*Page 72*
*Aslm na dawo nasan da yawa kun ji hau shi, amma kunsan komai yana faruwa ne da dalili, ga dai wannan bazan yi updating next chapter ba sai na samu comments da like guda talatin talatin in munyi ko zuwa gobe ne sanyi*
°Ignore the typing error°
" Government house Abuja, misalin ƙarfe biyar na yamma , malam zaune a cikin babban falon daddy, tare da shi kan shi daddyn suna fira , tare da sake tattauna wa akan abubuwan da ke faruwa,
Dan tun zuwan su , basu samu damar haduwa da daddy ba sai yanzu da Allah ya nufa , duk abubuwa ne suka taru suka ma daddy yawa , baya dawo wa gida sai cikin dare , watara rana ma a waje yake kwana,
Suna cikin magana pA wayar daddy da yake amfani da ita cikin gida tayi ringin, da kata wa suka yi , daddy ya ɗauƙi Kiran tare da yin sallama,
Magana aka yi daga can ɓangaren da aka yi kiran wayar, daddy yayi maza ya mike yana ambaton alhamdulillah, tare da cewa yanzu haka yana ina , aka bashi amsa yace gashi nan zuwa , yanzu yanzun nan,
Sannan aka kashe wayar, daddy cike da murna ya wa malam magana, yace alhamdulillah yanzu wayar da aka mun kyakkyawan labari aka sanar min cewa anga Aliyu,
Malam cewa alhamdulillah masha Allah yana ina kenan , daddy yace dan sandan da ya kira Ni yace yanzu haka yana asibiti, bari in je , zan sa azo kuma a dauke ku ,
Malam yace to-to-to Allah ya bashi lafiya, sallama suka yi sannan daddy ya wuce cike da murnar ganin lion da akayi,
Shima malam tashi yayi ya nufi ɓangaren da aka aje su , dan ya sanar dasu A'ishah wannan kyakkyawan labarin,
A falo malam ya tadda da su duka a Zazzau ne, ahyan da AYANA na kallon cartoon , ya shiga da sallama suka amsa mai a tare , ya nemi guri ya zauna,
Yana cewa torh sai da mu godema Allah, an ga Aliyu, nan da nan suka ɗauki murna tare da ambaton alhamdulillah, A'ishah ta tashi tana cewa to yana ina malam , mu taso muje ko ,
Malam yace a'a mama na , mahaifin shi yanzu ya samu labarin, shima ya tafi , yace zai tura azo a dauke mu, saboda haka ku tashi kuje ku shirya kafin Motar da zata ɗauke mu ta iso,
Tashi suka yi dukan su suka shiga cikin daƙi dumin yin yadda malam yace
****
Isar daddy da tawagar shi asibitin, daidai lokacin shima Ahmad ya iso , tare da jagoranci man yan likitocin asibitin da kuma wasu jami'an yan sanda suka raka su i zuwa ɗakin da aka kwantar da lion .
Suna zuwa suka shiga cikin ɗakin , suka samu likita a kan shi yana duba shi,
Likitan dakata yayi, sannan ya gaishe da dady , dady ya amsa sannan ya tambayi likitan , doctor ina fatan ba dai wata matsala ko ,
Likitan ya bawa dady amsa da, da izinin Ubangiji you're Excellency, rashin ishesh-shen ruwa ne da abin ci, munyi mai wasu allururi da zasu temaka main, inshallah Nan da wasu ƴan awannin zai iya farka wa,
Dady yace to masha Allah, ina fatan dai ba matsala in muka dauke shi dumin koma wa da shi asibitin shi,
Likitan yace eh You're Excellency in anyi haka ma ba wata matsala,
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Roman d'amour* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...
