*SHI NE SILA!*
😪😪😪Na Princess Amrah
(NWA)
2018_na gaisheku masoyana na nesa da na kusa, wanda na sani da wanda ban sani, ina matukar jin dadin yanda ku ke bibiyar wannan labarin, musamman Maman Saleem, Allah ya raya mana Saleem dinmu ameen. Wannan shafin sadaukarwa ce gareki, Allah ya bar zumunci da zaman tare._
*****
10~ Lokaci na tafiya, kwanaki na shud'ewa, abu kamar wasa cikina ya girma sosai haihuwa ko yau ko gobe, sosai cikina ya yi girma, saboda tun yana da wata hud'u ya bayyana kowa ya gane ina d'auke dashi. Surutai kuwa na shasu babu adadi, da zarar na fita sai zund'ena a ke ana gwadani da yatsa. Haka zalika mahaifina ma, Goggo kuwa da ba kanwar lasa ba ce bata k'yale kowa, duk wanda ya nemi raina mata wayo wankeshi ta ke tas.
Yau ta kama ranar alhamis ne, ranar Mallam ya dawo da kwanaki biyu. Tun da na tashi na ke jin wani irin ciwo wanda ko a mafarki ban tab'a jin irinshi ba, ciwon ciki sosai had'e da mara kamar zasu fashe. Tun abin bai yawaita ba ina daurewa har ya fara cin k'arfina. Hakan ya sa a daddafe na shiga d'akin Goggo, na samu Mallam zaune yana cin abinci. Ko da suka ganni suka fahimci rashin lafiyata, "me ya sameki Ummah?" Goggo ta tambayeni tare da isowa inda na ke. "Goggo marata kamar zata fashe, zan mutu ku taimaka min." Na fad'a da k'yar da wahala.
Mallam cikin tashin hankali ya ce "sako hijabinki mu tafi asibiti, ai ba za'a zauna ba." Ya yi gaba, Goggo ta d'auko min hijabin sannan muka tafi tana rirrik'eni.
Muna fita kuwa muka yi sa'a da wata mota mai kwasar dabbobi daga gidan mai gari ta zo, tsayar da ita Mallam ya yi aikuwa mutumin ya tsaya. Ganin halin da na ke ciki ya sa ya ce "ku shigo da ita, subhanallahi, Allah ya raba lafiya."
Mallam da Goggo suka sakani gaban motar, ni da Goggo muka zauna shi kuwa Mallam ya koma kusa da mai tu'kin kasantuwar iyakar wurin zaman ke nan, tun da dama irin bud'ad'd'iyar nan ce wadda ake d'aukar yashi da ita.
Nan da nan muka isa asibiti, duk wata hidimar ku'di Mallam ya biya, bai damu da kasantuwar cikin shege ba, hankalinshi tashe har aka shiga da ni d'akin haihuwa.
Na jima ina nak'uda har dare ya yi, su kansu masu karb'ar haihuwar sun cire tsammanin zan iya haihuwa da kaina, har sun karb'o takarda zasu kaiwa Mallam ya cike a shiga aiki da ni suka ji ina kiransu, suna zuwa kuwa dama kai ya fara fitowa, suka taimaka min jinjirar ta k'arisa fitowa.
Wannan shi ne asalinnki Ikram, tushenki ke nan. Halle shi ne mahaifinki wanda har yau har gobe babu wanda ya kuma sanin inda ya ke, tun wata rana da ya fara neman matar mai gari, mai gari ya sa aka masa korar kare daga garin, aka kuma ce in har ya sake ko waiwayar k'auyen sai an kasheshi. Tun daga nan bai sake waiwayar garin nan ba, ban kuma sake jin wani labari dangane da shi ba." Ta yi shiru daga nan tana share kwalla. Umman Ikram na rufe bakinta Mallam ya fad'i kasa timmm! Sumamme.
A razane suka yi kanshi, banda Goggo da ta yi k'ememe tana hura hanci wanda ya tabbatar min da borin kunya ne.
Ruwa suka d'ebo suka dinga yayyafa masa amma shiru bai farfad'o ba. Sosai hankalinsu ya tashi, suka rasa ma abin da zasu yi.
Ikram ce cikin kuka ta ce "Umma mu kaishi asibiti dan Allah."
"Ya zamu yi da shi Ikram? Ba mota garemu ba ba kuma mashin ba, ta ya zamu iya d'aukarsa?"
