*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
(NWA)
20189~ Washe gari na tashi da wani irin zazzab'i sosai wanda tun da nake ban tab'a yin ko mai kama da shi ba.
Ko da na mik'e tsaye kuwa jiri ne ya kwasheni ina shirin fad'uwa da sauri na koma na zauna.
Goggo ce ta shigo ta ce "Umma taso ki wanke kwanonin cin abincin, na lek'o tun d'azu na tayar kina bacci har na gyara wake da shinkafa na d'aura."
Yunk'urin tashi na yi amma wani jirin ya kuma kwasata "Goggo na kasa tashi jiri sai d'ibata ya ke."
"Aikuwa a haka zaki daure ki mik'e, dole kuma ki zanzare ki yi aiki saboda cikin da ya ke jikinki dama dole ki ringa jin irin wannan abubuwan."
Kai kawai na gyad'a, ita wato bama ta d'auki cikin wani abu ba tun da har ta ke yin wannan maganar. Da k'yar da jib'in goshi na samu na mik'e, fita na yi na samu har mutane masu siyan abinci sun fara zuwa, ciki kuwa har da Halle.
Sosai na ji dad'in ganin Halle da na yi, ban nufi yin wanke wanken ba sai wurin Halle da na isa ina binshi da wata irin muguwar harara. Bayan na k'arisa inda ya ke na ce masa "ina da magana da kai."
Murmushi ya yi ya mik'e tsaye ya ce "ina kike so mu yi maganar ne gimbiya? Ko gidana ki ke so muje?"
Ban ko bashi amsa ba na nufi k'ofar gida shima kuwa ya bini a baya.
Daga bayan gida muka je dan bana so ina tsayuwa da shi ta hanyar da mutane ke gittawa, ko ba komai ganina dashi zai zubar min da mutunci.
"Ke na ke sauraro gimbiya, ki fad'i matsalarki ko ma wace iri ce zan magance miki ita, ke babbar yarinya ce wacce samun mace mai d'and'anonta sai an shirya, na yi mu'amala da mata kala da kala, amma ban tab'a..."
"Ya isa haka Halle! Ba wannan ne ke tafe da ni ba. Ina son shaida maka ne ina d'auke da juna biyu kuma naka ne. Saboda haka ka shiryawa tonon asiri, wata k'ila ko wannan ya zama k'arshen zaluncinka ga mata."
Dariya Halle ya k'yalk'yale da ita har da tafa hannu, ya dafe cikinshi da k'yar ya tsaya da dariyar ya ce "yo sai me? Ko an fad'a miki cewa ke ce ta farko? Sannan kuma idan kin tona min asiri ai kanki kika tonawa. Dan haka sai ki san na yi, idan zaki tonawa kanki asiri to."
Shiru na yi saboda tabbas gaskiya Halle ya fada, saboda sunan namiji baya b'aci sai dai na mace, in har na tonawa Halle asiri kuwa kaina na tonawa, ko ba komai dama shi sana'arsa ce, ba zai ji komai ba.
"Ke na ke sauraro Umma, zaki tonawa kanki asiri ne ko kuwa muje na miki yanda na ke wa wanda na ma ciki. Idan zaki amince kai tsaye mu tafi birni cikin rufin asiri a zubar da cikin nan, idan kuma ba kya so sai k barshi ki sha kunya." Ya k'arisa maganar da dariya.
"Allah ya kyauta min na zubar da wannan cikin. Yanzu kai ka fi son ka ji kunyar lahira a kan ta duniya? Idan haka ne to ni ba haka na ke ba, gwara na ji ta duniya. Ka tafi na barka da Allah, shi zai saka min, ciki kuma insha Allahu zan haifa abin da ke ciki, zan kuma bashi labarinka macuci azzalumi." Na fasa kuka tare da barin wurin na nufi gida.
Ko da na shiga Goggo na samu tana nemana, ganin ina kuka ga Halle biye da ni yasata fahimtar abin da ya fitar da ni. "Ki tafi ki min wanke wanke har abinci ya kusa nuna." Ta fada.
Wurin kayan wanke wanken na je na wankesu tas sannan na dauko kwandon na ajiye inda ake sauke tukunyar abinci.
Bayan sati d'aya Mallam ya dawo, shi kanshi ya fahimci sauyin da na samu lokaci guda. "Rumana kin canza sosai kin k'ara kyau abinki. Lallai Indo ta iya kiwo da yawa, ga wata k'iba da kika k'ara, kin k'ara haske kamar sabuwar amarya."
Na bud'e baki zan yi magana ke nan Goggo ta d'aure fuskarta ta ce "ai dole ne ka ga wannan sauyin daga Umma, saboda babban abin kunyar da ta d'auko mana."
"Abin kunya? Me kike nufi da abin kunya Indo?" Ya fad'a had'e da zaro ido.
"Umma dai ciki ne da ita, ba kuma ina nufin ciki na cin abinci ba, ciki na haihuwa na ke nufi."
Hannu Mallam ya d'aga yana gwadani "Rumanar tawa kike nufi? Kai ba dai ita ba, da sakel, wallahi akwai lauje cikin nad'i, 'yata ba zata taba yin ciki ba tare da aure ba. K'azafi ne wannan, tashi mu tafi na kaiki asibiti a aunaki 'yata, a tabbatar mata da ba ciki kike dashi ba."
Wani irin kuka na fasa da k'arfi ina gyad'a kaina, "ba k'arya Goggo ta ke maka ba Mallam, tabbas ina d'auke da juna biyu, kuma na shege maras uba! Ko jiya na je asibiti kuma an tabbatar min da hakan. Ka yafe min Mallam, wallahi sharrin shaid'an ne, k'addara ce wacce ta riga fata..."
