43

1K 54 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

43~  Sai da ta fara shiga d'akin Khalid domin ta dubashi da jiki. Yana zaune yana kallon news ta shigo, murmushi ya mata had'e da bata izinin zama. "Sannu Yaya, ya k'arfin jikin?"
   "Jiki alhamdulillahi Ikram. Ya School d'in? Yau na ga kin dad'e baki dawo ba." Khalid ya fa'da tare da miyar da baki d'ayan hankalinshi gare ta.
     "Wallahi kuwa, na biya ta asibiti ne na duba marar lafiya." Ta bashi amsa had'e da mik:ewa. "Bara na shiga ciki, da yunwa na iso sosai."
    "Ok to, nima bara na tashi sai mu tafi tare." shima 'din ya mi'ke ya bi bayanta.
    Ganin Momy zaune yasa suka zauna suma 'din a parlor, sannu da zuwa momy ta mata sannan ta ma Khalid ya jiki. "Bara na 'dan watsa ruwa momy." Ta fad'a cikin sigar gajiya sosai.
    "To ki yi sauri ki dawo ki ci abinci." Momy ta fad'a.
    Hayewa sama ta yi ta watsa ruwa sannan ta saka k'ananan kaya ta yi wanka ta fito. Zaune su ke suna fira itama ta jone masu.
    "Momy abin tausayi, wani bawan Allah ne babu lafiya d'azu da na ragewa yaa Haidar hanya motarshi ta lalace ake ta kiranshi, mutumin bai da lafiya sosai wallahi. Amma yanzu dana dawo daga makatanta na biya wai ya samu sauk'i. Na ce masa ma zamu je da ke ki dubashi."
     Cike da tausayi momy ta ce "Allah sarki! Aikuwa anjima ko zuwa dare ko yamma sai mu shirya na gano shi. Kin san ziyarar marasa lafiya abu ne mai matuk'ar muhimmanci da lada."
    "Haka ne momy. Allah ya bamu ladar, bara na zubo mana abinci." Ikram ta fad'a.
    "Ki zubo mana tare mu duka, nima ban ci ba dan bana jin yunwa lokacin da aka gama."
    Kitchen ta nufa kuwa a tray ta sako masu faten dankalin turawa mai kifi. A 'kasa ta aje shi nan suka ci su duka har da Yaa Khalid d'in da rabonshi da abincin kirki tun kafin momy ta sanar dashi matar data tsaidawa Haidar.
    Bayan sun gama ta kwashe kayan sannan ta feshe wurin da tangerine freshner, take kuwa duk 'karnin wurin ya sire.
     Bayan ta huta sosai momy ta ce "Maganar da na ce miki zamu yi Ikram.."
   Take gaban Khalid ya fad'i, saboda ya tabbatar da maganar da momy zata ma Ikram bata wuce had'ata aure da Haidar ba.
    Jin zuciyarsa na neman jagulewa yasa shi saurin mik'ewa ya ce "Da alama sirri ne zaku yi tsakanin uwa da 'ya bara na koma d'akina." Ya k'irk'iro murmushi.
    "Dawo zauna. Ai har da kai za'a yi maganar." Momy ta fad'a had'e da jawo masa hannu.
    Babu yanda ya iya dole ya koma ya zauna 'din, duk da yanda ransa ya ke matuk'ar 'baci a kan maganar da momy zata ma Ikram.
    "Ikram na san ke mai hak'uri ce kuma mai d'aukar k'addara. Sannan kamar yanda muka fara magana kwanaki, cewa duk irin mijin dana zab'o miki ki aura zaki aura? Kika kuma shaida min da cewa ba zaki tab'a iya sab'awa umurnina ba. To ba ma umurnin ba ne wannan shawara ce, idan ta miki to, idan kuma bata miki ba feel free ki fad'i ra'ayinki, dan bana son na shiga hak'k'inki."
    Ajiyar zuciya Ikram ta sauke had'e da fa'din "Wallahi momy ko kare zaki d'aura min a matsayin mijina ba zan tab'a sab'a miki ba, zan rik'e shi a matsayin mijina kuma abin alfaharina. Barinma na san ba zaki tab'a zab'ar min wanda kika san zan cutu ba. Na d'auke ki tamkar uwar data haife ni, yanda ummana zata bani umurni na bi haka zalika kema 'din zaki bani na bi koda ace bana so. Dan Allah ki daina fad'in sharawa ce, ina son ki ce umurni ne kuma dole na bishi."
