page 63

250 23 10
                                    

Not editing

Nurses da sauri suka amshi AHYAN a  hannun lion suka shiga da shi , cikin  Emergency room da shi likitan da ke kan aiki doctor Anwar abokin lion shi ya zo zai duba AHYAN,

Tambayar lion ɗin yayi mai ya samu yaron da sauri A'ishah ta ce  ciwon zuciya ne da shi doctor , indai aka bari yayi kuka irin haka ke faruwa

Doctor Dan Allah ka ceci rayuwar ɗana , doctor Anwar be ce mata komai ba yayi mata murmushi ya shiga cikin Emergency room ɗin ,

Daddy da Alhaji joorda ne suka ƙara so asibitin, lion na ganin daddy shi  ya ƙara sa inda suke,

Daddy ya tambayi lion ya jikin yaron ince dai ba wata matsala, lion cikin yanayi na ƙun ci yace wai ciwon zuciya ne da ɗana ɗaddy , in wani abu ya same shi ban san me zan yiba,

Daddy cewa yayi ɗan ka kuma, lion yayi nodding kan shi, daddy ya sake cewa kana nufin wancan ita ce A'ishah ɗan dake cikin yanayin nan shine jikan nawa,

Lion yace eh sune daddy, daddy cewa yayi to yanzu ka natsu ka saurare Ni , kai namiji ne , be kamata ace ka ɗaga hankalin ka irin haka ba,

Godiya ya kamata kayi  wa da ya baiyana maka su, tare da yi ma ɗan ka addu'ar samun lafiya kai yanzu ba ƙaramin yaro bane fa,

Yanzu duba , daddy ya nuna A'ishah kalli halin da take ciki , kamata yayi ka kwantar mata da hankali dan duk halin da kake ciki ta Fika nin kin shiga cikin damuwa,

Yan zu kaje ka tau shi zuciyar ta,lion cewa yayi to ɗaddy , sannan ya nufi gurin A'ishah,

A'ishah sai kai da kawowa take a bakin Emergency room ɗin tana addu'ar Allah yasa ba abin da zai samu AHYAN ɗin,

Buɗe baki lion yayi zai mata magana , A'ishah ta ɗaga mai hannu, sannan ta zauna kan kujerar dake gurin ta dungule han nayen ta tayi tagumi,

Shima lion ɗin shiru yayi be ce komai ba ya zauna gefe da ita yana kallon ta,

Shiko daddy samun wani guri sukai suka zauna, suna zama Alhaji joorda ya ce Ashe you're Excellency aliyu yana da mata,

Daddy cewa yayi eh , AM musu aure tun kafin ya tafi ƙarin karatu , samun matsala suka yi aka neme ta aka rasa tsawon shekara uku sai , sun jima suna neman ta sai yau suka haɗu, kuma san da ta tafi ta tafi ne da ciki,

Daddy ya ɓoye wa Alhaji joorda gaskiyar lamarin ne , dan ya ɗauki abun a matsayin sirri,

Alhaji joorda be daɗe ba yawa daddy sallama ya wuce tare da tunanin wannan al'amarin , shin yanzu me zai cewa ruky ta fahimta ,

yadda bata taɓa neman abu ta rasa ba in tasan lion Yana da mata har da ɗa zata iya kashe kan ta

Da tunani kala kala ya ƙara sa gida, yana shiga cikin gidan Hajiya Binta ta tare shi tana tambayar shi ya Alhaji ina dai fatan komai dai-dai

Samun guri Alhaji joorda yayi ya zauna sannan ya tambayi Hajiya Binta da ina ruky,

Itama Hajiya Binta zama gefen shi tayi tana cewa hmm ruky yanzun nan na gama lallashin ta sai kuka take akan abin da ya faru ɗasu wai ya ɓata mata damar neman auren ta da me girma shugaban ƙasa da Aliyu suka zo yi,

Alhaji joorda cewa yayi subhanallah yanzu ya take bari in he in duba ta ya yin ƙura zai tashi,

Hajiya Binta ta ce ai dama ka bari zuwa an jima dan yanzu na baro ta , ta samu bacci, koma wa Alhaji joorda yayi ya zauna, ya shiga duniyar tunani , irin halin da ruky zata shiga in taji wannan labarin,

Hajiya Binta cewa tayi a'a ya dai Alhaji lafiya naga kayi shiru, Alhaji joorda cewa yayi wallahi ina tunani akan wannan sabon al'amarin ne,

Hajiya Binta ta ce wanne kenan Alhaji, Alhaji joorda ya ce, mai girma shugaban kasa ya ɓoye min , Aliyu na da mata har da yaro san da naje neman haɗa auren Aliyu da ruky,

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now