39

881 53 0
                                    

*SHI NE SILA!*
           😪😪😪

              Na Princess Amrah
*NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
                           (2018)

39~  Da k'yar ya iya furta mata "Nadiya..." cikin sassanyar murya.
     Bata ce komai ba sai kallon Khalid da isowarshi wurin ke nan yana fad'in "Zo mu tafi Ikram, komai ya wuce ai."
    'Ikram?' Abbas ya tambayi kanshi. 'To ko dai ba ita ba ce? Waccan sunanta Nadiya, wannan kuma Ikram.' Ya maimaita a zuciyarshi.
    D'an satar kallonshi ta yi ta ga har yanzu bai daina kallonshi ba. "Ina Hajiyar ta ke?" Ta tambayi Khalid.
    "Na kaita mota, ki yi sauri mu tafi ita kad'ai na bari, kuma da alama hankali a tashe ya ke." Ya fad'a yana kallonta.
    "Allah sarki! To mu tafi." Ta fad'a had'e da bin bayan Khalid. Ya sani sarai Abbas na kallonshi kuma da alama yana son ya mishi magana amma ko kallonshi bai yi ba, saboda a duk lokacin da ya kalli Abbas yana tuno sanda ake rikonshi zai bugi abbansu, wanann wani abu ne da ya faru wanda bai zai tab'a mantawa da shi ba.
    Tsabar 'kwarjini da Ikram ta ma Abbas ya sa ya ma kasa furta mata komai, sai bayan ta tafi ya naushi iska da hannunshi wani irin zazzafan hawaye na fito masa. "Mesa ka yi shiru Abbas? Why?" Ya fad'a a bayyane.
    Su kuwa su Ikram mota suka isa a lokacin Goggoji na zaune a kujerar baya, bayan sun shiga Khalid ya tayar da motar Ikram cikin k'arfin hali ta ce "Sannu Hajia..."
    "Ban cancanci maganar kirki daga bakinki ba Ikram. Hak'i'ka na ci miki fuska, na miki abin da sam bai kamata ba. Amma dan Allah ki gafarta min, *na yi da na sani* tun daga ranar da aka fara kirana cewa sai na fad'awa wani abin da ya faru. Na sani cewa ban kyauta ba, ban wa Alhaji Muhammadu da zuri'arsa adalci ba, duk da ya ke ni na haifeshi da cikina amma rud'in shaid'an da son abin duniya ya sa aka had'a baki dani aka sace yarinyar da bata ji ba bata gani ba. Kai cona!" Ta 'kara fashewa da kuka.
    "Dan Allah d'an dakata Yaa Khalid." Ikram ta fad'a.
   Dakatawa kuwa ya yi da motar duk da bai san dalilinta na cewa ya tsaya d'in ba.
     Saukowa ta yi bayan ta bud'e motar ta fito, ta rufe sannan ta bud'e baya ta koma inda Goggoji ta ke sannan ta rufe ta ce "Mu tafi yaya." Ya tayar da motar kuwa.
    Rik'e hannun Goggoji ta yi ta ce "Duk da ya ke kin yi abu wanda ba mai kyau ba ne a baya, amma ki sani cewa Allah mai karb'ar tuba ne, ni na yafe miki sai ki ci gaba da neman yafiyar Allah da kuma Momy wacce a ko yaushe ta ke cikin takaici da bak'in cikin abubuwan da kuke guma mata. Na san halin momy, ita d'in mai hak'uri ce kuma na tabbatar da zata yafe miki."
    Cikin kuka Goggoji ta ce "To ina fatan hakan 'yar nan. Allah ya miki albarka ya baki miji na gari.."
    "Amin." Ikram ta fad'a had'e da k'irk'iro murmushi wanda iyakarsa a fuska bai kai zuci ba.

***
    Gidanta suka fara sauketa, har ciki Ikram ta rakata inda ta samu Fareeda zaune ta rafka tagumi tana tunanin inda su Goggoji suka tafi, saboda ita kam basu fad'a mata zasu je kotu ba, duka ma case d'in bata san da shi ba.
    Bayan Ikram ta zaunar da ita ta ce "Allah ya 'kara lafiya Hajiya. Mu zamu wuce." Suka tafi, Khalid kam dama bai shigo ciki ba, Ikram na shiga mota suka kama hanyar gida a lokacin kusan k'arfe d'aya na rana.
    Abbas kuwa daga nan ba gida ya wuce ba, wurin wani abokinshi ya tafi domin neman shawara.

