page25

214 18 3
                                    

✨✨✨✨✨✨
Mai sona
✨✨✨✨✨✨

بِسْــــــــــــــــــــــمِ اَللّهِ الرَّحْمنِ الرَّحِيمِِ"


Page 25


*𝐖𝐑𝐈𝐓𝐄𝐑 { 🅟︎🅞︎🅥︎ }*

Shan hannu sukai, lion ya ɗauki key ɗin motar shi, ya fita a cikin gidan,

Yana toƙin mota yana jin waƙar dj Khalid dan yana cikin farin ciki na samun mafita da yayi a yau ɗin nan, a haka har ya ƙarasa gida, ya fa-ka motar ,

Wa yo-yin shi ya ɗe ba ya fito daga cikin motar ya shiga cikin part ɗin Shi,

Da shigar shi cikin part ɗin bedroom ya wuce ya shiga toilet ya watsa ruwa,

Ya fito, yayi shafe-shafe shi kamar wata mace, boxer kawai ya saka ya dawo Palo ya zauna ya kunna tv,

Ya kamo tashar da ake buga gwallon ta mola, wayar shi ya janyo dan raban da ya danna tun jiya,

Tarin miss call ɗin A'ishah ya gani , da message, hakan be sa ya damu ba sai ma mur mushin mugun ta da yayi tuno da ƙoɗi rin shi akan ta ,
Danna mata kira yayi,

A'ishah dake jero salloli tana rokon Allah yasa lion yana lafiya ne taji wayar ta na ringin,

Cikin sauri ta sallame ta janyo wayar ta , sunan lion da ta gani ne yasa ta amsa kiran da sauri hannun ta har rawa yake ,

Cikin Muryar ta me kama da kuka tace;, yaya Aliyu, kaine, acan ɓangaren lion murmushi yayi yace baby nine mana ,

Wani abu ne mai nauyi wan da zaman shi cikin zuciyar mutum zai iya sa mutum ya kamu da ciwon zuciya koma ya mutu lokaci ɗaya ,

Ta ji ya sauka, ya ɓace ta ɗena jin ran ɗaɗin da take ji a cikin zuciyar ta,

Ta furta alhamdulillah kana tace yaya Aliyu ina ka shiga nake ta neman ka har gidan ku na bika amma ban same kaba,

Lion cewa yayi relax baby girl, shiru Aishah tayi tana sauƙe nun fashi wani na bin wani,

kamar wacce tayi guɗun fanfalaƙi ko kuma wacce kura ta biyu ta samu ta tsira

Lion ya cigaba da cewa yanzu ina gida kizo ki same Ni, ina so muyi wata magana ne,

A'ishah ta bashi amsa da to gani nan , tashi tayi taje ta wanƙo fuska, ta shafa ƴar hoɗa da man baki , ta gyara kwallin idon ta,

Tasa hijabi ta ɗauƙi jakar ta , ta fito cikin ɗakin, ɗakin mama ta leƙa tace mama Ni na wuce, mama tace to a gaida mutan gidan kice in na nan zuwa, Aishah tace to ta fita,

Nan ma a waje sallama tawa malam ta wuce, ba wani ɓata lokaci ta ƙara so gidan su lion ta tura ƙofar gidan ta shiga,

Tana kawowa dai-dai ƙofar shiga part ɗin lion ta ja ta tsaya, ta buɗe jakar ta , ta ciro ɗan turare ta mai suna toch , ta shafa a bayan kunnuwan ta da tafuƙan Hanna yen ,

Ta rufe ta mai da , ta tura ƙofar shiga ta shiga, bakin ɗauke da salla cikin wata siririyar murya, lion ɗago wa yayi ya kalle ta, dumm gaban shi ya bada ganin irin kyan da tayi mai,

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now