki. Na amince zan mata ne dan kar ince a'a ta je wurin wani lauyan, Allah ka'dai ya san kuma abin da zasu aikata. Ka ga idan an yi auren yanzu sai na san hanyar da zan bi dan warware case d'in."
Kai ya jinjina ya ce "Lallai kin yi fasaha sosai Barr. Allah ya taimaka ya bada sa'a."
"Amin Khalid. Maganar nan fa gobe ne za'a fara zama, dan da har na fara tunanin yanda za'a yi, tun da dai itama Ikram 'din ba wani natsuwa ne tattare da ita ba."
Sosai ya ji dad'i ya ce "Allah ke nan, Allah baya gyangyad'i bare bacci. Dukkan abin da ka saka gaskiya a ciki to Allah yana taimakonka. Allah yana tare damu shisa na kub'uta yau d'in nan daga hannun azzalumai."
"Haka ne Khalid. Tun sanda Ikram ta fad'a min b'atarka sam ban samu kwanciyar hankali ba. Tare dani 'yan sanda su ke bincike saboda ni kam na yi mamaki a ce wai kamarka ka b'ata."
"Mamaki na ke sosai Barr. Ban san wanda suka saceni ba, ban san abin da na masu ba, sai dai na ji mutanen gidan sun ambaci sunan Umari, wai shi da wasu suka kaini, kuma abin haushi sai suka ce masu wai ni mahaukaci ne, a lokacin sun kwad'a min bindiga bana a cikin hayyacina."
"Allah dai ya k'ara tsarewa to. Mutanen yanzu kam abin tsoro ne. Kuma gashi na san gobe fita zata maka wahala tun da dai yau ka dawo. Ya za'a yi ke nan?"
"Barr. Ai dolena na fito koma ya zan yi, koda ace babu Ikram ni dole na je kotu insha Allahu, barinma tare zamu zo da izinin Allah."
"To Allah ya yarda. Bari na baki motar daga nan sai na hau a daidaita na isa gida." Khalid ya fad'a yana k'ok'arin yin parking.
Saurin dakatar dashi ta yi ta ce "Ya za'a yi ka sauka a nan? Mu je har gida tare, yanzu dole ka ringa b'oyon kanka, saboda matuk'ar suka je basu sameka ba dole su ci gaba da nemanka."
Titi ya sake hawa tare da d'auke hanyar gidansu, zuciyarsa har yanzu bata daina mamaki ba, a wani b'angaren zuciyar kuma farin ciki ne fal, saboda gobe za'a saurari k'arar mugayen mutane wanda suka yi *silar* mutuwar 'yar uwarsa Feenah.
Horn ya yi bayan ya isa bakin gate d'in gidan nasu, da gudu mai gadi ya iso ya bud'e gate 'din yana d'aga masa hannu cike da farin cikin dawowarshi.
Parking space ya dosa tare da kashe motar, tare suka shiga cikin gida da Barr. Kareema yana gaba tana bin bayanshi.
Basu tarar da kowa a parlor'n ba, hakan ya sa Khalid ya isa har d'akin Momy'nshi ya sameta kwance ta rafka tagumi sai sak'e sak'e ta ke a ranta. Kamar a mafarki ta ganshi, ya yi bak'i ya d'an rame kamar ba shi ba. Saurin tashi zaune ta yi ta k'ara murje idonta dan tabbatar da shi d'in ne dai ko kuwa idonta ne?
Ganin haka yasashi murmusawa ya ce "Ni d'in ne dai Momy. Allah ya kub'utar dani daga hannun azzalumai."
Tsaye ta mik'e ido bud'e ta kasa furta komai, kama hannunta ya yi suka isa parlor dan dama Barr. Kareema zama ta yi a kan kujera.
Gaisheta ta yi cike da mamaki momy ta amsa gaisuwar. "Kina mamakin dawowar Khalid ko momy? To ba abin mamaki ba ne, kin san shi ikon Allah ya wuce mamaki. Haka kuma idan Allah ya yi niyyar kub'utar da mutum to dole sai kub'uta komai zaluncin mutane. Allah ne ya tsara dole sai an saceshi kuma dole sai ya dawo gareku."
