26

1K 66 2
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

_Na gaisheki Munay. Tanx for the soyayyar da kike gwadama wannan littafin, Ikram na gaisheki sosai da sosai. Naki ne wannan shafin don farin cikinki. #anatare#_

26~  kallonta Ikram ta yi dan ta fahimci dalilin sakin lemon da miemie ta yi.
   Cikin raini Haidar ya kalleta, gintun tsaki ya saki had'e da hayewa saman bene yana k'walawa Momy kira.
    Wani irin zazzafan hawaye miemie ta saki tare da fad'awa kan jikin Ikram,
   Rungumarta Ikram d'in ta yi tana d'an bubbuga bayanta alamar rarrashi.
     "Wai sai yaushe zaki cirewa kanki wannan soyayyar ne miemie? Wallahi wahalar da kanki kawai ki ke. Ni na san halin Ya Haidar na kuma san ko waye shi. Ya tsani mutane sam baya k'aunarsu. To a kan me ke zaki sakawa kanki k'aunarsa wadda kin san babu abin da zata amfana miki sai wahala?"
     Cikin kuka sosai miemie ta ce "Ni ma kaina ba da son raina hakan ta faru ba Ikram. Ban san ya aka yi na ke fama da dakon son Dr. Haidar ba..." ta k'arisa maganar da kuka sosai. A daidai nan Khalid ya shigo rik'e da Khairat da ta gaji da kuka ta yi shiru.
      "Khairat to ga Aunt d'in mun zo wurinta." Khalid ya fad'a tare da pretending da bai ji maganganun da su Ikram ke yi ba, alhalin kuma ya ji komai.
    "Khairat 'yan mata, zo nan." Ikram ta fad'a bayan ta mik'ar da Miemie zaune tana 'kak'ulo murmushi.
   Ganin haka ya sa Khalid saurin barin wurin ba tare da ya tsaya tambayar abin da miemie ke wa kuka ba.
    Ganin ya fita ya sa Ikram fad'in "Dan Allah ki daina kukan, bana son d'an rainin hankalin nan ya fito ya sameki kina kukan nan dan ya samu damar k'ara raina mutane."
   Shirun kuwa miemie ta yi, amma har cikin zuciyarta bata ji dad'in kalmar da Ikram ta fad'a ga abin k'aunarta ba.
    Da sauri Khairat ta iso inda miemie ta ke hannunta rik'e da ledar da Khalid ya mata siyayya.

****
    Babu annuri ya shiga d'akin momy, ya sameta zaune a bakin gado tana waya, zama ya yi a kan sofa yana jiran ta gama wayar, zuciyarsa sai zafi ta ke masa a kan rasuwar da mutumin ya yi. Abin da ya faru yanzu a parlor kuwa sam bai yi mamaki ba, saboda dama ya saba ganin haka a wurin mata, wasu matan har kuka su ke suna bibiyarshi ya sosu amma sai wulak'anci kawai ke shiga a tsakaninsu.
    Bayan momy ta gama wayar ne ta fuskanceshi ta ce "Akwai matsala ne?"
   Kad'a kai Haidar ya yi ya ce "Wanda na ma aiki bai rasun ba shi ma ya rasu yanzu. Momy na rasa me ke damuna, kusan duk wanda zan ma aiki sai ya rasu. Na rasa me ya ke damuna wanda kuma da ba haka na ke ba momy.." ya fad'a cikin damuwa.
    Shiru momy ta yi kafin ta ce "Ba wani abu ba ne yayansu. Ni ina ganin ai wannan is common, kusan duk wanda za'a kawo ka ma theatre sai ciwo ya ci 'karfinsu sannan ake turosu wurinka, shisa aikin bai cika yin tasiri ba. Ka cirewa kanka damuwar, babu komai insha Allahu."
    Sosai ya gamsu da maganar momy, tashi ya yi tsaye ya ce "Ina Khalid ne? Ko ya fita?"
   "Bai fita ba." Momy ta fad'a tare da mik'ewa tsaye.
    "Zai kai Ikram makaranta ne, daga nan su wuce cafe su bincika ko jarabawarsu ta fito."
   Ko da jin momy ta ambaci Ikram ya k'ara tsuke fuska, har a ranshi baya k'aunar Ikram ya tsaneta.
    Momy bata yi mamakin ganin haka ba, ficewa ta yi ya mara mata baya.
   Ko da suka sauka k'asa har miemie ta wartsake kamar ba ita ce ta gama shar'bar kuka ba.
