part 16

227 8 0
                                    

✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨

While you're reading this page listen to this song up there☝️

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"

Page 76-80

Lion bayan ya fita a part ɗin dadyn!! shi motar shi ƙirar benx ya fito da ita ya tada yabar gidan..

Sai da ya samu gurin a inda su ka saba haɗu wa da A'ishah ya faka motar ya dauƙi wayar shi ya danna wa A'ishah kira..

Su A'ishah bayan sun gama aikin gidan sun ci abinci wanka sukai suna cikin shirya wa A'ishah taji wayar ta na ringing ,

Janyo wayar tayi ganin wanda ke kira yasa ta saki wani ƙayataccen murmushi..

Ɗauƙan kiran tayi ta kara wayar a kunnen tare da furta cikakkiyar sallama haɗe da gaishe da lion cikin siririyar Muryar ta mai daɗin sauraro ,

Lion amsa sallama yayi yace lafiya lau baby na da fatan kin tashi lafiya?, kin ci abin ci kuwa? shin akwai abin da ke damun ki ko kina buƙatar wani abu ne?.

A'ishah murmushi haɗe da wani farin ciki ganin yacce lion yake furta irin damuwar da yayi akan ta ,

aje man da ke hannun ta tayi ta nemi guri ta zauna tana mai lum she kyawawan idanuwan ta tana buɗe su cikin wani tsanani ƙauna ta lion dake ratsa ko wani sassa na jikin ta,

Ɗaƙar A'ishah buɗe bakin ta tace yah Aliyu, lion cewa yayi na'am baby na,

A'ishah ta cigaba da cewa na tashi lafiya , sannannn ba abin da ke damunaaah bana buƙatar komai Alhamdulilla!!

Lion daga can bangaren ajiyar zuciya ya sauke yace har naji wani sanyi a cikin zuciya ta,

ki sani bazan iya ɗauka a cikin zuciya ta wani abu naga ya faru dake ba, A'ishah cewa tayi cikin jin daɗin kalaman shi,

hmm yah aliyu kenan, lion cewa yayi hmm menene baby na yanzu dai ina jiran ki a gurin da muka saba haɗu wa kiyi sauri ki fito dan ida nuwan na yin war sanya ki a cikin su,

A'ishah cewa tayi to gamu nan fitowa yah Aliyu , lion ya ce to sai kin fito baby na sannan dan Allah zan nema wata alfarma a gurin ki,

A'ishah cewa tayi to , ina jin ka yah Aliyu nah, ɗan murmushi Aliyu yayi yace ina so kafin ki iso gurin ki kula min da kanki , kada ki bari ko ƙuɗa ya taɓa min ke,

Gyalgyalewa da daria A'ishah tayi har nafi sai da ta juyo ta kalle ta murmushi kawai tayi ta cigaba da abin da take yi,

A'ishah cewa tayi yanzu yah Aliyu abin da kake bukata kenan , lion cewa yayi eh in kikai min shi zuciya ta zata samu salama,

A'ishah cewa tayi cikin wani irin salo da bata san ta iya shiba tace to ka ɗauka an gama ɗannn samari tana cewa haka ta kashe wayar dan in bata kashe ba lion bazai kyale ta , ta gama shirin taba,

ci gaba da shirya wa tayi cikin sauri dan har nafi ta gama shirin ta ...

Lion Aisha na katse kiran, ya ɗaura wayar akan ƙirjin shi ya lumshe ido yana murmushi shi kadai kamar wani gaɓo,

wai shine har ya tsaya yana zubu zance haka shi da yake ganin in mutum ya cika yawan magana to da alama ya fara zare wa, zan tukan soyayya ko ada shirme da ɓata lokaci ya ɗauke shi.

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now