Ajiyar zuciya momy ta sauke had'e da rungume Khalid hawaye sai zirara su ke daga idonta, har yanzu kuma bata samu damar fad'in komai ba.
Da 'kyar ta sakeshi a daidai saukowar Ikram daga bene, ganin Khalid ya sata sakin murmushi had'e da k'arisa saukowa da gudu ta nufosu. Har ta yi niyyar itama d'in ta rungumeshi sai ta tuna da ba muharraminta ba ne. Dariya had'e da kuka ta fasa tana fadi'n "Yaa Khalid! Ina ka shiga muna ta nemanka?"
Zama ya yi ya ce "Long story..." sannan ya labarta masu kaf abin da ya faru, da kuma had'uwa da Barr. Kareemah da ya yi bayan ya samu damar gudowa.
Sai a wannan lokacin Momy ta ce "Na gode ma Allah da ya dawo min da d'ana lafiya tun da sauran rayuwata. Wanda suka maka kuma ka barsu da Allah ba sai an da'ukar masu mataki ba, kar d'aukar mataki ya sake jefamu cikin matsala."
Ikram ta ce "Ai kuma momy wata k'ila zasu iya ci gaba da bibiyarshi har su ganoshi su sake tafiya dashi, in har da wata manufa suka saceshi to tabbas burin nasu bai cika ba. Inaga kamar dai a d'auki matakin shi zai fi."
Barr. Kareema ta ce "Ko da za'a d'auka to ba yanzu ba, a d'an dakata na wani lokaci, saboda su kansu zasu tsorata yanzu, tun da sun san ka gudu, sannan kuma sun san za'a iya nemansu, kun ga ke nan ai a k'yalesu har sai sanda suka sakankance an bar maganar sannan mu kuma mu fara namu aikin."
"Haka ne Barr." Momy ta fad'a har yanzu bata daina hawaye ba, ga kuma murmushi tana yi.
Abinci Naanah ta kawo masu amma Kareema ta ce ta 'koshi, Khalid da ya yi missing komai na gidansu kuwa sosai ya ci abincin, tausayi ya ba Ikram yanda ta ga yana ci alamar akwai yunwa sosai a tattare dashi.
Ikram shiga d'akin yayanku ki kirashi, kar ki fad'a masa komai kawai ki ce ina nemanshi, a bashi mamaki." Ta yi murmushi.
Bayan Ikram ta tashi momy ta ce "Tun bayan b'atarka yayanka ya shiga damuwa sosai, ko abincin kirki ya daina ci, wurin aiki ma ya daina zuwa ko an kirashi baya d'auka. Ni da Ikram kuwa ba'a magana, barin Baabah Naanah da ta yi kewar barkwancinka."
Dariya suka yi su duka cike da nishad'i, tabbas yau kam ran momy ya yi farin da ya da'de bai yi ba.***
Kwance ta sameshi ya tasa plate d'in abinci gaba bai ci ba sai tunani kawai da ya ke. So biyu ta yi sallama amma bai ma san tana yi ba, hakan yasa ta zauna a kan kujerar da ke fuskantarshi, d'an tafa hannunta ta yi ya d'an zabura kad'an tare da kallonta, samun kanshi ya yi da kasa d'auke idonshi daga gareta.
Saurin d'auke nata idon ta yi ta ce "Yaa Haidar wai sai yaushe ne zaka cirewa kanka damuwa ka ringa cin abinci? Ka ga yanda ka koma cikin lokaci k'alilan. Ba'a jaa da ikon Allah, duk abin da kaga ya samu bawa to mu'kaddari ne daga Allah. Sannan kuma zai iya canza komai a duk lokacin da ya ga dama. Dan Allah ka yi hak'uri ka zama jarumi, Allah yana tare damu kuma shi kad'ai zai iya magance mana damuwarmu."
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, har ga Allah ya ji da'din kalaman da Ikram ta fad'a masa, sai dai girman kanshi ba zai tab'a barinsa nuna mata ya ji dad'in ba.
"Ka zo momy tana kiranka, and I've a suprise for you, amma yau so 'daya tak sai ka min murmushi ba ma dariya ba." Ta k'irk'iro murmushi duk da ya ke ba wai dan Haidar d'in yana burgeta ba ne, kawai dai bata jin da'din halin da ya ke ciki, ko ba komai shi d'in jinin Momy da Khalid ne, tana son ganinshi a cikin farin ciki.