***
    A gajiye suka koma gida, momy bata parlor hakan ya tabbatar masu da cewa ta je salla, hawa Ikram ta yi sama ta cire kaya ta d'an watsa ruwa sannan ta saka 'kananan kaya dan dama tana hutun sallah. Kallon mirror ta yi ta saki wani irin murmushi wanda ban tab'a ganin ta yi irinshi ba sai yanzu. A hankali ta furta "You did it Ikram. Ikram kin cika masu burinsu." Ta sake yin wani murmushin wanda har sai da ha'koranta suka bayyana.
    Cikin natsuwa ta 'dauki wayarta ta latsa kiran wata k'awarta, bugu 'daya kuwa ta da'uka suka gaisa ta ce "Kin ga yau ban samu na shigo School ba ko? Wallahi wani abu ne ya tsayar da ni, in ce dai wani abu bai wuceni ba."
    A d'aya b'angaren k'awar tata ta ce "Abin da aka yi jiya ne aka maimaita. Highlighting and contouring. Kin san wai daga shi an gama b'angaren make up baki 'daya."
    "Hakan ya min da'di kuwa. To na gode sosai 'kawata. Sai anjima." Ikram ta tsinke wayar.
    Turare ta feshe jikinta da shi sannan ta sauka k'asa ranta k'al, ta ma rasa ta inda zata fara labartawa Momy wannan daddad'an zance duk da ya ke ba wai tana son fad'a mata ainahin cewa ita ce ta tsaya a maganar  har asiri ya tonu ba.
    Ko da ta sauko kuwa momy na zaune tana kallon wani Indian film mai suna 'Ramayya Vastavayya' wanda arewa 24 suka saka. Da ganin momy tana jin dad'in film d'in hakan yasa ko da ta isa parlor'n bata zauna ba, dining kawai ta zarce domin zuba abinci.
     Farar shinkafa da miyar dankali ce aka dafa, zubawa ta yi kad'an sannan ta tsiyayi ruwa daga water dispenser ta d'ora a dining table 'din.
     Ta d'aga cokali zata kai baki ke nan ta ji Khalid ya ce "Ke amma yarinyar nan son kanki ya yi yawa. Wato sai ki zuba naki ni kuma ko oho ko?"
    Kai cokalin ta yi a bakinta sannan ta ce "Kaima d'in ai ban hanaka ka zo ka ci ba."
    "Wannan yarinya akwaiki da tsiwa ga iya zunguro baki kamar shantu. Ke wannan idan kika yi aure ina jin sai kin ringa zungure mijin da bakinki idan bai yi hankali ba."
    Bata san sanda ta kece da dariya ba, har ga Allah Khalid na burgeta, ko ba komai akwai barkwanci da son saka mutum cikin farin ciki, barinma kuma yau da suke cikin tsantsar farin ciki wanda baya iya misiltuwa.
    Abincin ta zuba masa a plate sannan ta zuba miya daban ta ce "To acici gashi nan na zuba maka."
    "Kin kyauta sosai 'yan matan momy. Allah ya miki albarka kin ji?" Ya fad'a had'e da kanne mata ido d'aya.
    Hannu ta d'aga zata k'wala masa cokalin hannunta ya yi saurin kaucewa yana fad'in "Allah dai ya baki hak'uri." Yana dariya.
    Duk wannan dramar tasu momy tana jinsu. A ranta ta ce 'Da shi ya kamata na had'ata, sai dai kuma an samu akasi, saboda shi d'in ya ce min ya tsaida wacce zai aura, wanda bata shiri da shi 'din dai zan aura mata, na san da yardar Allah zasu daidaita kansu.' Ta yi murmushin dattako had'e da ci gaba da kallonta.
     Bayan sun gama cin abinci nat suka dawo parlor sai zaulayar junansu su ke suna dariya.
     Shigowar Haidar ce ta dakatar da su daga dararrakun da su ke yi, "Sannu babban yaya, kai da ka ce kana da aiki da yawa ne ka dawo tun yanzu?"
    Guntun tsaki Haidar ya yi ya ce "Ji na yi ba zan iya ba. Da dare zan ma wani theatre saisa kawai na dawo, wai dan na d'an huta kafin nan."
     Momy ta ce "To ai sai ka je ka ci abinci. Ikram ki zubo ki kawo masa a nan."
