𝐏𝐚𝐠𝐞{41}•
🅝︎🅞︎🅣︎ 🅔︎🅓︎🅘︎🅒︎🅣︎🅔︎🅓︎
*B͎i͎s͎m͎i͎l͎l͎a͎h͎*
,, A'ishah pov°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
"Kano, shine naji baki na ya furta haka kawai naji sunan Garin ya kwanta min a rai, duk da bani da kowa acan , a zahiri ma ban taɓa barin Zaria ba zuwa wani gari daban ba, sai a yau ɗin da kaddara tasa zan yiwa garin nisa,Ɗaukan kaya na, akai aka sa a bayan mota, ina shiga ya rage saura mutum biyu motar ta cika , gaba na faɗu wa ya ringa yi, har lokacin da motar ta cika, aka zo amsar kuɗin mota na ba da,
Bayan an amshi kuɗin, kowa driver ya shiga cikin mota ya tada muka bar cikin gare jin , muna hawa titin kano na jin gina kai na da jikin kujerar motar ina sauƙe nun fashi a hankali,
Zuwa wani lokaci kadan muka fara shiga cikin garin Kano tun a hanya wasu suka fara sauka, har aka shiga cikin garin Kano gaba ɗaya,
Driver ya kawo dai-dai in da suke tsaya wa, na shiga duniyar tunani, wata tsohuwar mata dake kusa dani ta dafa Ni tace ƴata an kawo inda za'a sauka,
To nace na tashi muka fita tare , aka fito mana da kayan mu, sake ce min tayi baza mu samu abin hawa sai mun yi ɗan gaba ƙaɗan,
Da to na sake amsa wa na ɗauƙi kaya na bani bayan ta, har muka kawo inda masu adaidaita suke , ta gaya musu in da zata je, ta shiga ba nima shiga nayi ba tare da na gayi in da zani ba,
Ana kawo dai dai unguwar da tsohuwa ta gayi a kai ta, aka sauke ta , ta fita, me adai-daita yana tan baya ta Hajiya ke ba anan zaki sauka bane nayi shiru ban ce mishi komai ba,
Ya ja ya cigaba da tafiya,har yayi nisa sosai ya sake tam baya ta wai ina zaki je Hajiya, nan ma shiru namai,
Kashe adai-daitar yayi ya fito waje yace dal Allah fito Malama Ko an gaya miki na fito ne dumin In ɗauke ki kawai in ta zaga gari dake,
Wannan wani irin wulaƙan ci ne, ko kina hauka ne, fita nayi,
Kaya na ya jefo min waje , ya fisge dubu ɗayar dake hannu , ina jiran ya bani can ji, be sau rare niba ya ja adai-daitar shi ya ƙara gaba,
Tsaya wa kawai nayi ina bin in da ya bi da kallo, na jima a tsaye a gurin kafin na ɗauki kaya na cigaba da tafiya,
Tafiya nake kawai ban san in da nake nufa ba, ungu wanni kawai nake shiga, har yamma ta kawo kai,
Yun wa ce ta fara kama Ni ciki na ya fara kiran ciroma, sai. Lokacin na tuna wunin yau ban da komai a ciki na ba,
Wani guri na hango, ana sai da abin ci, na ƙara sa na ce a bani,
Na zauna akan Bencin gurin na fara ci, na cinye nasai , ruwa nasha, nayi alwala, naje can gurin wata bishiya, na kwance ɗan kwali na na shin fiɗa nasa kaya na a gaba , na tada salla
Sai da na biya bashin sallolin da ake Bina gaba ɗaya, lokacin gari yayi duhu, amma kasan cewa garin Kano ko wani lungu akwai fitilun kan hanya, har yanzu zirga-zirgar mutane bai daka taba kamar rana kowa hidimomin shi yake,

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Roman d'amour* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...