[ DUK WANDA YA KARANTA BA TARE DA YAYI VOTE KO COMMENT BA SHI DA MAHALICCIN MU ]
Page 52."Me ƙo sai ta fara fito da tsofaffin kwanukan ta tun na aure, A'ishah ta cigaba da fito da kayayyakin sawar ta da suka yi raguwa,
Tana cikin fita da su ta ɗago wata riga ta ji abu ya faɗi ƙasa daga cikin rigar, sa hannu ta yi inda abin ya faɗi ta ɗau ƙo dan taga ko menene,
Kyawawan ida nuwan ta da suka sha kuka suka rine da hawaye ne , sukai tozali da ATM card,
Take wani mur mushin farin ciki, ta rungume ATM ɗin a ƙir jin ta kamar yadda uwa ke rungume ɗan ta, san nan ta furta alhamdulillah har so uku,
Me ƙo sai daka tawa tayi da abin da take ta juyo tana kallon A'ishah, take mama ki ya cika ganin farin ciki da yake bayya ne a kan fuskar A'ishah wanda tun ha ɗuwar bata taɓa ganin A'ishah a wannan yanayin ba,
Tambayar ta yi da yar nan lafiya kuwa, cike da murna A'ishah ta miƙa wa me ƙo sai ATM card ɗin tana baba Allah ya kawo mana maganin matsalar mu,
Amsar ATM ɗin me ƙo sai tayi tana maimaita maganin matsalar mu, sake kallon ATM ɗin tayi ta kalla ta sake kalla tana juya shi, ita dai a halin yanzu ta san ba abin da suka fi buƙata sama da kuɗi ,
gashi A'ishah ta bata wani abu haka nan wai shine maganin matsalar su , to ko dai damuwa ce ta ruɗar da A'ishah har take wa wannan abin kallon kuɗi ,
Dogon nunfashi mai ƙo sai taja sannan ta ce ƴar nan me kike nufi, A'ishah duk ta gano me , me ƙo sai take tunanin ɗan murmushi tayi me kyau ta ce,
Baba aikin san banki in da mutane ke ajiyar kuɗi, me ko sai ta ce kwarai kuwa na kan ma wuce su in zani yawon aika ce aika ce na,
A'ishah ta ce yauwa , wannan katin da kike gani shi ne mutane suke amfani da shi gurin cire kuɗaɗen da suka yi ajiya,
To nima wannan nawa ne , nasan ko kuɗin sadaƙi na da ke ciki yafi ƙarfin kuɗin maganin AHYAN, alhamdulillah me ƙo sai ta furta ta ce in dai kam maganar gaskiya ce ƴar nan da muwar da muka shiga yau ta zo ƙarshe,
Yan ke shawarara sukai akan A'ishah ta je ta cire kuɗin ta siyo maganin ayan , me ƙo sai ta zauna a gida dan ta kula da yaran,
Har bakin bankin me adai daita sawun da A'ishah ta shiga ya sauƙe , ta fito ta sallame shi , ta ƙara gurin ATM machine ɗin ta bi layi yadda taga ana yi, har aka kawo kanta,
aiko kamar yadda lion ya koya mata ran da ya Kaita aka buɗe mata account ɗin ,bata manta ba, cike da addu'a ta sa ta fara duba balance , abin da idon ta ya gane mata ne yaso ya ruɗar da ita har ta kusa faɗuwa kafin ta saita kan ta,
Wato kuɗin da ke ciki sun kai kimanin 4 MILLION har da ƴan canjin a sama kusan dubu ɗari biyu,
Take ta fara cire dubu ɗari biyu ta zare ATM card ɗin , tasa su cikin jaka ta bar gurin cike da farin ciki,
Pharmacy ta koma ta siyo magungunan AHYAN, ta fito tsallaken ti-ti taga inda ake gasa kaji , take ta tsallaka ta siya guda biyar, uku nata biyu ta ce abawa almajiran da ke gefe, sai da ta siya kayan drinks kafin ta hau abin hawa ta koma gida,