Shiru suka yi banda kuka babu abin da su ke aikatawa.
Ikram ta fara karanto masa suratul yaasiin da k'ira'arta mai matuk'ar dad'i. Sai da ta karance surar tsaf sannan ta dakata ganin Mallam ya fara bud'e idonsa.
"Mallam dan Allah ka tashi, ka tashi muna kaunarka, ba zamu juri rashinka ba."
Da k'yar ya iya bud'e baki ya ce "ku yafe min duk wani abu da na maku wanda na sani da wanda ban sani ba, kun san shi Dan Adam ajizi ne. Bana jin zan ci gaba da rayuwa Rumana, ku yafe min duk ni na ja miki, ban tab'a sanin abin da Indo ta ke miki ba, ban kuma taba tsammanin hakan ba,
da ban aureta ba da duk hakan bata kasance ba."
"Ka daina fad'ar haka Mallam, ni baka mana komai ba kuma idan ma ka mana mun yafe maka, tsakaninmu da kai babu komai face kyautatawa, ina fatan wannan kyautatawar ta zama silar shigarka aljannah."
Kuka sosai Ikram ke yi ta ce "insha Allahu zaka tashi kaima ka ci gaba da rayuwa kamar kowa, cuta ai ba mutuwa ba ce, idan zaka iya tafiya ka tashi mu tafi asibiti a duba abin da ya ke damunka."
"Bana son musa miki ne Ikram, amma ina ji a jikina tawa ta zo karshe." Ya bata amsa.
"Ba zaka mutu ba Mallam, ka tashi mu tafi." Ta fad'a tare da k'ok'arin kamashi ya mike tsaye. Ko komawa ta kan Goggo basu yi ba kawai suka zarce asibiti da shi duk da cewa da kyar su ke yin tafiyar sabida jan kafafuwansa ya ke, kusan nauyinshi baki daya a jikin Umma da Ikram ya ke.
Emergency aka karb'eshi su Ikram kuma suka zauna a bakin d'akin da aka shiga da shi. Ya d'auki tsawon lokaci ana dubashi kafin wata malamar asibiti ta fito ta ce "ku zo wai yana son ganinku, amma ku kula da yanda zaku masa magana saboda jininsa ya hau sosai *shi ne silar* fad'uwarsa ma. Ya matsa ne sai ya yi magana da ku ai da ba zan bari ku shiga ba."
Da sauri kuwa suka shiga d'akin, cikin halin da suka ganshi ba k'aramin razasu ya yi ba, cikin lokaci kadan ya canza kamar ba shi ba, ko da ya d'aga kai ya gansu ya ce "akwai maganar da na manta ban fad'a maku ba ne kuma ina gudun kar na mutu ban fad'eta ba. Ko bayan raina ina so ku nemi danginmu a Misrah, ku masu bayanin komai na tabbatar da ba zasu k'i ku ba, idan ma nawa dangin sun k'i ku to na san dangin Rumana zasu so ku sosai. Ku nema mana yafiya daga wurinsu. Tabbas *mun tafka babban kuskure* (novel by Rash Kardam) da muka gudo muka barosu alhali bamu san irin halin da zasu fada na rashinmu ba, yau gani ni ma zan bi matata Rumana, zan mutu na bar 'yata da jikata, babu abu ma fi muni sama da yaya su gudowa mahaifansu. Indo kuwa ku barta da Allah, na san cewa *ita ce sila* ita ta ja miki komai Rumana, duk abin da zata maku Allah yana gani kuma shi zai maku sakayya, ku sani cewa sai kun yi hakuri da rayuwar da zaku tsinta bayan babu ni, na tabbatar cewa Indo ba zata kyautata maku ba, ko ba komai bata hada komai da ku ba, sannan kuma ni ban taba haihuwa da uta ba barin ace akwai jinina a wurinta, kun ga kuwa baku da sauran wani amfani a wurinta. Idan na mutu ku fada mata cewa 'Allah ya isa cin amanar Rumana da ta yi, bima kuma ba zan taba yafe mata ba akan yardar da na yi da ita ta cuceni, saboda inda ta san ba zata kula da tarbiyyarki ba Rumana ni da na tsayar da duk wani nema da nake domin na zauna tare da ke, amma haka Allah ya nufa, dama can ya tsara cewa ta wannan hanyar zaki haifi Ikram."
