page 21

205 9 1
                                    

✨✨✨✨✨✨
Mai sona
✨✨✨✨✨✨

*𝐔𝐧𝐢𝐭𝐲 𝐰𝐫𝐢𝐭𝐞𝐫'𝐬 𝐚𝐬𝐬𝐨𝐜𝐢𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧*
.𝖒𝖔𝖙𝖙𝖔.
{ 𝒘𝒆'𝒓𝒆 𝒖𝒏𝒊𝒕𝒚 𝒘𝒓𝒊𝒕𝒆𝒓𝒔, 𝒎𝐢𝒔𝒔𝒊𝒐𝒏 𝒕𝒐 𝒎𝒐𝒕𝒊𝒗𝒂𝒕𝒆 𝒂𝒏𝒅 𝒆𝒏𝒕𝒂𝒓𝒕𝐚𝐢𝐧 𝒐𝒖𝒓 𝒓𝒆𝒂𝒅𝒆𝒓𝒔}

𝑃𝑒𝑛 𝑜𝑓
R̶o̶s̶e̶ f̶l̶o̶w̶e̶r̶

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
h̶e̶r̶w̶w̶e̶r̶ j̶i̶d̶d̶e̶r̶h̶

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

Dan Allah kuyi following ɗina a social media handle ɗina kamar haka , yin haka shine nuna Godiyar ku a gurina, musamman anan Wattpad..

*Facebook* jiddorh ofeecial

*Tiktok* @jiddorhofeecial

*Instagram* jiddorhofeecial

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيم

Page 101-105

*{Author POV}*

Ranar wata asabar, misalin ƙarfe shabiyu na rana, zaune A'ishah take akan ta barmar dake shinfiɗe, a cikin gidan na "ya" mardiya, gaban ta tarin littattafai ne a zube tana dudduba wa...

Lion bai dade da wuce wa ba yazo sun sha fira tun safiya kafin ya mata sallama ya wuce wai yana da wani uzuri daya taso mai,

ganin bata da abin yi ne yasa ta ɗauko littafan ta tana duba wa.

Sallama taji daga waje ana doka wa, ta amsa, ta ƙara da tace waye, duk da ta gane Muryar ko waye , daga ji ba sai an ƙara ba Nuhu ne ke sallamar,

daga waje Nuhu dake tsaye ya kafa uwar hula duk ta mai yawa ya bata amsa da nine Nuhu,

Tsaki A'ishah taja cikin zuciyar tace ko uban me ya kawo shi gidan oho, a fili tace to yayi to ga ninan,

tashi tayi ta shiga cikin ɗauki, ta dauko hijab ɗin ta tasa ta nufi hanyar waje, da fitar taja ta tsaya nesa kaɗan da inda Nuhu ke tsaye, tana ɗaɗɗaure fuskar ta ,

Nuhu cewa yayi masoyiya ina wuni , harara A'ishah ta wurga mai ta amsa da lafiya akwai wata matsala ne,

Ƙirƙiro kuka Nuhu yayi, yana cewa inalillahi wa'inna ilaihir'raju'un rashi mukai, babban rashi mukai A'ishatu ,

Gaban A'ishah ne ya faɗi dumm tace kai dalla tsaya ka gaya min wani irin rashi kuma ka fara shaya-shaye ne ba wanda ya sani ,

share guntun hawayen shi nuhu yayi yace, cikin yanayi aihini Allah yayi wa lawaii mijin mardiya cikawa , lawaii ya mutu, Allah Sarki mardiya shike nan ta dawo bazawara ,

salati A'ishah tayi ta sanar wa Ubangiji , hawaye ya cika idanu wan ta bata saurari Nuhu ba ta shiga cikin gidan tana sake sallame wa,

Ke duniya ina zaki damu yau dai gashi an wayi gari ba lawaii, kuka A'ishah taci ta ƙoshi ta lallashe kanta ,

ta tashi ta kimtsa gidan, nan da nan labari ya isar wa yan uwa da abokan arziki tare da maƙota , aka fara zuwa taya jimamin rashi.

Zuwa wani lokaci su mama suka dawo rike da "ya" mardiya, Allah Sarki baiwar Allah duk ta shiga cikin wani yanayi,

a rirriƙe aka shigo da ita kukan ma ya gagare ta hawaye kawai ke zuba a saman fuskar ta, dakin ta aka shiga da ita ,

Yan uwa suka shiga bata haƙori tare da nasiha cewa duk me rai mamaci ne, kamar yacce lawaii ya tafi yau haka koma ma watarana za a wayi gari babu shi...

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now