page 43

276 12 0
                                    

Page { 43 }


" ƴau kwanan A'ishah biyar da zuwa garin Kano, daga ranar da ta zo zuwa yau ta ga abu iri iri a cikin gidan da shagon sai da abin ci na mama ladi

Washe garin ranar da mama ladi ta sau ke cikin gidan ta , A'ishah ta fara zuwa shagon tana ɗan taya su wan ke wan ke da ɗan abin da ba a rasa ba, dan mama ladi tace ta fara da wanke wanke kafin ta ƙama ƙware ta gane kan gadon abun,

Kawo iyan zu A'ishah ta gane duk wani abu da mama ladi da ƴan matan da suke mata aiki suke ai kata wa a fili da ɓoye ,

Wato sun fake ne kawai da sai da abin ci amma a zahirin gaskiya akwai wata sana'a da suke yi daban a ɓoye,

A zahiri za a ce mama ladi tai maƙon ƴan matan take tana basu ma sauƙi tare da sana'ar yi amma a ɓoye maman ladi magajiyar ƙaruwai ce ,

Hur ɗa take da manyan manyan masu kuɗi na garin Kano mata da maza , tana kai musu ƴan mata suna biyan buƙatar su da su ana bata kuɗi ,

A'ishah tuni ta fahimci haka, zaman ta a gidan tayi ne dan bata da gurin zuwa ta zauna ne kawai dan ta ƙara sanin kan garin dan in ta bar gidan bata da gurin zuwa

Yau da ta kasance ranar ta , ta shi da a gidan, ƙarfe huɗu na asuba ta tashi, ta wanke bayi tayi wanka da Alaula tun kafin kowa ya tashi layi yayi yawa,

Ta gabatar da sallar asuba tare da yin azkar ta ɗaura da addu'ar neman tsari daga duk wani me nufin ta da Sheri , tare da neman yafiyar Ubangiji akan lefukan da ta aika ta,

Haka ta cigaba da zama tana karatun Alkur'ani cikin zuciyar har gari ya fara ƴin haske, dan kaf gidan ba dadduma bare Kur'ani

Yan matan gidan suka fara tashi ana bin layin shiga cikin bayi, tuni cikin gidan ya kacame da baya niya,

A'ishah tashi tayi ta ninke ɗan kwallin ta da tayi Sallah akai , sannan ta fito daga cikin ɗakin bata tan kawa kowa ba a tsakar gidan tasa kai ta fita a cikin gidan,

Yan matan ganin A'ishah ta fita suka haɗa baki suka saki buɗa , tare da cewa ayi dai mu gani, mun nan anan wai inyamuri ya faɗa kwata,

Ohmm kwana nawa ne yarinya zaki dawo kan han ya madai dai ciya ai duk wannan abin kanta kile ne , tana fara amsar ƴaƴan banki sai ta fi kowa sheɗan ci

A'ishah Kai tsaye shago ta wuce ta fara aika ce aika cen da ta saba cike da tunanin yan da zata bar gidan

Damu war ta ma kar wani abu ya sami abin da ke cikin ta, tuna wa da tayi akwai wani halitta da ke rayuwa a cikin, cikin ta.

Shafa cikin tayi ita da yake shafe baza ka ce akwai wata halitta da ke rayuwa a cikin ta ba, ita man ta sama take wai tana da ciki ..

            *******

         ZARIA

Malam ne zaune tare da mama a tsakar gida akan tabar ma, jikin na shi ya ɗan yi kyau ya ji sauƙi

Malam ne yayi gyran murya yayi yace wai Niko ince dai A'ishah bata fito tsakar gidan nan ne , kwanakin na bana ganin ta sai kace bata gidan,

In ba manta wa nayi ba ko zuwa gaishe Ni bata yi ba tun ranar da aka kai Ni asibiti,

Nan da nan mama ta rude, ta rasa wace irin amsa zata bawa malam , da kyar ta daure ta sai ta Muryar ta sake ƙoƙarin yin rawa, tace malam kenan kasan abin ka ga mai juna biyu,

Bata jin daɗi ne shiyisa bata fito, kuma maganar Hai she ka tana jin tsoron yadda zata fuskan ce ka ne, kar ma ka gan ta baƙin cikin tuna wa da abin da ta aika ta wani ciwo ya ƙara kama ka,

