Page 54
( Yanzu komai ya canza , sai kun yi comment da like zaku ga posting, amma in bakwa so kuji yan da wannan yaki zai kasance to, duk wanda ya karanta littattafin batare da yayi comments ko like ba shida Ubangiji )"Nigeria Abuja government house, Allhaji Mohammed taha , zaɓaɓɓen kuma sanannen shugaban kasar Nigeria , na tsawon shekaru biyu da suka shuɗe,
Zaune yake saman wata ƙerarriyar kuma haɗaddiyar kojera a cikin ƙaya taccen falon shi na musamman da ke nan cikin villa Abuja, gaban shi wani table ne dauke da kayan motsa baki, da tarin ta kardu ne a gefe guda yana duba ɗaya bayan ɗaya yana sa , hannu.
Gefen shi Saman kojera mai cin mutum uku accounter general be zaune yana jiran ya ji dalilin da yasa Mister president ya mai wannan kiran ganga wa,
Sai da ya gama duba file ɗin dake hannu shi yayi signing, sannan ya aje a gefe , sannan ya dawo da hankalin kan accounter general , ya ce , me muku ke jira har yau talatin ga wata baku biya ma aika ta albashin su , ba bayan tun wata na ishirin nayi approving,
Accounter general buɗe baki yayi zai yi magana, Mister president ya ɗaga mai hannu yace daka ta,
kai Musulmi ne nasan kasan hadisin da Allah ya umarce mu da mu biya ma'aikatan mu hakkin su tun kafin gumin su ya bushe,
Al'ummar ƙasar nan sun yar da dani sun zaɓe Ni, Ni kuma zabi na ɗaura ku akan matsayin nan dumin a ganina za kuyi adalci, amma ina a kullum matsala ake samu,
Mutane na ganin lefi a zahiri, ba ɗinin haka kuwa ba haka bane, yanzu umarni ne daga nan zuwa gobe ku tabbatar an biya ko wani ma aika ci hakkin shi, za ka iya tashi ka tafi,
Buɗe ƙofar falon akai aka shigo, account general ya tashi ya fita ran shi a ɓace,
Wannan da ya shigo ɗin ne yazo ya zauna a ƙasa , yana cewa you're Excellency ya iso baƙon naka,
Bashi umarnin yayi da aba shi izinin shigo wa, tashi PA ɗin yayi ya fita ya bawa baƙon damar shiga,
Yana shiga gai suwa ya fara miƙa wa mai girma shugaban kasa , kafin ya bashi izinin zama,
Bayan mutumin ya zauna shugaban kasa ya buɗe baki ya fara magana kamar haka, ina fata a wannan karon ka zo min da labari mai daɗi,
Mutumin ɗan jan nunfashi yayi sannan yace , eh kusan haka you're Excellency, a iya shekaru biyun nan da muka kwashe muna bin ciken in da yallaɓai yake, sai wannan karon muka samu damar gano ƙasar da yake in da yake zaune a halin yanzu,
Miƙa mai wasu file yayi ya ƙara da cewa, in kabi daki daki wa wa'in nan takar dun zaka samu ƙarin baya Ni,
Cike da murna mai girma shugaban kasa ya mai godiya, ya ƙara da cewa zuwa gobe zai ga saƙo , sannan sukai sallama ya wuce,
Tun bayan tafiyar lion ƙaro karatu , ya dena samu shi a waya ko ya kira bata shiga,
be damu ba har sai bayan shekara bayan ya zama shugaban kasar Nijeria rashin samun lion ya same shi sosai yayi bincike duk wasu kasa she said yasan lion zai iya zuwa amma bai same shi ba,
hakan yasa ya ɗauko ƙwararron masu bincike ya basu umurni shiƙa ƙasa shen duniya dumin bin ciko in da lion yake, ba a samu nasara ba sai yau da aka kawo mishi labari mai daɗi,
Yana cikin tunanin yadda zai ɓullo wa ' al amarin a tura ƙofar aka shigo, ɗaga ido shi yayi don ganin ko waye ya shigo,