   Momy na fitowa ta sauka k'asa ta gaisheta, Haidar bai ko kallesu ba ya yi k'ok'arin barin d'akin, a nan suka yi kicib'us da Khalid da ke k'ok'arin shigowa parlor'n.
    "Big bro ashe ka dawo." Ya fad'a tare da bashi hannu suka gaisa.
   "Ehh na dawo. Ina ka shiga ban ganka ba da na shigo?" Ya fad'a babu annuri a fuskarsa.
    "Na je da waccan yarinyar ne na siyo mata chocolates." Ya bashi amsa tare da nuna Khairat da ke ma'kale jikin miemie.
   Bai ko kalli wurin ba ya ce "To ni zan koma."
   "Zaka koma wurin aikin? To ai baka min dariya ba, ko da ya ke idan ka d'aure fuskar ma ka fi yin kyau, Ali gadanga k'usar yak'i."
   Murmushi Haidar ya yi wanda daga Khalid sai momy kad'ai ya ke wa irinsa, ficewa ya yi ba tare da ya kuma fad'in komai ba.
   Wani sanyi miemie ta ji a ranta, sosai ta ji dad'in ganin murmushin Haidar, ita dai duk wulak'ancin a haka ta ke sonshi, kuma ta yarda in dai zai aureta to ko kullum zai ringa d'aureta da igiya ya mata bulala hamsin ba zata damu ba.
    Jin shiru d'akin ya sa momy fad'in "Ya kika baro Kareema?"
   "Lafiya k'alau ta ke momy, ta ce ma na gaisheki, aiki ya mata yawa ne a wurin aiki shisa kika jita shiru bata zo ba." Miemie ta fad'a a hankali kanta du'ke ita a dole tana jin kunyar momy.
      "Allah sarki! Ai aikin nasu dama akwai lokacin da ya ke masu yawa. Allah dai ya taimaka." Momy ta fad'a. "Zo nan Khairat. Ina maminki?"
    Kafad'a Khairat ta mak'e alamun ba zata zo ba.
    "To ke ya za'a yi? Ko tare da miemie'n zamu tafi?" Khalid ya fad'a yana kallon Ikram.
   "Fita zaku yi? A'a ku je sai kun dawo. Ni ina tare da momy dan dama ba wurinki na zo ba wurinta na zo, mara kirki wacce bata zumunci."
    "Ke dai kika sani, tun da dai kin zo wurin momy d'in ai da sauk'i." Ta fad'a tare da mik'ewa ta nufi up stairs.
    Mayafinta ta d'auko sannan ta sauko rik'e da wayarta a hannu.
    "Momy mun tafi." Ta fad'a bayan ta k'ariso inda ta ke.
    "To a dawo lafiya, Allah ya maku albarka." Momy ta fad'a da fara'a k'unshe a fuskarta.
    "K'awata sai na dawo." Ta fad'a tana ma miemie dariya.
    "Sai kin dawo to, ki yo min tsaraba."
    "An 'ki a yo d'in, ni 'yata Khairat kawai zan ma." Ta ma khairat murmushi tare da bin bayan Khalid da ya riga da ya fita yana jiranta.
     Wata jar mota ce suka hau, hanya suka kama basu zarce ko ina ba sai make up school d'in.
   A hanya sai fira su ke Khalid na mata halin nashi na barkwanci, sai dai mafi rinjaye na zuciyarshi tunanin yanda zai yi ya fad'awa Ikram yana sonta ya ke.
    "Wai yaya mesa kake son saka k'ananan kaya?" Ta tambayeshi tare da kallon kayan da ke jikinshi.
    "Haka kawai, ke bakya sonsu ne?" Ya tambayeta hankalinshi na kan tuk'in da ya ke.
    "Bana son ganin namiji da k'ananan kaya Allah, ni idan na yi aure mijina ba zai ringa sakasu ba sai dai idan cikin gida ne kawai, amma duk sanda zai fita to manyan kaya zai saka. Kai ni fa yaya ko saurayi na yi bai isa ya zo min da k'ananan kaya ba."
    "Lallai Ikram an girma. Ke ce da kanki ke maganar aure da saurayi?" Ya tambayeta yana murmushi.
   "Har ka sa na ji kunya Yaya, ai maganan gaskiya ne, tun da na zo ban tab'a ganinka da manyan kaya a haka kawai ba sai ranar friday, friday d'in ma ba ko wace ba, sai ko idan zaka je wurin d'aurin aure."
