part 18

217 11 2
                                    

✨✨✨✨✨✨
𝐌𝐀𝐈 𝐒𝐎 𝐍𝐀
✨✨✨✨✨✨

*𝐔𝐧𝐢𝐭𝐲 𝐰𝐫𝐢𝐭𝐞𝐫'𝐬 𝐚𝐬𝐬𝐨𝐜𝐢𝐚𝐭𝐢𝐨𝐧*
.𝖒𝖔𝖙𝖙𝖔.
{ 𝒘𝒆'𝒓𝒆 𝒖𝒏𝒊𝒕𝒚 𝒘𝒓𝒊𝒕𝒆𝒓𝒔, 𝒎𝐢𝒔𝒔𝒊𝒐𝒏 𝒕𝒐 𝒎𝒐𝒕𝒊𝒗𝒂𝒕𝒆 𝒂𝒏𝒅 𝒆𝒏𝒕𝒂𝒓𝒕𝐚𝐢𝐧 𝒐𝒖𝒓 𝒓𝒆𝒂𝒅𝒆𝒓𝒔}

𝑃𝑒𝑛 𝑜𝑓
R̶o̶s̶e̶ f̶l̶o̶w̶e̶r̶

Wʀɪᴛɪɴɢ ʙʏ✍️
Hiya Iqbal

*𝐍𝐚 𝐬𝐚𝐝𝐚𝐮 𝐤𝐚𝐫 𝐝𝐚 𝐥𝐢𝐭𝐭𝐚𝐟𝐢𝐧 𝐧𝐚𝐧 𝐠𝐚𝐛𝐚 𝐝𝐚𝐲𝐚 𝐠𝐚 𝐝𝐮𝐤 𝐰𝐚'𝐢𝐧𝐝𝐚 𝐬𝐮𝐤𝐞 𝐜𝐢𝐤𝐢𝐧 𝐰𝐚𝐧𝐢 𝐡𝐚𝐥𝐢 𝐚𝐤𝐚𝐧 𝐬𝐨*

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"

Page 86-90

" Lion sai ƙarfe ɗayan dare ya dawo a gajiya, yana shiga part ɗin shi ya kwanta akan sopa nan da nan bacci yayi awon gaba da shi a gurin,

" Aishah kiran sallar farko ta tashi duk jikin ta na ciwo , alwala taje ta dauro ta dawo ta shifiɗa dadduma ta tada sallah,

Bayan ta ƙiɗar da Sallah, wayar ta , ta janyo ta sake gwada kiran number lion Amma har ta gama ringing bai dauka ba,

Dafe zuciyar ta tayi jin wani ciwo da take mata, Allah ne kawai yasan halin da take ciki, daka daren jiya zuwa waye war garin yau,

Tun kan gari yayi haske ta fita tsakar gida ta fara aika ce aika ce , har zuwa ƙarfe bakwai na safe kafin ta gama komai ta dumama abin ci taci tayi wanka ta shirya ,.

Sai lokacin mama ta fito taga har A'ishah ta gama aikin komai,

Kwala kiran sunan ta tayi da A'ishah A'ishah, "A'ishah fito wa tayi sanye da blue ɗin hijabi hannun riƙe da jakar da take tafiya makaranta da ita,

Durƙusa wa tayi a gaban mama tace": ina kwana mama, mama ta amsa da lafiya lau kin tashi lafiya,

ta ƙara da cewa yau tun yanzu zaki wuce makarantar ne,

"A'ishah amsa wa tayi da a'a mama gidan su anti sa'a zan je gurin ya nafi akwai aikin makaranta da zamu ƙarasa tare da ita ,

Mama cewa tayi": oh to-to tashi ki shiga cikin ɗaki zaki ga wata leda ki dauƙo ki kaiwa yayar taku,

"Aishah cewa tayi ": to ta tashi ta shiga ɗakin mama ta ɗauko ledar ta fito ta yi mata sallama .

Bayan ta fita daga cikin gidan gaida malam tayi kamar kullum,ta mai sallama tayi gaba ,

"Nuhu ne ya biyo bayan ta yana cewa :" masoyiya yauda wuri zaki je makarantar kenan wani tuƙoƙin ɓacin raine ya turnuƙe zuciyar A'ishah amma ta juyo ta sauke idon ta akan mummunan fuskar
Nuhu ya kifa wata uwar hula akan shi wandon shi ƙafa ɗaya ya nan nade yana goge jajayan haƙoran shi da asuwaki inba hancin tane ya jiyo mata ba dai-dai ba dan wani wari-wari
hamami-hamami taji yana yi, share duk tunanin da take yi tayi ta kalle shi tace eh ina da abin yine shiyisa zan tafi da wuri ko akwai wata matsala ne,

Ta bashi amsa , duk da cewa bai ji dadin amsar da ta bashi ba murmushi yayi yace": ya kankanar zuciya ta nayi bala'in kewar ki kwana biyun nan daure wa kawai nake , rayuwa babu ke bata da amfani aduniyar

"A'ishah cewa tayi to yayi , ada in nuhu na mata kallar kalaman nan haƙa ramin daɗi suke mata ba, amma yanzu kallar Nuhu take amatsayin wawa sakarai,

Gaskiyar nafisa ne da take cewa ko kunyar kanshi baya ji ya dube ta ya dube shi wannan sai dai yazo a mai gadin gidan ta ,

duba fa duk da tasa niƙab ji yadda yake jiyo tashin tsamin da yake

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now