𝐏𝐚𝐠𝐞{42}•
🅝︎🅞︎🅣︎ 🅔︎🅓︎🅘︎🅒︎🅣︎🅔︎🅓︎
*B͎i͎s͎m͎i͎l͎l͎a͎h͎*
"A'ishah shiga cikin shagon tayi ta samu guri ta aje jakar ta , ta zauna ta haɗe kan ta da guiwar ta, ba jima wa bacci ya kwa she ta,
Gari ne ya fara waye wa, ƴan matan da suke taya maman ladi sai da abin ci, suka fara zuwa, duk wacce tazo taga Aishah sai tayi mamakin ko wace haka a kwance,
Lokacin da Aishah ta tashi kusan ƙarfe goma sha daya na safiya,
Gyara hijabin ta tayi ta zauna, mama ladi ta shigo cikin shagon tana cewa au ƴan mata ashe kin tashi,
Shine ba ki fito kin ci abinci ba, sun ku yar da kan ta ƙasa Aishah tayi bata ce ko mai ba,
Maman ladi ta zauna a gefen ta, tace yarin ya mai ya fito da ke daga gida haka har yasa kika kwana a guri mara tsaro irin wannan,
A'ishah shiru ta sake yi bata ce ko mai ba, mama ladi bata ji haushi ba ta sake tamba yar Aishah da, baki da gurin zuwa ne? , Aishah a wannan ka ron ta bata amsa da ehhh,
Mamam ladi tace zaki iya zama tare da Ni ki rin ƙa min aiki ka mar yad da kika ga sai ran ƴan matan can ke yi,
A'ishah ta sake cewa eh bata re da tuna nin ko mai ba, mama ladi tace to madallah Ni kuma na miki alƙawarin baki ma sauƙi,
Duk yan matan nan da kike gani mafi yawan cin su a , gida na suke zama, muna sana'a muna rufa wa junan mu asiri,
Ita dai Aishah ham dala tayi cikin zuciyar ganin cewa zata samu gurin kwana, daga nan bata sake cewa komai ba,
Maman ladi ta ƙwa da kiran sunan Jamila, wata budurwa, da fuskan tar ta sha bilicin ne, ta shigo cikin shagon tana tau na cingam,
Tsaya tayi a kan su ta ce maman ladi gani naji kina kira na,
Maman ladi ba tare da damu war komai ba tace, kin ga ƴar uwa kuka samu , je ki kawo mata abin ci da abin sha,
Maman ladi ta tam bayi Aishah Meye sunan ki, Aishah ta bata amsa da sunana Aishah,
Jamila sai da ta ƙare wa Aishah kallon tsaf sama da ƙasa, kafin ta wani ya tsine fuska, sannan ta fita,
Wasu daga cikin ƴan matan ne suka fara tam bayar Jamila, wace ce wacce suka gani cikin shagon, Jamila ta ja wani mugun tsaki tace,
Ku dai wallahi iyayen ku sun yi asarar haihuwa ba abin da kuka sani sai muna furci da raba wa maza canfanin ku, shiyisa duk kwakwalwar ku ta to she,
To so kuke ku sani sabuwar karuwar ce maman ladi ta kawo, yan zu sai ko wacce sai ta koma gurin aikin ta,
Jamila na cewa haka , ta wuce ta fara zuba masa , wasu daga cikin ƴan matan suka bi bayan Jamila da harara, suna cewa Shegiya Jamila baƙar kuna ma, daga tam baya zata bimu da gori, sai kace ita ba mata irin ta take raba wa canfanin nata ba,
Yoo ba gwamma mu ba antena ake su burɓuɗa mana,
Haka suka cigaba da gaye gayen su,
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...