    Samun kanshi ya yi da kasa cewa ta barshi, a karo na farko ke nan da ya ji yana sha'awar ta zubo masa abincin da kanta.
    "To momy." Ta fad'a dan sai da ta d'an jinkirta ko zata ji ya ce mata ta barshi amma ta ji akasin haka.
    Nak'o masa plate ta yi nat da abinci sannan ta zubo miyar a container daban, da gangan ta zubo abincin da yawa dan kawai ya tanka, saboda ta san ba ya wani cin abinci sosai, ko rabin wancan 'din ba zai iya ci ba.
     Mamaki kuwa ya bata dan bai ce mata komai ba sai dai kawai ya bi abincin da kallo sannan ya 'dan kalli Ikram data guntse dariya tana jiran tankawarsa.
    Fara cin abincin ya yi ba tare da ya fa'di komai ba, cike da natsuwa ya ke kai loma bakinsa, 'Abincin ma sai an masa yanga.' Ikram ta fad'a a zuciyarta.
    Kad'an ya ci sannan ya umurci Ikram da ta d'auke ta kai kitchen, bata musa masa ba kuwa ta d'auka ta kai ta dawo.
    Sai da Khalid ya tabbatar Haidar ya gama cin abinci sannan ya ce "Yaya albishirinka."
    Ba tare da ya kalleshi ba ya ce "Ina jinka."
    "Ni kuma ba zan fad'a ba sai ka ce goro." Khalid ya fad'a yana dariya.
   Banza ya masa ba tare da ya kuma fad'in komai ba. 'Karfin hali irin na Khalid shi ya sake yi masa magana "Big bro your dream comes true today..."
     "What!? What do you mean?" Haidar ya fad'a, saboda kowa ya san dream 'dinshi bai wuce asirin wanda suka yi aika aika ga k'anwarsa ya tonu ba.
     Ajiyar zuciya ya sauke tare da fad'in "Dont try to kid me Khalid."
    "Am not kidding You yaya Aliyu. Yau dai asirinsu ya tonu har ma an yanke masu hukunci, yanzu haka suna gidan yari ina tunani." Khalid ya fad'a.
    Mik'ewa ya yi ya matso inda Haidar 'din ya ke ya ce *"Ikram  ce silar ganosu Yaya..."*
    Ido Haidar ya bud'e tun Khalid bai gama maganar ba, miyar da kallonshi ya yi ga Ikram sannan ya kalli Khalid, "What are you still saying? Ikram ce ta gano wanda suka sace Feenah har suka mata fyad'e? Garin ya haka? Ya aka yi ta gano?"
      "Calm down yaya, I'll explain everything to you." Khalid ya fad'a.
     Momy cike da d'aurewar kai ta ce "Nima kaina ina son jin abubuwan da ke faruwa, Ikram ya aka yi?"
     Da sauri Ikram ta mik'e ta isa inda Khalid ya ke, hannuwanshi duka biyun ta ri'ke ta ce "Please don't tell them Yaa Khalid. Bana so idan na yi abu ana fad'i..please." Ta yi kamar zata yi kuka.
     "Ya zama dole na fad'a masu abin alkhairin da kika mana, ko ba komai darajarki zata d'agu ga duk wani d'an gidan nan ko kuma masoyin gidan nan. Momy Ikram duk zaman nan ashe ta sa a mata bincike, itama kuma da kanta ta ringa yi ta hanyar Barr. Kareema har suka gano wanda suka sace Feenah da kuma wanda suka mata fyad'e.."
     Tuni Haidar ya mik'e tsaye cike da mamaki, binsu kawai ya ke da kallo dan shi kanshi a d'aure ya ke ya ma rasa abin da zai fad'a.
     "Momy Ikram ce ta tabbatar da cewa su Goggoji ne suka saka aka sace Feenah...." Ya kwashe komai tun daga farko har k'arshe ya zayyane masu.
      "Innaalillahi wa innaa ilaihi raji'un! Goggoji? Kakar taku?" Momy ke ta maimaitawa kanta d'aure, sai dai kuma ta matuk'ar tausayawa Goggoji, ko ba komai *Ikram ta zama silar shiryuwarta.* Ta kamo Ikram da ke zaune har yanzu bata saki hannun Khalid ba, sosai ta ji haushin fad'a masun da Khalid ya yi, bata so hakan ba, sai dai so ta yi kawai a ce asiri ne ya tonu ba wai ta hanyarta ba.