    Bai ce mata komai ba sai dai a ranshi ya ke fad'in 'aikuwa kin gama ganina da k'ananan kaya tun da dai ba kya so. Farin cikinki shi ne nawa, duk yanda na ke son saka k'ananan kaya na hak'ura da su daga yau, sai idan a cikin gida ne.'
    "Ya dai? Na ga ka yi shiru yaya, ko na b'ata maka rai ne?" Ta fa'da cikin wani yanayi, da wata murya wacce ba ko yaushe ta ke da irinta ba.
    Murmushi Khalid ya yi ya ce "Ehh kin b'ata min rai 'yar rainin hankali, kuma ki nemo soso da sabulu ki wankeshi tas dan bana son ganin datti ko kad'an a ciki."
     Dariya ta k'yalk'yale da ita ta ce "To da wane irin sabulu za'a wanke?"
    "Koma dai da wanne yarinya." A daidai nan suka iso shagon.
    Babban shago ne mai k'unshe da part part ko ina da abin da ake yi.
   Wani wurin salon ne, wani boutique, wani gyare gyaren jiki sai kuma wurin make up da sauransu.
   Kai tsaye reception suka nufa inda wata mata ta ke zaune, ba bahausa ba ce saboda yanayin kayan jikinta.
    Bayan sun gaisa matar ta ce "Mr. Khaled ko wannan ce wacce ka min maganar zaka kawo?"
    Murmushi Khalid ya mata ya ce "ke ni ba Khaled sunana ba." Had'e da d'an zaro ido.
    "Zaka fara halin naka ko?" Ta tambayeshi tana dariya.
    "She's my sister, she want to be a big make up artist as I told you. (Y'ar uwata ce, tana so ta zama babbar mai kwallita kamar yanda na fada miki.)"
    "Ok, since she came here, am assuring you that she will become a big big make up artist, just pay the money (Tun da dai ta zo nan, ina mai tabbatar maka da cewa zata zama babbar mai kwalliya)." Ta fad'a tare da jawo wata 'yar takarda.
    ATM d'in da momy ta bashi nata ya mi'ka wa matar, a POS ta d'aura ta bashi ya saka pin d'in sannan ta saka amount, zarewa ta yi ta mik'a mishi ATM d'in sannan ta zaro wasu takardu guda biyu.
    "What is your name?" Ta fad'a tana kallon Ikram.
    "Ikram Mahmoud." Ikram ta bata amsa.
    Rubutawa ta yi sannan ta tambayeta da wane lokaci ta ke sha'awar ta ringa zuwa? Saboda lokuta guda uku ne a kowace rana, akwai masu morning, masu afternoon sai kuma evening. Morning Ikram ta zab'a.
    "Ok, you are starting by tomorrow (zaki fara daga gobe)" ta fad'a tare da bata wata 'yar takarda.
    Karb'a tayi ta mata godiya sannan suka tafi, cafe suka nufa kai tsaye daga nan.
     Dafifin mutanen da suka gani a cafe d'in ne ya tabbatar masu da cewa jarabawar ta fito, ganin haka ya sa Khalif ya ce "Mu tafi gida kawai, akwai wani abokina da ya ke da cafe amma bayan gari ne da nisa sosai, scratch card kawai zan siya aje a duba miki waec d'inki."
     Mota suka koma Ikram sai jindad'i ta ke, a wata zuciyar kuma tana fargabar sakamakon da zai fito.
    Gida suka koma da gudu Ikram ta shiga bayan ta ja Khalid fad'a tana hakin gudu.
     Bata ankara ba taji ta bugi mutum da 'karfin gaske har sai da suka isa k'asa tare.
    Dubawar da zata yi, wa zata gani?
    Haidar ne kwance shame shame a k'asa yana binta da wani mugun kallo.
    Saurin mik'ewa ta yi tsaye had'e da d'auke kallonta daga gareshi tana waigen Khalid da ya biyota a baya.
    Dariya ta ke son yi amma babu hali sai k'ok'arin guntseta da ta yi.
    Har yanzu Haidar ya kasa mik'ewa sai sa'ke sa'ken yanda zai yi da Ikram ya ke.
    Momy da ke k'ok'arin fitowa ta ga Haidar kwance, Khalid ma ya shigo zai wuce ke nan ya ga Haidar kwance sai huttai ya ke.
     "Big bro me zan gani haka?" Khalid ya tambayeshi cike da mamaki.
