page 57

192 21 1
                                    


Page 57


" Juye-juye yake ta yi a kan gadon da yake kwance tare da dafe kan shi da yake ji yayi mai nauyi, sai da yaji ya kafa mai , sannan ya fara buɗe idon shi a hankali,

Ya sauke su tsaf akan daddy dake tsaye a kan shi yana jiran ya farka, cike da mamaki ya furta Daddy,

Daddy ya furta Yes my son ka tashi, sannan lion ya yin ƙura ya miƙe, da sauri ya rungume Daddy ya fara zub da hawaye,bubbuga bayan shi daddy yayi yana cewa you're a big man my son you're my lion

Ka bar kuka kai jarumi nane , komai zai wuce, lion sake rungume Daddy yayi yana cewa Nagode Dad daka kuɓutar dani daga hannun wancan azzaluman mutanen , dad Please ka tafi dani kar ka ban Ni anan nan gaba ƙaɗan in suka gane bana nan suka gano Ni kashe Ni zasu yi ,

Sannan ya haɗa hannun shi dana daddy yace dad please, daddy cewa yayi relax Aliyu haidar, a yanzu ba wan da zai iya cutar da kai , yanzu ka natsu , ka tashi kayi wanka, ka gyara kanka, kaci abin ci , zamuyi magana,

Ba dan yaso ba ya bari dady ya fita, gani yake kamar latifa zata zo ta mai da shi cikin ukubar da ya fito,

Bayan ya gama duk abin da dady ya umurce shi da yayi ya aske ƙasum bar da ya tara ya ci abinci, daddy ya dawo suka sake zama, sannan ya umurce shi da ya bashi labarin duk abin da ya faru tun bayan barin shi Nigeria,

Tir yan tir yan lion ya bashi labarin komai tun daga farko har ƙarshe,

Anan daddy ya gane da akwai kul lalliya a ƙasa, ɗan daga gani akwai sharrin asiri a cikin lamari, wai kamar shi ɗan shi na cikin shi za ayi wa wannan abu,

Amma har da lefin shi , in da tun farko bai san garta lion ya tsaya ya bashi tarbiyya, ƙila da bazai bi matan banza ba , har hakan ya faru,

Amma yanzu ma lokaci bai wuce ba , zai yi wa tuf kar hanci, sannan ya ce wa lion kayi haƙori my son komai me wuce wa ne, ada kaga soyayyar uba , amma yanzu zan sauke nauyin dake kan uba , akan ɗa, sannan ka manta da duk abin da ya faru a baya ka fuskanta gaba,

Kamun alƙawarin dena duk wani abu mara kyau da kake aika tawa a baya , kamin alƙawarin zama mutumin kirki, lion cewa yayi dadi duk wani abu da kace nayi a yanzu shi zan yi

Da yace good, haka, cikin sirri a daren ranar ba tare da barin ko wacce sheda ba dady ya ɗauke lion suka bar India

************

Masu tsaron gidan ko washe gari da suka dawo haiya cin su basu gane an shiga cikin gidan ba , har an fita da lion , har kokin su na naɗa tsaro suka ci-gaba da yi kamar ko da yaushe,

A gurguje

A can ƙasar Poland sai da su latifa suka kwashi tsawon kwanaki biyar a can kafin suka yi shirin dawowa , India

Bayan sauƙar su ita da Hajiya shukura aka zo aka ɗebe su zuwa gidan ta , tun daga shigan ta cikin falon gidan ta , abin ya bata mamaki na rashin gyaran da bata ga an wa gidan ba bayan umarni ne ta bawa lion ko tana nan ko bata nan ya tabbatar ya gyara gidan kullum so biyu,

Ɓera ɓera sunan da ta fara kira kenan dan ta ce ita a gaban ta ɓera ne ba lion ba,

Amma ta ji shiru bai fito ba bai amsa ba kamar yadda ya saba a ko da yaushe,

Fara duba ɗakunan da ke cikin gidan tayi amma ba lion ba alamun sa ,

Danna wani abu tayi nan da nan ma aika tan gidan suka haɗu a falon, ta zauna ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya , tana kar ka ɗaya,

Sai da ta kare musu kallo tsaff sannan ta ce , ina wan da nasa kuyi min gadin shi a cikin gidan nan,

Shiru sukai kowa na mamakin abin da take tambayar, har zuƙa tayi har sai da ta ciro bindigar dake jakar ta , ta har bi ɗaya daga cikin su a ƙafa, ya zube a ƙasa yana ihu,