    Murmushin dattako Momy ta yi tare da dafa kan Ikram ta ce "Allah ya miki albarka 'yata. Kasantuwar Khalid ya tsayar da matar aure, kuma na ga rashin dacewa a ce shi yayi aure kuma yayanshi zaune sai tsofewa ya ke bai yi ba, yasa na yanke hikuncin had'aki aure da yayan naku in dai babu damuwa.."
    Bata ko rufe bakinta ba Ikram ta mik'e tsaye, ta kasa furta komai sai ruwan hawaye da ke zirara daga idonta wanda bata san sanda suka fara fita ba. Karkad'a kai kawai ta ke tana tuno abubuwa da yawa wanda suka gabata.
    Momy ma mik'ewar ta yi ta dafa kafad'arta ta ce "Ba zan tab'a tilastaki ba a kan abin da bakya so. Wallahi Ikram idan kika ce ba zaki auri yaron nan ba ba zan ta'ba ganin laifinki ba. Saboda soyayya ba'a mata dole. Rayuwar aure rayuwa ce ta har abada. Ki fa'da min ra'ayinki a kan hakan."
    Duk da bata son abin amma sai ta samu kanta da kasa musawa momy. Momy ta mata abin da har ta bar duniya ba zata tab'a mantawa da ita ba, bata jin zata iya sabawa ra'ayin momy, ko ba komai Haidar jinin momy ne, kuma idan har ta nuna k'inshi sai momy ta ji babu da'di duk da ta san ba zata tab'a nuna mata rashin jin dad'in ba.
    Cikin kuka ta ke fad'in "Ba wai zan 'kishi ba ne momy. Ina tunanin kamar Yaa Haidar ba zai soni ba, ba zai tab'a kyautata min a matsayina na matarshi ba."
     Kamata momy ta yi ta zaunar a bisa kujera sannan ta ce "Sa idonki cikin nawa Ikram. Ai ba shi ya haifi kansa ba, dole ne ya bi umurnina ko yana so ko baya so. Kuma ya zama mashi dole ya kyautata miki in har yana son farin cikina. In dan wannan ne ina son ki cire damuwa a ranki, ki d'auka kamar wanda kike so ya ke sonki ne zaki aura. Ni kuwa na miki al'kawarin ba zaki yi dana sani ba. Ki share hawayenki kin ji?"
     Kai kawai ta gyad'a zuciyarta sai tafarfasa ta ke mata, ta ma rasa abin da zata yi, ita dai a zahirin gaskiya ta san babu mutum wanda ta fi tsana a rayuwarta sama da Haidar, ta tsane shi bata k'aunarshi. Taya ma zata yi rayuwar aure da wanda *SHI NE SILA* har mahaifiyarta ta bar duniya? Ta ya zata zauna inuwa d'aya da mutumin da *SHI NE SILA* da farin cikinta ya kau?
       A sab'ule ta ce "Bara na shiga ciki momy." Ta mik'e da sauri tare da hawa sama.
     Da gudu ta k'arisa cikin d'akin, kuka ta saki da 'karfi had'e da hayewa kan gado da k'arfi ta dafe zuciyarta.
    "Ya za'ayi na auri Yaa Haidar?  Ya zan yi na auri mutumin da ya zama *silar* rugujewar farin cikina? Ya Allah idan mafarki na ke ka sa na tashi da gaggawa, Allah ka tasheni daga wannan mummunan mafarkin." Ta sake fasa wani kukan.
    "Bani da yanda zan yi da ya wuce na bi umurnin momy, ba zan tab'a musa mata ba, dole na auri Haidar ko bana so." Kuka ta ke sosai tana 'kara tuno baya, yanda ta ringa yiwa Haidar magiya ya taimaka ya yiwa Ummanta aiki a ranar amma ya nace dole sai washe gari wanda hakan ne ya zama *silar* mutuwarta, tana k'ara tuno sanda ya ke sanar da ita ummanta ta rasu saboda appendix har ya riga ya gama gurb'ata kayan cikinta. "A hakan zan aure shi? Ta ya zan iya manta abubuwan da ya min?"
     Wayarta ta d'auka da nufin ta kira miemie ta sanar da ita, tunawar da ta yi da yanda miemie ke masifar k'aunar Haidar yasa ta fasa kiranta, ya zame mata dole ta tinkari wata da wannan maganar ko zata samu sassauci, saboda matu'kar ta bar maganar a ranta abin zai ringa damunta ne, wanda hakan ka iya zama *silar* kamuwar wata cutar.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now