Kuka suke sosai har suka kasa fad'in komai, Mallam ya ci gaba da "Ikram ki kula da kanki, sannan ki ci gaba da toshe kunnuwanki daga surutan mutane, na sani cewa wannan tabon zai ci gaba da bibiyarki har d'iyan d'iya. Ki kula da rayuwarki a duk inda zaki tsinci kanki, ina ji a jikina cewa...." bai gama fad'in maganar ba tari ya ci k'arfinsa, sosai ya ke tarin sai ga jini had'e da majina suna fita. Abin ya basu tsoro hakan ya sa Ikram da sauri ta je ta kira malamar asibitin, ko da ta zo har Mallam ya cika. Abin awon numfashi ta ringa danna masa a zuciya ko zata ji bugun zuciyar amma ina, Allahn da ya halicceshi ya bashi aron rayuwar ya karb'i abinsa.
"Sister ya aka yi? Ya samu bacci ne?" Ikram ta tambayeta cikin tashin hankali.
Kai kawai ta gyad'a tare da jawo zanin rufa ta rufeshi ruf har da fuska.
"Baki bamu amsa ba, bacci ya ke me?" Umman Rumana ta kuma tambayarta.
"Ku yi hak'uri, zan maku wata 'yar tambaya kafin na baku wannan amsar."
Shiru suka mata suna kallonta, "yanzu misali a ce wannan abin na hannuna sai na baki aronshi ki yi amfani da shi, idan na zo na karb'i abuna laifi ne?"
Ikram da ya ke yarinya ce bata fahimci komai ba, sai Ummanta ce ta ce "kina nufin Mallam ya rasu ke nan? Allahn da ya fi mu sonshi ya karb'i abinsa?"
Jinjina kai sister d'in ta yi tare da fita ta bar d'akin cike da tausayinsu.
Sake bud'e fuskarshi Ikram ta yi, ta k'are masa kallo, ya k'ara kyau sosai, gashin nan na gemensa ya yi liya liya gwanin sha'awa, hancinsa ya k'ara fitowa d'an siriri, kamar ka kirasa ya amsa.
"Da gaske Mallam ya rasu, dama haka malaminmu ya fad'a mana, idan mutum ya rasu zahirin halittarsa ke fitowa. Shi ke nan mun rasa Mallam, mun rasa gatanmu mun rasa farin cikin rayuwarmu Ummah." Ta fashe da wani sabon kuka. Ita kuwa Umman ta ma kasa yin kukan, sai fad'in "Allahummag firhu war hamhu." Ta ke yi.
Fita suka yi suka nufi gidan domin su sanar a zo a d'auki gawarsa a kaishi gidanshi na gaskiya.
Umman Ikram ce ta nufi gidan mai gari ta sanar da shi, Ikram kuma ta wuce gida jiki sanyaye, tana ta rero kuka mai ban tausayi, dama tun da ta ke a rayuwarta mutum biyu ne ta sani danginta, daa uku har da Goggo, to Goggo kuma ashe bata had'a komai da ita ba. Ummanta da Mallam d'in ne dai, Mallam kuma lokacinsa ya yi.
A haka ta shiga gida bata ko san ta isa ba, Goggo ta iske zaune ita da k'awarta suna fira, Ikram ta dake ta ce "Goggo sai ki zuba ruwa a kasa ki sha, yau Mallam ya rasu kuma *ke ce sila, ke ce silar mutuwarsa Goggo, ke kika yi ajalinsa."* kuka ya ci karfinta.
"Mallam ya rasu? yaushe aka yi? Ke fada min gaskiya Ikram"
"Ta ya zan yi k'aryar mutuwa ga mafi soyuwar mutum a gareni? Me zaisa na ce kakana ya rasu alhali shi kad'ai gareni? Ki daina wani nuna alamar kin damu, saboda Mallam ya mutu da fushinki matuka, kuma ya ce mu shaida miki 'Allah ya isa bai yafe miki ba." Ta bar wurin tare da zuwa ta gyaggyara d'akinsu ita da Ummanta dan a ciki ta ke so a masa wanka.
@wattpad: PrincessAmrah
![](https://img.wattpad.com/cover/145187938-288-k711487.jpg)
YOU ARE READING
SHI NE SILAH!
Romanceshi ne silar rugujewar farin cikin rayuwarta. shine silar shigar ta cikin kunci da bakin ciki. shi ne silar rashin gata hadi da galihu a rayuwarta. shin waye silah? ku biyoni a cikin wannan labarin inda zan warware maku zare da abawa.