*"K'addara ko ra'ayi?* (novel by Amrah and Rerbeeart) babu ruwan k'addara kar ki ci amanarta. Rumana duk irin abin da na ke miki? Duk irin gatan da ni da mahaifiyarki muke miki amma ki rasa abin da zaki saka mana dashi sai sakamu mu ji kunya? Tir da sabuwar d'abi'ar da kika d'aukarwa kanki, kin cuci kanki kin siyar da martabarki, ki fad'a min ma waye ya miki cikin kuma miye dalilinki na yinshi?"
Shiru na yi sai kuka da na ke ta faman sharawa, shi kuwa ya mik'e tsaye ya ci gaba da tambayata "waye ya miki ciki Rumana? Ki fad'a min waye ya miki ciki?" Nan ma shiru na masa hakan yasa ya shara min wani irin zazzafan mari wanda har sai da na ga giccin wuta a idanuwana.
Tun da na ke a rayuwata ban tab'a ganin b'acin ran Mallam kamar wannan ba, baki d'aya fuskarsa ta canza, abinka ga jar fata, duk sai ya zama kamar ba shi ba.
Kuka na k'ara fasawa bayan ya mareni, na duba har k'asa tare da rik'e masa k'afa ina fadin "nasan na ja maka abin kunya kuma abin fadi ga mutane, dan Allah ka yafe min, na yi dana sanin hakan, ka ji k'aina ya mahaifina." Kuka sosai na ke.
Da karfi ya fizge kafarsa tare da barin wurin ya nufi d'akinsa.
Kallon Goggo Indo na yi da ko a jikinta abin da ya ke faruwa, murmushin takaici na yi sannan na ce "Allah dai ya san gaskiya kuma yana tare da mai gaskiya." Na tashi na nufi dakina na ci gaba da kuka.
Sai da muka yi kwana uku a haka ni da Mallam, ko na gaisheshi baya amsawa kuma hakan bai sa ni fasawa ba. Sai da na bari Goggo bata gidan sannan na shiga d'akinsa, zaune ya ke ya hada kai da guiwa sai zancen zuci ya ke, kusa da shi na zauna na fara magana "Mallam dan Allah ka yi hakuri ka saurareni." Bai tanka min ba haka kuma bai koreni ba, hakan ne ya bani damar ci gaba da magana "so da yawa wasu matan su kan yi ciki ne a bisa wasu dalilai, wasu su kan yi ne a kan rashin kula ki sakacin iyaye, wasu su na yi ne a kan kwadayin abin duniya, kowa dai da nasu dalilin. Kyamarsu da iyayensu ke yi akan sun yi ciki kuwa da dama shi ke kai wasu ga barin gidajensu tare da fadawa harkar karuwanci. Mafi yawancin iyaye basu dauki korar yaransu a bakin komai ba, ba za'a iya yiwa yaro uzuri a saurari daga gareshi ba. Dan Allah Mallam kar ka zama daya daga cikin wannan iyayen, matuk'ar kana fushi da ni ba zan iya ci gaba da zama a gidan nan ba, gida dai gidanka ne ba nawa ba, to taya zan zauna a ciki bayan kuma mai shi babu ruwanshi da ni? Ka min uzuri mahaifina, hakika nasan na yi laifi kuma gani a durkushe ina mai neman yafiyarka. Hakika ko Allah mahaliccinmu muna masa laifi kuma mu rokeshi ya yafe mana, dan Allah ina so kaima ka zama mai yafiya ba gareni kawai ba ga kowa ma. Na yi cikin shege Mallam amma ba da son kaina ba, bana so kuma ka tirsasani akan sai ka ji dalilin yinshi da kuma wanda ya min, saboda alkawarin da na dauka kuma nasan ka san darajar alkawari. Na rokeka dan Allah Mallam ka yafe min, kuma dan Allah kar ka kuma tayar da wannan maganar har abada! Abin da na haifa kuma ina mai neman alfarmar kar ka k'yamaceshi, ko ba komai jininka ne. Saboda akwai da dama mutanen da suke k'yamar d'an shege alhali kuma shi babu ruwanshi, ba shi yayi abin ba, dan Allah Mallam ka min wannan alfarmar." Na duk'ar da kaina ina kuka sosai mai ratsa zuciya.
Shima kukan ya ke har da fasawa ya yi "tashi tashi 'yata 'yar albarka. Na yafe miki har cikin zuciyata, kuma na miki al'kawari ba zan kuma tayar da wannan maganar ba, abin da zaki haifa kuwa zan bashi kulawa tamkar d'a ne na halak. Amma ke ma ki min alkawarin hakan ba zata sake faruwa ba."
Kamar ina jiransa na ce "na maka wannan alkawarin Mallam, insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba."
"To Alhdulillahi, mutanen unguwa kuwa suje can suyi surutansu, ki dod'e kunnuwanki dan nasan dole sai sun yi, amma sai suyi ai, tunda dai ni mahaifinki na yafe miki ai shike nan, mahaifiyarki kuwa dama jiya na yi magana da ita ta ce ta yafe miki. Kar ki ji komai ki ci gaba da rayuwarki ba tare da ko d'ison damuwa ba."
Dad'i na ji sosai sannan na tashi na nufi d'akina, zuciyata sayau na ke jinta kamar babu damuwar komai a cikinta...
@wattoad: PrincessAmrah

YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.