page 47

184 24 3
                                    

*Page 47*


°°By jiddorh°°

Nakan ɓata lokaci na ina typing am saboda Allah comment vote ko following ɗina na daƙiƙo kadan sai ya gagare ku.

_________________________

"Yau kwanan A'ishah biyu gidan me ƙosai , cikin kwanaki biyun nan me ƙosai ba ƙaramin ɗawai niya da ita tayi, ba gashi tun da tazo take fama da amai da kwadayi,

Yanzu haka tana kwance tsakiyar ɗaki ta jiyo hayaniya daga waje, kasa kunnen ta tayi taji me ke faruwa ,

Kamar Muryar me ƙosai ta jiyo tana bada haƙori in dai kuma ba kunnen ta bane yake jiyo mata ba dai-dai ba,

Ta shi tayi ta leƙa dan taga me ke faruwa, labulen ta daga ta tsaya a a bakin ƙofar ɗakin , dai-dai inda wata mata ta tsare me ƙosai tana cewa wallahi na baki nan da maraice ki haɗo min kuɗin wake da man gyada na,

Me ƙosai tace haba larai sai kace yau na fara amsar kaya a hannun ki ban biyan ki , ki temaka ki sake hakori zan haɗo kuɗin ki in kawo miki wallahi kwana biyu duk abubuwan ne suka haɗu suka chaɓe min,

Matar cewa tayi ke tsohuwa Ni ba haƙorin ki Nazo jiba, in zaki bani kuɗi na kawai ki ban,

A'ishah ganin abin yana nema yayi yawa yasa ta ƙara sa fita , ta tsaya gaban matar tace nawa ne kudin ki,

Harara matar ta wurga wa A'ishah ta ce ke kuma a suwa, A'ishah tace sanin ko wace ce kike so kiyi ko kuma kuɗin ki keke so a biyaki,

Matar ta ce wa Ni , riƙe usulin ki a bani kuɗi na shi ya kawo Ni, A'ishah ta ce oh Allah ko to nawa ne matar ta ce dubu uku ne cif, tana cewa haka A'ishah ta shiga cikin daƙi ta buɗe hand bag ɗin ta , ta ir ga dubu uku ta mai da sauran ta fita,

Tana fita ta miƙa wa matar kuɗin charaf matar ta fisge kuɗin , tana washe baki tana cewa ma dallah yanzu naji batu bata tsaya ba ta fita a gidan,

A'ishah kallon me ƙosai tayi tace kiyi hakori Allah zai yi maganin ko mai, tana cewa haka ta shiga cikin daki,

Matar gidan da tun da aka fara rikicin bata ce komai ba bare ta bada haƙori, tace Chaf ɗi jam , ita me ƙosai bata lura da ita Bama ita ma ta shiga cikin ɗaki,

Samun A'ishah ta yi a zaune, ita ma ta nemi guri ta zauna, tace yar nan da kin sani , A'ishah ta tare ta bata bari ta ƙara sa abin da take don cewa ba,

Tace a'a baba , ba yadda tun ha ɗuwa mur kike temako na sai yau ɗan naga kina cikin wani hali na neman temako kuma ina da halin temaka miki na kasa, a gani na hakan ba halarci bane,

Kuma sannan in baki man ta ba tun farkon haɗuwar mu dake nace miki ina neman gidan haya, kika ɗau ke Ni kika kawo Ni cikin gidan ki, kina ciyar da Ni da shayar da Ni da dukkan iya War ki, ba tare da nuna cewa kin gaji da ni


      *{ a daure a rinƙa com
     ments da vote dan Allah }*

Kudin da na bawa matar cikin kuɗin da nayi niyar kama haya ne tun farko, buɗe jakar ta tayi ta ɗebo raguwa kuɗin ta ir ga , dubu arba'in da biyar ne yayi saura, cire dubu talatin tayi ta miƙa wa me ƙosai tace ga wannan ki sai mana kayan abinci sauran ki tada jalin ki, Allah zai rufa asiri

Ƙin ƙarɓa me ƙosai tayi A'ishah ta ce baba dan Allah ki amsa karki cewa komai ai an riga an zama ɗaya,