Ba kowa bane face Hajiya asabe matar shi kuma first lady ta Nigeria, shigo wa tayi falon ɗau ke sa kwar kwasa cikin kayan bacci, sai ƙam shi turare take,
Mai da kan shi yayi ƙasa ya cigaba da duba takardar da yake duba wa, tare da mamakin halin Hajiya asabe da tunanin ranar da zata girma, ita bata duba cewa tsufa ya riga da ya fara nuna mata duk abin da take ya kamata ace ta bar wa yara,
Zuwa tayi ta zauna gefen shi tana cewa my dear Excellency, har yanzu aikin bai ƙare ba kenan , ya kamata ka dun ƙa samun lokaci kana huta wa, in kayi a office in ƙa dawo gida nima sai ka bani lokacin ka,
Shi dai bai tan ka mata ba ya cigaba da abin da yake yi, idon ta ne yakai kan file ɗin da yake duba wa taga sunan lion a Kai,
Da sauri ta zabura ta miƙe tana dafe kirjin ta, kallon ta dady yayi yace Hajiya asabe lafiya naga kin tashi a zabure haka,
Cewa tayi yanzu Alhaji har yanzu baka cire wannan yaron a cikin zuciyar ka ba, ka damu ka ɗaƙa hankalin ka shi yana can wata duniyar yana more rayuwar shi bai damu da kai ba kai kana nan ka sawa kan ka dariya,
Cikin tsawa yace dakata Hajiya asabe dama akan maganar nan kika wani zabura kamar wacce miciji ya sara,
To maza ki wuce in kin san ɗaga min hankali ne ya kawo ki guri na, tsaki Hajiya asabe tayi ta fita a fusace daga cikin falon zuciyar ta na tafar fasa,
Ƙafa ɗady yayi, ya tashi ya kwashe takar dun a gurin musamman takar Dar binciken Aliyu, a gurin mai tsaro ya aje su, dan yasan Hajiya asabe tabbas sai ta dawo ta bincike su ba ta tafi kenan ba, zata iya bin ko wace hanya dan ganin bai sake ganin Aliyu ba,
Ƙodirin ta kenan so take ya mutu ta ci gado bata duba ita ma da shekarun sun ja , kana naka ne Allah na nashi ba a san waye gawar fari ba,
A haka baccin da ya jima bai ɗauƙe shiba yau ya ɗauke shi,
Hajiya asabe sashin ta , ta wuce tana shiga ɗakin ta , ta fara wurgi da abu buwa , har sai da ta fasa abubuwa da yawa ka fin ta sai ta nunfashin ta , ta zauna, wayar ta dauko ta dan nawa ƙawar ta kira,
Ringin biyu ta ɗauka tana cewa you're Excellency in ce dai lafiya kika kira Ni da tsohon daren nan,
Hajiya asabe tace ina fa lafiya , can ɓangaren tace to meya faru, tace wannan shegen yaron Aliyu, duk boka yen da na bi dan his Excellency ya man ce da shi amma.....
Shi kuma lion kun ji irin tashi ƙaddarar,
Ya koke ganin lion zai kuɓu ta daga sharrin latifa..
Ku dai cigaba da kasan cewa tare da Ni a cikin wannan chakwalkwalin chakwakiyar,
Tare da danna min comments da like bazai ɗauke ku tsawon lokaci ba gurin following ɗina,
Sanna akwai sabbin littafi na guda biyu na fara ɗaya , nisan kiwo, na biyun mai suna SANYIN ADALCI is a Hausa mafian love story na tabbatar baku taɓa ji ko karan ta irin shiba ,
me kuke jira muyi maza ku aje shi a Library ko reading list ɗin ku , tun kafin na yanke shawara na maida shi na kuɗi madadin na kyauta,
A yanzu Ban fara sakin pages Amma bayan na gama mai sona da izinin Ubangiji zan fara saki muku shi ,
Ku daure ku duba king luxury zai shiga ranku...

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Storie d'amore* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...