Malam cewa ya'yi in ban da abin mama na baƙin ciki kuma ai ya riga ya kama Ni bazai banin ba ciwo da kun yar abin da ta aika ta har mutuwa ta, sai dai kawai muyi addu'ar Allah ya yaye mana wani abun,

Mama ta ce Amin , malam ya sake cewa yan zu dai shiga ɗakin su ki kira min ita ina so muyi wata magana mai mahimmanci,

Gaban mama ne ya faɗi dumm , ta sake yiwa malam ƙar ya da cewa , ai malam da ka bari zuwa anji ma ta sha magani ta ɗan kwanta kan ta yana mata ciwo ,

Mama ta yiwa malam ƙar ya ne ɗan tasan  ba daɗe wa lokacin shan maganin sa zai yi , in yasha maganin yana sa shi bacci,

zai iya man ta wa har zuwa gobe, tafi so ya kai sati kafin ta faɗa mai abin da yake faruwa, amma ina malam yace,

Ai da dai kin taso min ita haka nan dan so nake mu zauna muyi maganar fahimta da ita lokaci na wuce wa ya kama ta a sanar da uban cikin da ke jikin ta tun kafin lokaci ya ƙure mana,

Mama ta sake cewa a'a malam da dai an bari tayi baccin

Malam bai sake cewa mama komai ya mike, mama ta ɗau ka ya hakura ne zai shiga ɗaki ya huta amma ina malam ɗakin su A'ishah ya nufa ya daga labu len,

Mama subhanallah ta furta ita ma ta miƙe ta bi bayan malam,

Malam da ya ɗaga labulen ɗakin yana cewa maza mama na ta so za muyi magana, sai ya lura ba A'ishah a cikin ɗakin sai nafisa da yaran yaya mardiya a cikin ɗakin nafisa na yi musu lesson,

Nafisa ganin malam a bakin ƙofa tayi sauri ta miƙe, malam ya tam bayi nafisa ke ina yar uwar taki,

Nafisa ta yi ƙifi-ƙifi da ido bata bawa malam amsa ba, malam ya sake cewa ba dake nake na tambaye ki kin yi shiru baki ce komai ba,

Mama dake tsaye daga bayan malam tace yi haƙori malam kazo muje ka zauna zan ma baya Ni,

Malam sakin labulen yayi ya wuce yana cewa ai dole na can can ci Amin baya Ni , Ni da nasa doka kada a sake Abar yarinyar nan ta fita shine aka take doƙar da na shin fiɗa ,

dan a nuna min cewa ban isa na sa doka a bita a cikin gidan nan ba kenan, zama malam yayi a inda ya tashi ,

Mama ma ta zauna kusa da shi, tana ce wa ba haka bane malam kayi hakori ba wanda ya isa ka sawa doka a cikin gidan nan yaki bi kada ka manta dukan mu a karkashin muke,

Malam yace da kata bana son wani zan ce kawai ki faɗa min in da yarin yar na taje,

Mama tace shike nan malam zan faɗa ma malam amma sai kayi min alkawarin ba za ka tavda han kalin ka ba har ciwo ka ya ta shi,

Malam yace naji faɗa min, mama gyara Muryar ta bashi labarin duk abin da ya faru tana zuba da hawaye ,

Malam tari ya sar ƙa fe da shi , mama ta duka salati tana cewa malam malam sannu malam ,

nafisa ta kwalla wa nafisa kira da sauri nafisa ta fito ganin halin da malam ya shiga cikin ƙan kanin lokacin hawaye ya cika ida mun ta ,

Mama tace nafi ba tsaya kallo zaki yi ba maza jeki ki ɗebo  ruwa ki kawo ana wa malam  , da sauri nafisa ta je ta ɗe bo ruwa a kofi ta kawo aka samu malam ya sha , suka jin gina shi da jikin bango ya na sau ƙe nun fashi da num fashi ,

Malam be ce komai ba yayi shiru ,  mama da nafisa suka samu ya sha maganin ya koma ɗakin shi ya kwanta nan da nan bacci ya ɗau ke shi

°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Not edited

Vote and comment share to your love ones

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now