page 40

216 21 13
                                    

•𝐏𝐚𝐠𝐞{40}•

🅝︎🅞︎🅣︎ 🅔︎🅓︎🅘︎🅒︎🅣︎🅔︎🅓︎

*B͎i͎s͎m͎i͎l͎l͎a͎h͎*

     °°°°°°°°°°°°°°°°°°°°

" Bugawar zuciya ya samu , da ba dun kun yi han zarin kawo shi asibiti ba da sai in ce da ku yanzu kun rasa shi,

Amma yanzu mun shawo kan komai, zuwa cikin dare zai farka, zan rubuta mai wasu magungunan,

sannan ku tabbatar kun bashi cikakkiyar kula wa bad da bayani, ko ɗaga mai hankali,

In kuka kula zuwa gobe inshallah zaku iya koma wa da shi gida, godiya mama tai tawa doctor, yace bako mai , ai aikin shine,

Kafin suka fita daga cikin office ɗin , ɗakin da aka kai malam, mama taje , ita kuma yaya naja ta koma gida dumin taho da abin da zasu buƙata zuwa gobe.

Tana shiga zauren gidan ta cire hijabin ta , ta shiga cikin gidan a fusace tayi, ɗakin su Aishah, mardiya da nafisa miƙe wa sukai ganin yadda naja ta shigo gidan ba sallama

Kafin su shiga ɗakin suka jiyo ihun Aishah, da gudu suka ƙara sa , naja na kan Aishah ta rufe ta da duka,

Ɗakyar suka kwace Aishah a hannun ta, nafi taja Aishah gefe, yaya mardiya ta tambayi naja lafiya, naja dake faman nishi tace,

Wannan mai yar yarinyar nema take taga ta kashe mana uba, bayan abin kunyar data jan yo mana,

Tayi sanadiyar gojewar farin cikin mu a gidajen maza jen mu, fita ma yanzu in muka yi sai dai mu sauke kan mu ƙasa, dan kunyar mutane,

Aure ya mutu, na yaya Sa'a kuma rawa yake yau tana nan gidan gobe tana can, duk sanaɗiyar wa, wa yaja mana,

Ita , shine baza ta bar mu haka ba, wai wannan yarinyar, cikin shege ne da ita duk tsawon lokacin nan,

Ba wannan ba sanadiyyar haka zuciyar baba ta buga, saboda baƙin cikin abin kunyar da ta sake jawo mai,

Mai mukai miki dan Allah Aishah kike saka mana da irin wannan hukuncin,

Me tsohon na yayi miki in banda nuna miki soyayya da yayi fiye damu, naja na gayan haka tana fashe wa da kuka,

Kawo iyan zu da naja ta fara yi musu bayani, mardiya da nafisa dur ƙushe wa sukai a ƙasa suma suna kuka, shin wannan wace iriyar ƙaddara ce

A'ishah kukan take shar ɓa, ji take kamar zuciyar zata kama da wuta , jikin kuwa ji take kamar ya dena amfani ta dawo kamar wata gawa,

Haka suka ci kukan su suka tashi suka shirya, suka wuce asibiti, a ka bar Aishah ita ka dai a gida,

Tana jin gine da jikin bango, ta ɗaura hannun ta akan cikin ta, tunanin take ina lion ya shiga ne haka,

A fili ta furta wai yo Allah na me kake nufi ne Aliyu ina ka shiga ka bar Ni , Ni ka ɗai a cikin irin wannan yanayin da nafi buƙata ka,

Shin ina alkawarin da kamin, na cewa zamu rayuwa har mutuwar mu,

TUNA BAYA

Wata uku Baya, lion haba baby na ki bari yau nayi mana, wallahi yau in ban yi mutuwa zan yi,

Nadan tsoro kike kar in zo in guje ki, na miki alƙawarin zama tare dake har ƙarshen nunfashi na sai dai ke kika so mu rabu,

Zan rayuwa dake a ko wani irin hali, bazan taɓa barin kina ko juya miki ba,

Kada ki man ta wannan shine auren, in da nayi niyar cutar dake da tun ranar da na haɗu dake zan yi,

Ina da hakki a kan ki , ke mata ta ce, kuma kin san girman lefin dake kan mata ta bijirewa mijinta,

Ni bazan miki dole ba amma ki sani akwai mata da yawa dake waje suna jiran in ɗaga ido in kalle su ban kalle su ba,

Jin furucin lion Take kishi ya cika zuciyar Aishah, lion ganin ya gano Lagon ta cikin daɗin baki ya cigaba da lallaɓa ta har ta Yar da,

Ya mata alkawarin zata daɗi duk abinda zai mata, san zai biya a hankali tun da wannan shine karon ta na farko,

To dai a ranar ne lion ya raba Aishah da budurcin ta,

BACK TO STORY

share hawayen da ya tsiyayo mata saman fuskar ta. Aishah tayi ,

Wato dama duk tarin alƙawarin nan ƙarya ne da hanyar da zai bi ya yau dare tane,

Shiyisa hausawa suka ce namiji ba ɗan goyu ba,lallai kam sunyi gaskiya,

A'ishah ta ce na shiga uku , naje na biye wa namiji na wargaza rayuwa ta da ta ahali na,

Dole in rabu da su ba dan ina so ba, sai dai na sake samar musu da farin cikin da suka rasa tun watannin baya , dumin zama na dazu zai iya jefa su cikin wani irin mugun yanayi da yafi na baya,

Zama na anan a yanzu zai iya sa na rasa mahaifina dan baƙin cikin gani na da abin da ke ciki ,

Dumin sama wa abin da ke ciki na rayuwa mai kyau dole in bar gidan nan, bazan bari abin da bai ji ba bai ganin ba laifin dana aika ta ya shafe shi

Miƙe wa tayi ta janyo jakar da take zuba littattafan ta ada, ta zazzage su ,

ta fitar da takardun makaranta ta a ciki, tare da wasu kudade masu yan dama ta zuba a cikin jakar, tasa hijab da nikab, ta ɗauƙi kalli akwatin da lion ya aiko mata da shi,

Haka kawai zuciyar ta ya bata ta tafi da shi, aje wata farar takar da tayi a saman jaridar su ,  ta rataya jakar taka akwatin ta fita, daga cikin gidan

Kafin taɓar ƙofar gidan sai da ta juyo ta sake kallon gidan na ƙarshe, kwalla ta cika idanun ta, haka ta ja akwatin ta bar ƙofar gidan,

Da ta ƙarasa bakin ti-ti, masu keke nafep da mashi na suka yo kan ta, suna tambayar ta Hajiya ina zaki ne, saban gari zaki,

Ɗaya daga cikin masu keke nafep ɗin ta cewa , saman gada zata, kuma shata take so tayi, suka yi ciniki zai kai ta a ɗari biyar, yasa akwatin a ciki,

Ta shiga ya tada suka ɗauƙi hanya, a bakin garegin ya sauke ta ya fito mata da kayan ta,

Masu motocin suka zagaye ta suna tambayar ta , Hajiya Kaduna zaki , Abuja zaki Kano zaki

Buɗar bakin Aishah tace .....

•••••••••••

A GASKIYA BAKWAYIN COMMENT DA VOTE, SHIYISA BANA DAMUWA DANAYI UPDATE NIMA, TO GANI NAKE KAMAR BA A KARAN TAWA,

NIFA MUTUN CE KU WANI ƊAN ADAM YA BUƘATAR YAR YABA WA

SABODA HAKA WANNAN KARAN BUKATAR SHARHI.

IN NA GANI GOBE ZAN IYA UPDATE.

NA BARKO LAFIYA.

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now