page 70

228 12 1
                                    

Page 70

Ignore the typing error

Happy reading


Misalin ƙarfe takwas na safiyar ranar, duka ahalin na zaune a falon gidan ana karya wa cikin tsanaki,

Kama da ƙana nun yaran su AYANA ne, da manyan su A'ishah, yaya Sa'a, me ƙo sai tare da mama tare da malam,

Wayar malam ce ta fara ringin hakan yasa kowa ya natsu yayi shiru dumin bawa malam damar ɗaukar kiran,

Malam ɗauka yayi ya ƙara wayar a kunnen shi tare da yin cikakkiyar sallama,

Daddy ganin kwana biyu kenan da ɗauke lion yasa ya yanke shawarar sanar da malam  dun a tunanin shi suma suna da hakƙin sanin abin da yake faruwa

Amsa sallamar malam yayi suka gaisa cikin girmama juna sa kowannen su yake nuna wa ɗayan shi,

Daddy ya tambayi lafiyar mutanen gidan malam ya amsa mai da alhamdulillah kowa yana cikin ƙoshin lafiya,

Daddy yace to masha allah ,sannan ya fara gaya mai dalilin da ya kawo kiran wayan,

Sai sa ya gama labarta mai komai , kafin malam ya cire tabarau dake fuskar shi , yana amba ton innalillahi wa'in na ilaihir raju'un,

Hakan yasa hankalin kowa tashi jin furucin malam , in ka cire yaran da basu san ciwon kan su ba , kowa da ke cikin falon hankalin shi ya dawo kan malam ,

Suna jira malam ya ƙidar da wayar dan su ji dalilin da yasa ya shiga irin wannan yanayin cikin daƙiƙu ƙalilan,

Malam ya cigaba da cewa , yan zu kana nufin tun ranar ba a samu labarin in da yake ba ko gano wa inda suka aika ta wannan al'amarin

Ta can ɓangaren daddy yace , har yanzu dai abin da muke bincika kawa kenan allah ya gafar ta malam ,

shiyisa na kira na sanar da kai dumin a iyalin shi suma suna da hakkin sani ,

Ko sa taya shi da addua dumin allah ya kuɓuto dashi daga hannun wa'in nan azzaluman,

Malam yace kayi gaskiya , allah ya bayyana shi, insha allah daga nan muma zamu cigaba da addua har sai allah ya bai yana mana shi,

Daga haka daddy yawa malam godiya tare da yin sallama,

Malam kashe wayar yayi ya aje yana cewa allah shi kyauta, mama ce ta kasa haƙuru , ta tam bayi malam da malam nace dai lafiya,

Malam yace ke dai bari , uhmm nafisa ya kira nafisa , ta amsa da na am , yace kwashe yaran nan ki shiga da su ,

Tattara su tayi suka shiga cikin ɗaki, malam yayi haka ne saboda bai san wani irin halin ayan zai shiga ba in yaji wannan labarin ,

duk da cewa bashi da wayau , amma lafiyar shi tafi gaban komai , baza a so wani abu ya sake faruwa ba bayan wan da ya gama ji a yanzu ,

Gyaran murya malam yayi sannan yace ku saurara kuji ni nan, hankalin kowa ya tattara ya dawo kan malam dan saurarar abin da malam zai gaya mai mahim man ci haka da har yasa aka shiga da yara ciki,

Malam cigaba da magana yayi , yanzun nan da mai girma shugaban ƙasa muka gama waya, wato mahaifin aliyu , ya kira ni yana sanar da ni labari mara daɗi,

Akan mummunan abin da ya faru shekaran jiya da aliyu , ana furta sunan aliyu ƙirjin aishah ya bada dum har sai da ta dafe shi ,

Malam yace , gurin koma war su gida wato abuja  shida ɗan uwan shi da suka zo nan, bisa ƙaddara ta uban giji mutanen da ba asan ko su waye ba su harbi ɗan uwan nashi , shi kuma aliyun sun ɗauke shi sun shiga daji da shi,

A halin yanzu dai ba labari akan ɓatan aliyu ko sanin wa'in da suka ɗauke shi,

Sai dai mu taya shi da addua allah ya kuɓu to dashi daga hannun wa'in nan azzaluman mutanen,,, aishah miƙe wa tayi sai kuma jiri ya ɗebe ta faɗi a sume..

Nan take falon suka ɗauki salati da innalillahi wa'inna ilaihir raju'un ,

Aisha suka zagaye , mama tace mai kuke jira , naja atu , jeki kawo ruwa,

Da sauri anty naja taje ta ɗebo ruwa ta miƙa wa mai ƙo sai da ta ɗaura aishah saman ƙafar ta,

Amsar ruwan mai ƙo sai tayi ta tsiyaya a tafin hannun ta sannan tayi bissmillah ta shafa saman fuskar aishah,

Amma bata farka ba , sai da ta shafa mata ruwan har so uku , kafin ta farfaɗo, ta na sauƙe nau yayyen nun fashi,

Kallon fuskar kowa tayi da ke cikin damuwa da aihinin abun da ya faru, kana duk maganganun malam suka fara dawo mata kaf ta tuna,

Sai ta fashe da wani mugun kuka mai raɓa zuciyar mai sauraro,

Mai ƙo sai ce tace haba ƴar nan addua ya kamata ace kin yi , ba kuka ba , me kike tunanin zai faru in , yaaran nan suka zo suka iske halin da kike ciki,

Dafe bakin ta aishah tayi dumin hana wani sabon kukan da ya tawo mata fita, sannan ta fara sambato tana cewa duk ita raja komai,

Da ranan nan bata wulaƙan ta lion ba da mugayen furucin data gaggaya mai , ƙila da duk haka bata faru ba,

Dan kada , su ayaan suji , malam yasa su anty sa"a da su shiga da aishah cikin wani ɗaki daban,

Haka suka kamata suka shiga da ita cikin ɗakin , sai kuka take,

Can ɓangare daddy kuwa har rame wa yayi saboda damuwar ɓatan lion , ko abin kirki baya samun damar ci , ga riƙon mulƙin ƙasa guda, shi sai yaji ma duk mulƙin ya fitar mai a rai,

Shi tsoron shi ɗaya ma kada duniya ta gano abun da yake faruwa, yayi ƙoƙarin hana kowa sani a wannan lokacin , to nan gaba fa in asiri yazo tuno jamana , gashi ba a ga lion , za a ce ya gasa na zama uba balan shugaba,

Kusan wanin ranar haka gidan suka wuni ba kwanciyar hankali , saboda halin da aisha ta shiga tun bayan samun labarin ɓatan lion da tayi, gaba ɗaya ta ɗaga wa kowa hankali,

Yara yaran ma wayau aka musu aka fita da su yawo dumin kada su gano halin da ake ciki,

In ka cire anty sa'a mama mai ƙosai da malam ba mai lallashin aishah ,

Dan nafisa da anty mardiya da anty naja duk haushin ta suke ji, tun da suka ji kalar wula ƙan cin da ta rinƙa yiwa lion ,

Wannan kenen

Ku tara a shafi na gaba da yat dar allah.....

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now