✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
Page 36-40
Har suka ƙara so cikin school ɗin ta mai sallama ta re da Godiya ta fita a cikin motar da sauri,
Haka wunin ranan ta yi lecture ta gama, ta yi sallama da sahura ta fito daga lecture hall ɗin ta tadda nafisah na jiran ta,
Kama hanya fita daga cikin makarantar su kai , a inda suka tadda motar lion jiya yauma anan suka tadda ita sai dai, yau yana cikin motar bai fito ba,
Nufar inda motar ke fake sukai kawai suka shiga bakin su ɗauke da sallama dukan su , nafisah ta gaishe da lion ya amsa,
Kafin ya tada motar suka ɗauki hanyar barin kongo, yauma sai da yaje ya aje nafisah kafin ya baro cikaji ,
Koda suka ƙara so sapale can nesa da unguwar ya faka motar, yau sun gama lecture da wuri karfe huɗu da rabi kenan,
Yawan cin mutane suna zaune a ƙofar gida jen su ne a wannan lokacin, shiyi sa lion ya faka motar shi a nesa dan goje wa matsala.
A'ishah ba tare da ta kalli lion ba ta ce, jazakallahu fi Janna Allah ya biya ka , ta yin ƙura zata fita a motar ya ɗan riƙo gefen hijabin ta, hakan ya dakatar da A'ishah daga fita a cikin motar, ta jiyo da sauri,
Bisa kuskure ƙayar idanun su ya sarƙe da na juna, cikin wani kallar shauƙi suke kallon junan su ba tare da sun san da faru War haka ba,
Ko shike za a iya cewa basa cikin hankalin su a wannan lokacin,
A'ishah ce ta fara dawo wa cikin hankalin ta, da sauri ta ɗauke idon ta daga kallon shi, wata kunya ta kama ta, ji tayi kamar ƙasa ta buɗe ta shige,
Shi ma lion dawo wa yayi cikin sens ɗin shi, wani haushi ya kama shi na abin da ya aika ta, da sauri ya saki hijab ɗin ta da ya riƙe,
Ya fuske da shike shi namiji ne, yace, an jima da daddare zan kira ki sau ra kiƙi dauka,
Ba tare da A'ishah ta amsa mai ba ta buɗe murfin motar ta fita da sauri ta kama hanyar gida,
Lion wani killer smile yayi ya shafa kanshi, ya tada motar ya bar gurin,
Wasu ma gidan ta na hango a zaune a ƙofar wani gida nesa kaɗan da in da lion ya faka motar shi,
Magana suke kamar haka,
Ɗayan yace,
Shin Malam Mudi kaga abin da ido na yake gane min kuwa,
Na kusa da shi kamar jira yake ya amsa mai da cewa, Ni ko na gani,
Shin yarinyar ba yarinyar Malam malami ce ba , motar da ta fito a ciki ko kaf fara bazan yi ba ta wancan tantirin yaron ce ɗan gidan Alai Muhammad,
Wanda ya fara magana ya ɗaura da cewa duniya ta lalace, yanzu ace yarinyar da ake kwatance da ita a cikin unguwa , ita ma ashe sumumu kasam ce,
Malam Mudi ne yace kai dai malam Mudi bari, dole ma uban yarinyar ya sani,
Dan bazai yiwu yana yawo yana ya ɗawa da Allah ya ce Annabi yace, ashe tsiya tana nan tattare a gidin shi, dole a ɗauke mataki akai,
Cigaba da zage-zagen su sukai a gurin,
A'ishah ko a ƙofar gida ta tadda malam gaban shi kuma almajiran shi ne suke ɗaukan karatu,
Dum gaban ta ya bada gani Nuhu a gaban malam, haka kawai ta ji bata ji daɗin dawo War shiba, daƙyar ta daure ta ƙara sa gaban malam ta duƙa tamai sannu da gida, Malam ya mata sannu da dawowa,
Kafin ta tashi ta shiga cikin gidan, Nuhu sai murmushi yake ganin A'ishah yana sunne kai,
Da sallama A'ishah ta shiga gida ta tadda mama a gaban murhu tana girki, sannu da gida tawa mama ta shiga ɗakin ta , ta rage kayan jikin ta,
Ta fito tayi alwala ta koma tana ƙidar wa ta fito ta ansa girki a hannun mama ta ƙara sa,
Shiko lion gida ya koma, yayi shiri cikin kayan kwallo kafin ya fito suka wuce filin kwallo shida su kisser,
Da daddare bayan sallar ishsha'i, sai da malam ya shigo cikin gida kafin A'ishah ta fito ta zuzzuba musu abin ci,
Suka yi Bismillah suka fara ci, bayan sun gama A'ishah ta kawar da kwanukan daga gurin ta dawo ta zauna,
Ɗaya daga cikin almajiran malam ne yayi sallama ya duƙa a gaban su kafin yace wai A'ishah ta zu inji Nuhu,
Mama ce tace kaje kace mai ga ta nan zuwa, wani tugogin baƙin ciki ne ya turnuƙe A'ishah, ba dabin mama da malam dake zaune a gurin ba, ba abin da zai sa ta fita,
Tashi tayi ta shiga cikin ɗaki ta dauki hijib ta fita,
Inda ta hango Nuhu ta nufa bada bin hasken haƙoran shi ba ba abin da zai sa a gane Nuhu,
Da ƙara sawar A'ishah ta ja ta tsaya, tana kallon gefe da ban, ba tare da tace komai,
Washe baki Nuhu ya fara yana cewa A'ishah A'ishah ta kenan, baƙaramin kewar ki nayi ba kwana biyun nan, nai ta gwada nombar ki nayi ba amma ba notwon , zuba ya cigaba da yi bai damu da rashin maganar A'ishah
Ba,Surutun Nuhu ne yasa kan A'ishah ya fara ciwo, ɗan guntun tsaki taja wanda ba ɗabi'ar ta bace , ta ɗan yatsina fuska tace Ni zan ɗan shiga gida kaina na min ciwo,
Bata jira taji mai zai ce ba ta shiga gida, bin bayan ta da kallo Nuhu yayi yana mamakin sau yawar ta,
Share wannan tunanin yayi ya raya a cikin zuciyar cewa wata ƙila ciwon kanne ya ta kura mata, ɗakin su ya nufa ya na tunani kala kala cikin zuciyar shi,
A'ishah ko tana shiga gida ta tarar malam da mama har sun shiga cikin ɗaki, daga Muryar ta tayi yadda zasu ji tace mama da malam na dawo, sannan ta shiga cikin ɗaki, ta cire hijab ɗin ta rufe ƙofa, ta hau kan ƴar katifar ta, ta kwanta,
Da kwanciyar ta wayar ta ta fara ringing, ba kowa bane ke kira illa,......
I'm so sorry, na gama typing mai yawa , naje nayi updating app ɗin na dawo naga ya sha re,
Ga dai wannan kuyi manegi dashi,
Don't forget to vote and comment bye bye.
y͜͡a͜͡r͜͡ m͜͡u͜͡t͜͡a͜͡n͜͡ z͜͡a͜͡z͜͡z͜͡a͜͡u͜͡
🆂︎🆄︎🅻︎🅴︎🅹︎🅰︎
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...