San nan tace cikin tsawa ina kuka shiga me kuke har Aliyu ya bar gidan nan,

Ɗaya daga cikin su ne cikin tsaro , ya fara gayan abun da suke su da man yan su tun bayan tafiyar ta,

Ran ta ƙara ɓaci tayi, tace su kawo mata CCTV footage na tun ɗaga ranar da bata nan,

Cikin rawar jiki suka je suka kawo, ta fara kallo, har aka zo lokacin da masu tafiya club suka tafi,

Masu shan giya suka buɗe hajar su, har kawo i lokacin da wa ina nan mutanen suka diro, zuwa lokaci da suka shiga gidan, suka yiwa lion allurar bacci suka ɗauke shi suka tafi da shi,

Latifa tana gama kallon footage ɗin ta haɗa hannun ta guda biyu ta sa shi a kunkumin ta tana ƙare musu kallo, har idon ta ya rine yayi jawur,

Shukura ce ta dafa ta zata yi mata magana, ta ban gaje ta miƙe , ta ɗauƙi bindiga, sai da ta harbi mutum biyar aka suka faɗi ba tare da sun motsa ba ,

dakyar aka samu aka rinriƙe ta , ana bata haƙori , kafin ta sake fin cike wa , ta nuna su da yatsun ta , tana cewa na baku nan da awa ishirin da huɗu, ku nemo shi ku dawo min da shi ko kuma ko wan ne daga cikin ku na aika shi barzahu,

Cikin sauri suka fita dan fara neman inda lion yake, ita kuma ta shiga cikin wani ɗaki ta kashe wutar ɗakin, tayi shiri cikin wasu baƙaƙen kaya , ta fara zagaye ɗakin tana wasu sambatu na tsafi,

Ba jima wa daƙin ya sake haɗe wa yayi baƙiƙƙirin, sannan dakin ya tsage gida biyu , babban boka da suke kira da uban su ya fara sauko wa daga sama zuwa cikin ɗakin ,

Har sai da ya ƙara so gaban ta , sannan ya fara magana yake wulaƙan tacciya yar ko meye dalilin da yasa kika kira Ni ba lokacin haduwar mu ba

Latifa cewa tayi babban boka temako na zo nema cikin sauri, nayi saka ci ya bace daga hannu na , ka temake Ni ka gaya min in da yake,

Babban boka cikin babbar murya shi , ya sheƙe da wata nasa muɗiyar dariya , sannan ya ce a wannan karon kin yi wasa da sa Ar ki,

Kuma ba abin da zamu iya miki ko ki nemo shi da kan ki ko rayuwa da duk abin da kika mallaka su tarwatse

Yana gama cewa haka ya ɓace ɓatt, dakin ya dawo, dai-dai, duka ta kai wa ban go latifa, hankalin ta ya ƙara tashi jin abin da babban boka yace,

Ta fara neman lion kamar wacce zata yi hauka, ba wuya ta kashe mutum, Hajiya shukura ganin abin yafi ƙarfin ta , ta tattara ina ta ina ta tabar ƙasar tsoron kada garin haukar latifa ta kashe ta a ban za,

Farko da latifa tayi tunanin abokan gaban ta ne suka sace lion shiyisa tai ta neman shi a nan cikin India,

Amma duk da haka tura Nigeria a duba mata can , an kuma tabbatar mata baya can

Duk ta hauka ce tana neman shi lungu da saƙo,

*****

Saudiya daddy ya wuce da lion cikin sirrin , zuwan su daddy ya haɗo man yan malamai da suka kwarewa gurin maganin asiri da tsafi,

Aiƙi tukuru a wannan sata aka fara yi akan lion har sai da Allah ya basu Nasarar , cire ko wani irin mugun shiri a cikin shi,

Ya dawo dai dai kamar , da ya dena yawan mugayen mafarkai,

Komai ya fara dawo mishi dai-dai ya mai da hankalin sa gurin bautar Allah da neman gafarar shi,

Aka fara bashi horo na suja, yadda zai kare kan shi ya zama sadaukin maza , duk wani tsoro ya dena jin shi

Cikin watan Ni ukun da lion yayi a saudi, ilimin addini sai san Barka,ban garen jarunta kuwa ya zama sadaukin maza,

Ba irin launin faɗan da bai iya ba, ko cikin wa'in da aka basu tsaro tare shine zakaran gwajin dafi

Dady duk ya mai da lion haka ne ganin irin ma ƙiyan da ya tara yanzu ba mai tun karar shi,

Yanzu sai shirin koma War shi Nigeria, wani da zai faru ne a gobe inshallah Allah

Welcome back our lion

*******

Abiya ni in cigaba

Tare da vote, comments ,follow


MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now