     Zaunar da ita ta yi kusa da ita ta ce "Ikram ashe abin da kika yi ke nan a b'oye ko ni baki bari na sani ba?"
     Shiru Ikram ta mata. "Ikram kin san kuwa abin da kika aikata risky ne? Ko kad'an kar ki sake yin abu baki shawarceni ba kin ji?"
     Kai Ikram ta d'aga cike da natsuwa har yanzu dai bata furta komai ba.
     "Thank You very much 'yata, Allah ya saka miki da alkhairi, Allah yasa hakan da kika yi ya zama *silar* shigarki aljannah." Momy ta fad'a cike da soyayyar Ikram.
      Haidar da ya zama speechless bin Ikram kawai ya ke da kallo, ya ma rasa abin da zai yi, tabbas ya san yau kam Ikram ta cika masa burinsa, ta masa abin da shi da kanshi ya kasa yinshi, tun bayan rasuwar Feenah ya ke bincike amma ya kasa gano wanda suka mata aika aika, sai gashi cikin lokaci kad'an Ikram ta gano, *lallai Ikram ta zama silar dawowar farin cikinshi,* ta masa abin da ba zai tab'a mantawa da ita ba har k'arshen rayuwarsa. Ya zama dole ya cire girman kai for once in his life ya nemi yafiyar wata mace, ya kuma yi mata godiya a bisa namijin k'ok'arin data masa wanda shi ya kasa yi.
    Bai san sanda ya gurfana gaban Ikram da Momy ba, ganin haka yasa Ikram d'aga kai ta kalleshi sannan kuma ta sunkuyar da kanta.
     A hankali ya furta "Na miki mummunar fahimta Ikram, yanda na d'aukeki sam ba haka kike ba. Kin kyautata min kin cika min burina, a ce wai yarinyar da na fi ji ma haushi a rayuwata *ita ce silar* wanzuwar farin ciki a cikin zuciyata, farin ciki wanda kusan shekarata hud'u rabona da shi. Ki yafe min Ikram a bisa wulak'ancin dana ringa miki. Na gode k'warai Allah ya miki albarka.."
    Tun da ya fara maganar su duka uku da ke d'akin su ke binshi da kallo, Baabah Naanah ma da ke tsaye kusa da dining sai da ta yi mamaki.
    'Lallai Ikram ta dawo masa da farin cikinsa yau, da alama d'ana zai koma kamar yanda ya ke a baya.' Momy ta yi murmushi.
     "Ni ba dan ka gode min na yi ba, saboda dan Allah da kuma momy da Yaa Khalid na yi, no need of thanking, just thank God." Ta fad'a had'e da mik'ewa ta nufi up stairs. Cike ta ke da mamakin Haidar, ashe akwai ranar da zai iya gurfana a gabanta har yana neman gafararta? Lallai.
     Ko da ta shiga d'akinta kwanciya ta yi ta d'an rufe idonta, a hankali ta furta "Na gama da wannan saura kuma gano wanda suka sace Yaa Khalid." Ta d'an yi murmushi. "Shima insha Allahu zan yi nasara, kuma babu wanda zai sani a wannan lokacin sai dai kawai Barr. Kareema, itama kuma saboda ta bani shawara ba wai dan ta tayani ba." Ta sake yin wani murmushin had'e da shiga game d'in candy crush da ta kai level 900.
     A parlor kuwa sai farin ciki su ke, kallo d'aya zaka ma Haidar ka fuskanci canji na lokaci guda a tattare da shi, fira su ke sosai Khalid na k'ara basu labarin 'kullin da suka ma su Abbas da kuma wayon da Ikram ta masa, sosai Momy ke dariya, lallai Abbas wawa ne, kuma wai har ya ganta a kotu ya kasa tantanceta. Sun jima a haka har aka kira sallar la'asar sannan suka tashi, su biyun suka nufi masallaci, momy kuma ta nufi d'akinta domin sauke tata sallar.

_Jinjina ga 'yan d'in Lubbatu's crew, thanks for the love and support..Amrah loves you so so so much._

*team Ikramhaidar*
*team Ikramkhalid*

SHI NE SILAH!Where stories live. Discover now