Am sa me ƙosai tayi tana cewa shike nan ƴar nan Allah dai ya shi miki albarka ya kuma sauƙe ki lafiya, tana cewa haka tana share hawaye,

Can ƙasa A'ishah ta am sa ameen, har cikin zuciyar A'ishah abin da tayi tana ganin hakan shine dai-dai, koba komai me ƙosai ta bata ma tsuguni me tsaro, amma in da take ta kama haya ne bata san wani irin kallo mutane zasu mata, ba wani da zai am she ta,


Da maraice me ƙosai ta fita ta sissiyo musu kayan abinci wan da zasu buƙata, har da ɗan bushesh shan kifi dan taga kwana biyu A'ishah na fama da kwaɗayi,

Da ta dawo bata huta ba ta ranga ɗa musu dafa duka tasha man ja da kifi, aiko A'ishah ta ci sosai dan zata ran yar tayi kwana ki bata ci abinci me yawan wannan ba har ta ƙara samun ƙarfi a jikin ta

*****************
Washe gari me ƙosai ba ƙosai kawai tayi ba hadda koko da mutane suka kwana biyu suna mata mitar ta fara, yau A'ishah fitowa tayi tana taya me ƙosai sai da dawa

Me ƙosai na suya ita kuma tana zuba mutane , haka har ya ƙare, mutane ba ƙaramin jin daɗin kokon su kai ba, a kai ta nema , me ƙosai tace sai kuma in Allah ya kaimu gobe.

A'ishah wanka ta je tayi, ita kuma me ƙosai ta ɗumama musu raguwar abin cin jiya, suka hada da koko suka ci, bayan sun gama ci A'ishah ita da kan ta gyara ko ina,

Me ƙosai ita ma tayi wanka ta shirya ta wa A'ishah sallama ta tafi gidajen da take ƙananan aiyuka dama tayi kwana biyu bata fita ba,


    ( bazai ɗauke ku min Tina     
     biyu ba gurin following ɗina)

Haka tai ta shiga gida-gida wani gidan tayi wanke wanke ko shara wani gidan ma wanki, ba wani ƙuɗi suƙe bata ba , wasu hamsin zuwa ɗari gidan da sukai ƙoƙari ma har ɗari uku suke bata,

A'ishah bayan ta gama aika ce aika cen da take yi , kwanciya tayi ba daɗewa bacci ya kwashe  ta cike da gajiya,

Sai da aka kira salla azahar ta tashi tayi sallah, fita tayi dan tana so ta ɗaura musu abin da zasu ci da rana kafin me ƙosai ta dawo,

Fita tayi ta haɗa wuta ta daka kayan miya, ta daura taliya ba, daɗe wa ta gama ta sauke tukun yarta shiga ɗaki da shi, cikin kayan me ƙosai ta samu wata ƴar ƙaramar kula ta zuba ta liyar a cikin, ta zuba wa kanta itama ta zauna ta fara ci, bayan ta gama ta sha ruwa ta fitar da kwanan,

Tana fita kuwa sai ga me ƙosai tayi sallama ta shigo cikin gidan
 

   Amsa wa A'ishah ta yi , ta mata sannu da zuwa , me ƙosai ce yauwa yar nan sannu ki da zaman gida shiru ko murmushi kawai A'isha tayi , me ƙosai ta shiga cikin ɗaki, A'ishah ta ake kwanon ta wanke hannun ta ta bi bayan ta ,

Ɗauko kular da ta zuba abin cin a ciki tayi ta aje gaban me ƙosai tana cewa ga abin ci baba, me ƙosai buɗe wa tayi tana cewa yauwa amma kin yi kyan kai dama ina chan ina ta tunanin ki ba abin da zaki ci,

Buɗe wa me ƙosai tayi ta soma ci, to a haka dai lokacin yayi ta wuce, zaman A'ishah da me ƙosai sai son Barka, dan tana bata kulawa sosai kamar ƴar da ta haifa da cikin ta, .....

°°°°°°°°°°°°°°°°°°

Dan Allah dan Allah a rinƙa comments da vote da following ɗina kune zaku ɗaga ni

Jumma'a Mubarak

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now