     "Me ya faru da kai?" Momy ma ta fad'a bayan ta iso inda ya ke.
     Cikin k'yak'kyafcin ido Ikram ta ce "Momy karo muka yi da shi, shi ne muka fad'i tare, ni na mik'e shi kuma ya kasa mik'ewar."  Dariyar da ta ke b'oyo ce ta fito. Da k'arfi ta fasata har tana dafe ciki.
   Khalid ma dariyar ya yi ya ce "To yaya ka tashi mana, wai dan a ga lafiyarka ko wani abun ya sameka" ya k'arisa maganar da dariya.
    "Ahh to ai ba komai, dama idan babba ya fa'di dariya a ke masa." Ita ma momy ta d'an yi 'yar guntuwar dariya ta dattako.
      Iya 'kuluwa Haidar ya k'ulu, wani irin takaici ne ya lullub'eshi, muguwar tsanar Ikram na k'ara shiga k'ahon zuciyarshi.
    Kamashi Khalid ya yi zai mi'kar amma ya k'wace jikinshi tare da janye hannun Khalid ya mik'e da kanshi.
     "A min hak'uri big bro! Ba ni na kar zomon ba.." ya k'ara fashewa da dariya yana dafe ciki shima.
     Bai iya fa'din komai ba kawai ya bar d'akin, zuciyarsa sai tafarfasa ta ke, shi ya ma rasa wai wane irin hukunci zai d'aukarwa Ikram?
     Su kuwa a parlor dariya kawai su ke banda miemie da ta ha'de rai ita a dole an b'atawa masoyinta rai.
     "Momy...mun je an gama komai..." wata dariyar ta kuma k'wace mata.
    "Wai Ikram miye haka? Ki ma mutum abu kuma ki ringa yi masa dariya? This is unfair.." miemie ta fad'a dan sam ta kasa 'boyewa zuciyarta.
      "Yo ni me na masa? Ya Khalid ne fa ya biyoni, in ma dai laifin ne to ya Khalid ne da laifi ba ni ba." Ta sake yin wata dariyar.
     "Kin b'atawa yayanki rai kuwa sosai tun da kika ga ya k'i yin magana, ki bishi d'akinshi ki bashi hak'uri yanzu ba sai anjima ba." Momy ta fa'da duk da ita ma abin ya bata dariya amma ta yi k'o'karin dannewa.
    "Momy kin fa san halin Ya Haidar, ba kulani ba zai yi ko na je." Ta fad'a had'e da d'an tunzuro baki.
     "Ko dai ba zai kulaki ba ai ke ce da laifi. Ki tashi ki je ki bashi ha'kuri tun kafin na k'ara miki magana."
     Sanin cewa gaskiya momy ta fa'da mata, kuma bata son tana ja da maganar momy ya sata mik'ewa ba dan ranta ya so ba ta ce "To momy bari na je."
     "Miemie ki rakata kuma ki tabbatar da ta bashi ha'kurin."
     Sosai miemie ta ji dad'i, ko ba komai zata sake ganinshin ta ji da'di a ranta.
     Kama hanyar 'dakinshi suka yi, bayan sun shiga suka tayar baya nan.
     Suna k'ok'arin fita ke nan ya fito daga toilet d'aure da towel red na manchester united.
     Ganinsu tsaye suna kallonshi ya sa ya bisu da wani wawan kallo yana son tambayarsu me ya kawosu, amma kuma yana tunanin da inda zai fara, saboda magana da mace ya d'aukeshi tamkar b'atawa kai lokaci ne.
    Kallon da ya ga miemie na binshi da shi ne ya sa ya yi saurin kallon jikinshi.
    Duk sumar jikin ta bayyana, kyakkyawar surarshi kuwa ta fito sosai.
     Bakin madubinshi ya isa bai ko tanka masu ba. Wani body spray ya fara feshe jikin da shi sannan ya shafa mai, ya sake bin jikin da turaruka kala kala.
     Ganin tsayuwar tasu ta yi yawa ya sa Ikram fad'in "Yaya dama Momy ce ta ce na zo na baka hak'uri. Ba da gangan..."
     Bata k'arisa maganar ba ya d'aga mata hannu alamar ta yi shiru. Dakatawa da maganar ta yi tana binshi da kallon tsana, haushin kanta kawai ta ke ji da har ta shigo d'akinshi ma.
      Hanyar waje ya nuna masu alamar su fita kawai baya son ganinsu. Babu musu kuwa suka fita d'in.
