✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*
بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"
Page 41-45.
Lion, da sauri ta ansa kiran, ta kara wayar a kunnen ta, bakin ta ɗauke da sallama,
Can ɓangaren lion amsa sallamar yayi bayan haka bai ƙara cewa komai ba ,
Sunyi shiru suna sauraran nunfashin juna, daga baya ne A'ishah tayi magana, tace ya kake,
Lion yace lafiya kefa, A'ishah itama , nima haka,
Kamar jira lion yake, ya fara jero mata tambayoyi ita kuma A'ishah tana amsa mai,
Sai da taga alamun ya gama tambayoyin nashi , kafin, tace,
Ihmm kana ji ba gobe ba sai ka taso ka kaini makaranta ba, wanda yake raka Ni bakin hanya, ya dawo, tana gama gayar haka tayi shiru,
Har wajen minti biyu bata ji lion ya bata amsa ba, sai ta fara cewa hello hello kana jina,
Cire wayar tayi a kunnen ta, ta duba taga ashe ya datse kiran tin sanda ta fara mai magana,
To me kenan ko yayi fushi ne, ai bata ga abin jin haushi a wannan maganar ba, duk a cikin zuciyar ta take wannan zancen,
Yanke shawarar sake kiran shi tayi, amma har sau uku tana kira bai ɗauka ba, daga ƙarshe ma taji number switch up,
Danƙari, shine abinda tace, gyara kwanciyar tayi, tayi addu'a bacci, tunani ta rinƙa yi akan yanda zatai da wa'innan mazan goda biyu in Allah ya kaimu gobe,
Har bacci ɓarawo ya sace ta,
Acan ɓangaren lion kuwa tun bayan da A'ishah ta fara gaya mai wannan maganar yaji duk ranshi ya ɓaci, kashe wayar yayi dan yasan amsar da zai bata zata iya ,
Ɓata mata rai, kuma ta rasa wanda zata zaɓa akan shi sai wancen mummunan ƙolan,
Cewa yayi cikin zuciyar shi, ko bayan ya samu abin da yake so bazai barta tare da Nuhu, ba,
Yanzu ma zai san hanyar da zai bi , ya raba sune, ko ta halin ƙaƙanikayi, kai dole ma yayi wani, abu,
Juya wa yayi ya naushi filo yana cewa i have to do something, ganin yana shirin shiga cikin damuwa ne, ya tashi ya haɗa shisher ya fara banka wa cikin shi,
Saboda ita kwana biyu baije club ba , dan ya sani in yaje ma bazai samu ya dawo da wuri ba , har ma ya tashi da wuri ya kai ta makaranta, amma da ba ranar da ya taɓa fashin zuwa club,
Ƴan matan da yake ɗan latsa wa ma kwana biyu baya kula su, saboda yana ganin, in ya ci gala ba akan A'ishah duk zai fanshe komai,
Amma da alama shirin shi yana so ya warga je, to bazai yuwu ba, kota ƙarfe sai ya kasance da A'ishah, da ya shirya ayi komai cikin yadda ta, amma yanzu komai yayi ita taja,
Da alama shisher da yake zuƙa ne take gaya mai haka, to a haka a gurin da yake sha bacci ya ɗauke, shi kiran sallar farko , yau ya tashi, duk jikin shi yayi tsami sakamakon bacci da yayi akan kushin,
Wanka yaje yayi tare da ɗauro alwala ya shafa mai ya zura jallabiya,
Yau kawai ya tsinci kansa da son zuwa Masallaci, batare da ya ƙara tunanin komai ba ya fita,
Masallacin unguwar shine na kusa , da gidan su A'ishah kuma malam ne limamin masallacin,
Bin sahu yayi akai sallah da shi, bayan an gidar, yaga mutane basu tashi ba kamar yadda ya saba, da ya ƙidar da salla yake tashi,
Samun kanshi shima yayi da zama a gurin ya na addu'a, har aka fara watse wa a cikin masallacin shi ma ya taso ya, fito, mutane sai mami ki suke, amma sunyi shiru ba mai cewa komai,
Abin da lion Bai sani ba, dad ɗin shi na bayan shi har suka fito daga cikin masallacin,
Sun ɗan yi tafiya, lion yaji kamar ana binshi a baya, juyo War da zai yi yaga dad ɗin shi,
Cikin mamaki yace dad, yaushe, ka dawo, da cewa yayi jiya da tsakar dare my son, rungume shi lion yayi yace welcome dad, hope ka dawo lafiya lau son , kama hannun lion dad yayi har suka ƙara sa gida,
Kafin dad ya saki hannun shi yace son sai mun haɗu da safe lion cewa to dad kafin ya wuce part ɗin shi,
Shima dad part ɗin shi ya nufa, yana jin daɗin sauyin da ya gani atattare da ɗan nashi,
Lion Bai koma bacci ba har gurin takwas na safiya, kafin ya shirya cikin ƙananan kaya ya dauki key ɗin motar shi, ya fita a gidan,
A daidai inda suke haɗu da A'ishah ya faka motar shi, ya zuba wa hanya ido yana jiran yaga sawa zata fito,
In love tayi kuskure fito wa tare da ƙolon nan ba abin da zai sa bai sa an sassaran mai shi ba,
★★★★★************★★★★★
A'ishah kamar kullum haka ma yau ta tashi tayi aikin ta, wurin ƙarfe bakwai na safiya A'ishah taji sallamar nafisah, ta shigo gidan, sannu suka cewa juna, nafisah ta shiga ɗakin mama,
Bayan nafisah sun gaisa da mama, ta gaya mata aikan da yah sa'a ta mata ,
Kafin ta fito, ta tadda A'ishah ta shiga wanka, ɗa kin su ta shiga ta zauna tana jiran A'ishah ta gama su tafi makaranta,
Shaf-shaf A'ishah tayi wanka ta fito, ta shiga ɗaki, ta fara shirya wa, ta kalli nafisah ta ce sis kin san ba ƙaramin daɗin zuwan ki naji ba yau ɗin nan,
Nafisah cewa tayi daɗin zuwa na name kuma kika ji, A'ishah cewa tayi hmm kedai Bari,
Ina ga jiya Nuhu ya dawo, kin san dama shi yake raka Ni bakin ti-ti, to shine jiya nake cewa Aliyu ba sai yazo kaini makaranta ba, amma kafin in gama magana ya kashe, waya
Nasan yanzu in nuhu ya ganki bazai yi kuskuren biyu Ni ba, nafisah cewa tayi ai keki jiyo tun wuri kisan inda zaki cilla wawa, dama baku dace ba amma kika lige, yanzu tunda kin gane kya san yadda za kiyi maganin garan,
A'ishah bata ce komai ba ta.......
y͜͡a͜͡r͜͡ m͜͡u͜͡t͜͡a͜͡n͜͡ z͜͡a͜͡z͜͡z͜͡a͜͡u͜͡
🆂︎🆄︎🅻︎🅴︎🅹︎🅰︎
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...