Mik'ewa ya yi tare da gyara rigarsa, kallonshi ta yi ta ce "Baka min murmushin ba Yaya."
Bai san sanda ya saki guntun murmushi ba, abinka ga wanda bai sababa, ita kanta sai ta ga abin daban, tun da ta ke dashi bai tab'a mata murmushi ba, ko da fara'a ya ke da zarar ya had'a ido da ita ya ke dainawa.
Tafi ta yi ta ce "Yau dai sarkin 'yan marasa dariya ya min murmushi." Ta masa gatsine had'e da ficewa da gudu ta bar d'akin.
Guntun tsakin da ya zame masa jiki ya yi sannan ya bi bayanta.
Momy da Kareema ne zaune a bisa three seater, sai Ikram a one seater ta d'aura d'aya bisa d'aya kamar ba ita ce ta je d'akinshi har ta tsokaneshi fad'a ba.
Zama ya yi a k'asa ya ce "Gani momy."
Saurin b'oye dariyarta ta yi ta ce "Har yanzu dai babu wani labari ko?"
Sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce "Still dai babu momy, ko d'azu mun yi waya da inspector ya shaida min suna dai kan aiki."
Ya juya ga Ikram ya d'aure fuska tam ya ce "Ke kuma ki kiyayeni. Kuma ina suprise d'in? Idan babu kuma zan yi ball da yarinya yanzu."
"One...two...three..action.." Ikram ta fad'a tana dariya.
Fitowa ya yi daga bayan kujerar da ya b'oye fuskarshi d'auke da fara'a ya ce "Am here..."
Mik'ewa Haidar ya yi cike da mamaki yana kallonshi, gwadashi ya ke da yatsa amma ya kasa furta komai.
Rungumar juna suka yi bayan Khalid ya matso wurinshi, sun dad'e a haka kafin ya ce "Saifullah ina ka shiga ka barmu a damuwa?"
Zama yayi nan ya labarta masa komai kamar yanda ya fad'awa su Momy.
Sosai Haidar ke dariya kamar ba shi ba, Ikram kanta abin ya d'aure mata kai, shi dai gashi nan kamar wanda jinnu suka shafa, wata ran fuska d'aure wata ran kuma kamar ba shi ba, tsabar sabon da ya yi da d'aure fuska ya sa ko yayi dariyar ma bata masa kyau.
Barr. Kareema ta numfasa sannan ta ce "Tun sanda muka yi waya da Ikram ta ke bani labarin abin da ya faru, sam hankalina bai kwanta ba yanayin yanda na ji tana kuka sosai, na samu na rarrasheta kuma na mata alk'awarin insha Allahu ba zaka wuce kwana biyu baka dawo ba, duk da ba wani mataki na d'auka ba sai dai addua, kuma ina zuwa wurin 'yan sanda a kai a kai, gashi kuwa kwana biyu da maganar Allah ya yi nashi ikon ka dawo gida."
'Ikram again?' Haidar ya fad'a a zuciyarsa.
Mik'ewa ta yi ta ce "Ni dai bara na wuce momy, Allah ya kyauta gaba."
"Ameen Kareema, mun gode 'kwarai Allah ya saka da alkhairi, Allah kuma ya bar zumunci, a gaishe min da Khairat." Momy ta fad'a da murmushi.
"Khairat ma tana gidanmu, tun da ta je weekend bata dawo ba, umiform 'dinta ma binta na yi dasu." Ta fad'a.
"To madalla, Ikram ki taka mata."
Fita suka yi tare da Ikram har bakin mota sannan ta ce mata "Yanzu ya ke nan? Gobe fa za'a fara zama, k'ila ma kuma shi ne zaman k'arshe, tun da na gama had'a komai."
"Kuma ina tunanin ta yanda momy zata sake barin Yaa Khalid fita yanzu. Amma dai bari zan masa maganar, ko me ke nan zan nemeki a waya."
"To ba damuwa sai na jiki d'in." Ta shige motarta dama Khalid ya bata makullin.***
Kwanaki biyu da suka gabata.*team Ikramhaidar*
*team Ikramkhalid*
VOUS LISEZ
SHI NE SILAH!
Roman d'amourshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.