    "Ikram wallahi komai nashi burgeni ya ke, kin ga jikinshi kuwa? Ga shi da faffad'an k'irji irin wanda na ke ga namiji." Miemie ta fa'da farin ciki fal a zuciyarta.
     "Wato ke bama ki ji haushin abin da ya mana ba ko? Ya maki kyau." Ta yi k'wafa tare da yin sauri ta bar miemie baya. Ita kam wani irin sanyi ta ke ji a zuciyarta.
    Ko da suka koma d'aki momy ta gane cewa lallai Haidar ya yi halin nashi.
    "Kin bashi hak'urin?" Momy ta tambayeta.
    "Ehh na bashi amma ko 'kala bai ce mana ba, koromu ma ya yi da hannu." Ta fad'a rai 'bace.
     "To ai shi ke nan tun da dai kin bashi, dama abin da na ke son ji ke nan. Yanzu Khalid ya min bayanin yanda kuka yi, gobe zaki fara zuwa ko?"
    "Eh momy gobe zan fara zuwa insha Allahu. Momy wurin har da larabawa da indiyawa." Ta fad'a tana murmushi.
      "Ke autar momy fad'a min gaskiya. Wurin ne ke da larabawa da indiyawa? Ko dai sun je wankin kai ne?" Momy ta fad'a.
     "Anya kuwa? A wurin salon dai na hango ba'indiyar tana gyarawa wasu 'yan mata gashi. Balarabiyar kuma aikinta kawai koyawa mata rolling d'in mayafi."
    Jinjina kai momy ta yi cike da mamaki ta ce "Ki ce dai wurin babban wuri ne?"
     "Sosai ma kuma momy." Ta fa'da.
     "Miemie bak'uwa ta zo ko abinci ba za'a bata ba ko? Kin kyauta." Ikram ta fad'a tana murmushi.
     "Sorry k'awata, ai yanzu kika zauna ko? Bari na kawo miki nima na fara haramar komawa gida. Khairat har ta yi bacci tun d'azu, gashi yamma ta yi." Ta mik'e tare da nufar kitchen ta zubowa Ikram faten dankalin da ta girkawa momy.

*****
      Bayan ta gama cin abincin ta je ta yi wanka ta canza kaya sannan ta fito, ita ma miemie shiryawar ta yi bayan ta tashi Khairat ta mata wanka.
    Saukowa suka yi miemie ta ma momy bankwana ta ce zasu tafi.
      "Za'a zo d'aukarku ne?" Momy ta tambayeta.
     "A'a momy, a daidaita sahu zamu hau." Ta bata amsa.
    "A'a ba za'a yi haka ba ga motoci a gida. Ikram je ki 'dakin Khalid ki kirashi ya kaita, sai ki rakata ku tsaya shop a ma Khairat siyayya."
   Da gudu kuwa ta isa 'dakin Khalid, zaune ya ke ya zabga uban tagumi yana tunani.
     "Ya Khalid." Ta fa'da amma sam bai san ma da wanzuwarta a d'akin ba.
    Sake kiran sunanshi ta yi amma yanzu ma bai ji ba sai tunaninshi kawai ya ke.
     Hankalinta ne ya tashi da sauri ta d'an bubbugashi, firgigit ya yi tare da dawowa daga tunanin yana 'kir'kiro murmushi.
     "Lafiya na ganka haka? Tunanin me ka ke?"
    "Lafiya lau ba damuwar komai." Ya bata amsa.
     "Ban yarda ba yaya, ko dai ita ce ta b'ata maka rai?" Ta tambayeshi tana dariya.
      "Ita wa?" Ya tambayeta.
     "Ita Aunty'n tawa mana. Ni dai ka zo momy ta ce mu miyar da miemie gida." Ta yi gaba ya mara mata baya.
    Ko da suka fito bakin motar suka shiga ciki, Khalid ya yi ya yi ya tada motar amma ta k'i tashi, hakan ya sa ya fito ya sake d'an duddubata ya koma ciki amma har yanzu bata tashi ba.
   Momy na tsaye tana tambayar yanda aka yi Khalid ya bata amsa sai ga Haidar ya fiddo mota zai fita.
    "Yi sauri ka fita ka tsayar da yayanku gashi can zai fita sai ya tafi dasu." Momy ta fad'a tare da tsayar da Haidar d'in da hannu saboda ta ga ya d'an waiwayo.

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now