part 10

249 16 1
                                    

✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"

Page 46-50

Ta cigaba da shirya wa, har ta gama suka fito suka wa mama sallama, mama ta musu a dawo lafiya,
Ƙofar gida suka fita inda malam ke zaune tare da ɗaliban shi,
Malam suka gaisar ya basu kuɗin mota , suka mai sallama, Nuhu ba ƙaramin haushi yaji ba na ganin A'ishah tare da nafisah yayi ba,

Yaso ya gana da masoyi yar shi amma ganin dawa take tare dole ya haƙora, ku kuma aci mai mutun ci,

A'ishah cewa tayi su fara duba wa gurin da take haɗu wa da lion, in bai fito ba sai su bishi gida, gun suka nufa, nafisah na jin daɗin wayewar da A'ishah ta fara.

Ai ko suna isa gurin suka tadda motar lion a fake a gurin sautin kiɗa na tashi daga ciki , alamar da mutum kenan a cikin,

Hamdala A'ishah tayi a cikin zuciyar ta, ta kwan kwasa gilas ɗin motar, kamar jira yake dama yaji an buga lion ya buɗe, gilas ɗin batare da ya kalle ta ba yace get in, be lura Bama tare take da nafisah za gaya wa sukai suka shiga,

Sai da suka shiga ya ankare da nafisah da ta zauna a kujerar baya, gaishe shi sukai ya amsa da lafiya kamar kullum, bai ƙara cewa komai ba ya tada motar suka fita a unguwar,

Sun fara tafiya ya ɗan fara yiwa nafi magana, amma Sam yagi kallon Inda A'ishah ke zaune balan tana su haɗa ido,

Duk da cewa shima ba ƙaramin hukunta kanshi yake da haram tawa kan shi kallon ta da yayi,

Ita ko A'ishah baƙaramin shiga da muwa da ƙin kula ta da lion yayi ba tayi

A'ishah ko ta sa baki a firar lion baya tanka mata, sai ma hade rai Daya ke yi , ya wani tur bu ne fuska yana kallon gefe,

Har suka ƙara so makarantar , nafi ce ta fara fita tawa lion godiya ,

A'ishah kallon lion tayi bayan nafisah ta fita, tace yah Aliyu, wai mai na maka ne kake share Ni,

Wani kallo lion ya wurga mata , har sai da ta sun ƙuyar da kanta ƙasa,

Kamar bazai magana sai koma, yace, ya baki tafi tare da ƙolan naki ba kuma,

Anan ta gano mai yisa yake fushi, gaya mai dalilin da yasa nuhu bai biyu ta ba tayi,

Hakan da tace ne yasa ke ƙolar da lion, kenen ma ba Dan wani dalili ba da share shi, zatai ta bi wan can ƙolon,

Be sake cewa komai ba har ta mai sallama ta fita a motar, lion ya ja motar da mugun gudu ya bar makarantar,

Wani ruɗani A'ishah ta sake shiga, ta rasa dalilin fushin lion haka, bata son ya zatai ba,

Ita a matsayin yaya ta ɗauki she bayan haka babu komai, amma bata son ko meye acikin zuciyar shi lion ɗin ba,

Ga Nuhu masoyin ta wanda ta rasa dalilin da yasa bata so su haɗu ko ma a mata maganar shi,

Sannan dole ta nemi hanyar da zata fara iya ƙin tsallake Umar nin lion,

Dole tayi dogon nazari don neman mafita, in ta kama ta nemi shawara gurin wani to zatai hakan,

Da irin wa'in nan tunanin nikan ta ƙara sa lecture hall, lokaci na cika malamin da zai karan tar da su ya shigo,

Ya fara musu karatu, a fannin Educational psychology, baya Ni yake musu, cikin kware wa da fasiha ta yar da zasu fahim ta cikin sauki,

Amma da alama gaba ɗaya hankalin A'ishah baya tare da malamin, ba kowa ne zai fahimci haka ba ganin yadda A'ishah ta zuba wa malamin ido ko ƙif ta wa bata yi,

A zahirin gaskiya gangan jikin A'ishah ne ke tare da malamin, amma hankalin ta da tunanin ta gaba ɗaya ya tattara ya tafi wata duniyar tunani daban,

Tambaya ya jeho wa ɗaliban amma ba wanda ya amsa posting A'ishah yayi, yace ta tashi ta bada amsa,

Amma A'ishah ko gezau ba tai ba, hakan ba ƙaramin ƙona ran malamin yayi ba yana mata magana tayi banza da shi.

Wata yarinya dake zaune kusa da ita ne ya ɗan jijjiga ta, ta kira sunan ta,

A firgice A'ishah ta mige, take ta dawo cikin hankalin ta, ganin yanda gaba ɗaya kowa dake cikin hall ɗin ita yake kallo hatta lecturer, idon shi na kanta.

Sun kuƴar da kanta tayi cikin jin kunya, kamar ƙasa ta buɗe ta nutse, dan kunya , dan ma Allah yasa tasa nikap da tasan kun yar da zata ji yau sai ta fi haka,

Tana cikin wannan yanayin ne Muryar malamin ta doki dodon kunne ta cikin, kakkausar murya ya fara magana, dama yasan sunan ta, A'ishah Are You out of your sense, I'm lecturing but you're busy doing he'll of something,

Shiru A'ishah tayi ta kasa cewa komai, hakan data yi ya ƙara ƙolar da malamin , yace pack your thing I live out of this hall,

Jakar ta A'ishah ta ɗauka, ta fita a cikin lecture hall ɗin kanta a duƙe bata so ta haɗa ido da kowa.

Ko da ta fita can wani guri ta samu nesa da lecture hall ɗin ta samu guri ta zauna, har tana sauke wani ajiyar zuciya,

Bata yi tunanin wani irin hukunci lecturer zai yanke mata ba, sai ma cigaba da tunanin lion da tayi, in ta tuno fuskar shi har wani lum she , ido take tana buɗe, wa

Ayan zu ba wani abu da take da mura ɗin gani illa fuskar lion, rashin ganin shi kan iya jefa ta cikin wani mugun yanayi,

Dafe kanta tayi tana cewa oh Ni A'ishah wannan wacce irin masifa ce , Allah ka kawo min mafita,

Jin Muryar taya a kanta ana cewa, abbu ɗaya ne shine kin faɗa tabkin so kin kasa gane wa,

Nafisah, ke cewa tayi, kusa da A'ishah ta kamo hannu ta , ta riƙe, ta cigaba da magana, A'ishah ba wani abu bane ke damun ki ba illa.........................

To fans ban dai mutu ba har yanzu, amma ina neman addu'ar ku Allah ya bani lafiya

Don't forget to vote and comment.

y͜͡a͜͡r͜͡ m͜͡u͜͡t͜͡a͜͡n͜͡ z͜͡a͜͡z͜͡z͜͡a͜͡u͜͡
🆂︎🆄︎🅻︎🅴︎🅹︎🅰︎

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now