*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
(2018)_wannan shafin kyauta ce ga baki d'aya 'yan 'kungiyar *NAGARTA WRITERS* akan soyayyar da kuke gwadawa Ikram. Na mallaka maku shi kyauta dan jin dadinku. Team Ikramhaidar da team Ikramkhalid duk na gaisheku, #anatare._
29~ Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce "Kin ga dai yanda jarabawarki ta yi kyau sosai. Ina fatan zaki miyar da hankalinki ki yi karatu. Kamar yanda kika k'udura a ranki cewa likita kike son zama, ina bayanki kuma insha Allahi nasara tana tare da ke. Sai dai fatan alkhairi, Allah ya taimaka ya baki sa'ar abin da kika dosa."
Sunkuyar da kanta ta yi k'asa tana saurarenshi, bata tab'a sanin cewa haka Khalid ya ke ba, ashe shi d'in ma dai mai hankali ne?
Khalid ya ci gaba da fad'in "Bana son rashin jituwarki da Yaya ya jawo sauyin ra'ayinki. Likita kike da burin zama kuma kar wani abu ya shige gabanki."
Sai a lokacin Ikram ta d'ago kanta ta kalleshi. Wani irin yanayi ta shiga ko da ta ha'da ido dashi. Ta rasa abin da ya ke damunta, tun kusan sati d'aya da ya wuce ta ke jin canjin yanayi game da yayan nata. Sai dai me? Ta kasa gasgata hakan, ita a ganinta kawai sha'kuwa ce da ke tsakaninsu.
"Insha Allahu yaya ba zan tab'a baka kunya ba. Karatu kuwa zan yishi fiye da tsammaninka. Tun Ummana tana raye babban burinta shi ne ta ga na zama likita, sai dai kuma ban tab'a bata k'warin guiwa a kan hakan ba, saboda yanayin halin da na taso a cikinshi, abincin da zamu ci ma wahala ya ke mana." Ta yi saurin goge hawayen da ya fito mata. Ta ci gaba da "Ummana ta k'aunaceni a rayuwarta, ta kyautata min, ta k'untatawa kanta dan ganin ta faranta min. Hakan ya sa na ke fatan cika mata wannan burin nata na zama cikakkiyar likita." Wani hawayen ya sake gangarowa.
Khalid bai kuma fad'in komai ba tsabar tausayi da soyayyar Ikram da ya ji suna bunk'asuwa a cikin birnin zuciyarsa.
"Oga ga abincin." Waitress d'in ta fad'a tare da ajiye mishi nashi, sannan ta ajiye na Ikram dan dama a tray ta d'orasu duka.
Yanayin da Ikram ta ke ciki yasa har abincin ma ta ji ta 'koshi, sai dai kuma ta san koda ta ce ba zata ci ba Khalid sai ya tirsasata ta ci, idan kuma bai tirsasata ba to tabbas ba zai ji dad'i ba.
Jiki a mace ta fara cin chips d'in tana yi tana 'dan satar kallon Khalid. Shi d'in ma kuma a nashi b'angaren hakan ne.
Har ga Allah maganar da ya so ya yiwa Ikram ba ita bace ya mata, ya so ya fad'a mata sak'on zuciyarsa sai dai ko da ya had'a ido da ita ya ji sam ba zai iya ba, gani ya ke kamar Ikram zata tsaneshi ta wannan dalilin. Shisa kawai ya juya maganar ta wata hanya.
Kad'an ta ci ta ce ta k'oshi, shima kuma hakan ne, yanda yayi tsamman zai ci abincin sam ba haka ba ne, saboda baki d'aya kalaman Ikram sun kashe masa jiki, tausayinta ya ke ji sosai.
A tare suka ce "Alhamdulillah!"
Ikram ta yi saurin kawar da damuwarta ta ce "Ba dai kana nufin har ka k'oshi ba Yaya."
Shi kuma ya ce "Ba dai kina nufin har kin k'oshi ba Ikram."
Murmushi suka sakarma junansu sannan Khalid ya biya kud'in suka kama hanyar tafiya.
A hanya babu wanda ya cewa kowa uffan, sai dai kowa da kalar tunanin da ke cikin birnin zuciyarsa.
Ana kiran azahar suka isa gida, koda ta shiga momy na zaune a k'asa sai Goggoji zaune a kan kujera tana ta ruwan masifa.
Kallo Ikram ta bita da shi, tsohuwa ce 'yar kimanin shekara tamanin a duniya amma sai tsabar masifa ta aje. A ranta ta ce 'Ina jin wannan ita ce Goggoji.'
Sallama ta yi ta shige kai tsaye cikin parlor'n.
"Sannu Momy." Ikram ta fad'a tana kallon momy.
"Barka da zuwa Hajia." Ta cewa Goggoji tare da d'an risinawa alamar girmamawa.
Goggoji bata ce mata komai ba sai wani mugun kallo data bita da shi.
"Wannan d'in kuma a ina aka sameta?" Ta fa'da har yanzu bata daina kallon Ikram ba.
"Ita ce Ikram wacce na fad'a miki ina rik'onta, marainiya ce ita d'in." Ta bata amsa cike da tsoro.
"Duk a cikin dukiyar da d'ana ya mutu ya bari? To wallahi ban amince ba, ya zama dole ta tarkata kayanta yau 'din nan ta bar gidan tun kafin na gayyato su Sameera su kwashe mata su fitar da ita."
"Babu wanda ya isa ya fitar da Ikram daga gidan nan sai ko sanda ta tashi yin aure. Duk kuwa wanda ya nemi takura mata to tabbas zamu saka k'afar wando d'aya da shi, kuma hakan ba zai yi dad'i ba." Khalid ne ya yi wannan maganar a daidai lokacin da ya ke shigowa cikin gidan fuskarshi babu ko d'ison annuri a cikinta.
Kallon mamaki Goggoji ta bishi da shi. "Lallai Khalid wuyanka ya isa yanka. Yanzu saboda wata can bare kake fad'a min wannan maganganun?"
"Ke d'in ce ai na ga sai da haka. Kuma fad'a miki maganganu son raina yanzu na fara, tun da dai har baki iya d'aukar hukunci ma su Abbas ba to nima babu abin da zaki iya yi min..."
"Ya isa haka Saifullah!" Momy ta fa'da tare da mi'kewa tsaye da tsawa.
Shiru ya yi yana ka'da kanshi, la'b'banshi ya d'an tauna kafin ya yi k'wafa ya bar d'akin cike da takaicin tsayar da shi 'din da momy ta yi.
"Ikram je ki sama." Momy ta fad'a tare da nuna mata hanyar up stairs da hannu.
Babu musu kuwa ta haye, sai dai zuciyarta fal ta ke da bak'in ciki da takaicin halin da ta tsinci kanta.
Tun kafin ta k'arisa hawa benen ta ji Goggoji na fad'in "Yanda kike marar asali shi ne zaki kawo mana marar asali a cikin zuri'a, to sam ban laminta ba. Kuma ki umurceta da ta bar gidan nan daga yau zuwa gobe."
Momy bata fa'di komai ba sai dai ta nemi wuri ta zauna, dan a yanda ta ke jinta sam k'afarta ba zata iya d'aukar gangar jikinta ba.
"Kuma maganar ku'di ke na ke saurare. Na baki kwanaki uku tal! Ina son jin labarin hak'k'ina tun da ba gadona gareki ba." Ta mik'e tsaye tare da ficewa daga d'akin.
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.