Tana shiga cikin ɗakin ta iske AYANA ta tashi me ƙi sai na mata rawa da waƙa,
Aje kayayyakin da ta siyo tayi a gefen me ƙi sai na mata sannu da zuwa ta amsa ta amshi AYANA ta na cewa rigimammiyar ƴar nan har kin tashi, me ƙo sai ta ce aiko maza ki bata mama kafin ta fara rigimar Tata,
Zama A'ishah tayi ta fara bawa AYANA nono, me ƙi sai ta zauna , tana buɗe ledojin da A'ishah ta shigo da su ledar maganin ta fara buɗe wa tana ganin su ta furta alhamdulillah, kafin ta je kan leɗar kajin da tun shigo War A'ishah ƙamshin su ya cika ɗaki, buɗa me ƙo sai tayi tana cewa a'ah kice yau take sallah gare mu,
Sai da A'ishah ta gama ba yaran nono kafin ta zauna suka fara ci kamar ba gobe dama su me ƙo sai an daɗi ba a haɗu ba , ko magana babu jan kaji kawai take tana cika bakin ta tana kora wa da pick yght ,
Cewa tayi uhmm wannan madara ko a aljanna aka naka in baka gode wa Allah to sai dai fa mutane su ma taron dangi a kai kai wuta,
Dariya A'ishah ta fashe da ita ta ce kai baba duk san tin ne haka,
Haka dai ranar suka sha shagali har cikin me ƙo sai ya so ɓaci,
Bayan kwana biyu A'ishah ta ƙaro wa yaran kayan sawa da duk abin da suke da bukata,
Kafin ta samu me ƙo sai bayan ta gama soya ƙo San ta, tace baba dama wata magana na zo muyi, me ƙo sai ta ce tooh ina jin ki ƴar baba,
A'ishah ɗan jan nun fashi tayi sannan ta ɗau ra da cewa dama so nake na siya mana gida ɗan madai daici wan da bazai wuce MILLION ɗaya da rabi ba,
Me ƙo sai cewa tayi eh ƴar nan ban ƙi ta ta ƙi ba , amma nake ga da kin bar kuɗin nan kin cigaba da siya wa yaron nan magani har Allah ya kawo mai sau ƙi ,
A'ishah ta ce , a'a ko da an siya gidan kuɗin za suyi raguwa sai a cigaba da siyar mai kafin su ƙara wayau na nemi aiki da ta karddun makaranta na,
Me ƙo sai ta ce to shike nan bari na shirya naje gurin ya'u dillali nasa ya bin cika,
Haka me ƙo sai tasa dillali ya bin ciko musu gida, me ɗako na uku a ciki tare da ɗan ma dai-dai cin tsakar gida,
Dama san da suka bada cigiyar gidan sun ce na MILLION ɗaya da rabi , to haka aka gama ciniki A'ishah ta biya su a ka gama cike ko wace takar da,
A'ishah ta siyo kayan da za a zuba cikin gidan na wajen ki manin dubu ɗari huɗu, a ka yiwa gidan ƴan gyare-gyare suka haɗa ina su ina su, suka yiwa maƙota da abokan arziki sallama suka koma sabon gidan su,
Haka rayuwa ta cigaba da tafiyar musu cikin kwanciyar hankali ba tare da damuwar komai ba, tare da tai makon baba me ƙo sai A'ishah ta cigaba da rai non su AHYAN da AYANA , yaron akwai saurin girma, suna shiga shekara ɗaya A'ishah ta nemi aiki a wata primary school dake kusa da su , duk wata za a dinga biyan ta dubu sha biyar,
Haka rayuwa ta cigaba da tafiya
BAYAN SHEKARA UKU....
......................
KUYI HAƘORI KWANA BIYU WUTAR MU TA LALACE WANNAN MA DAI DA KYAR AKA SAME SHI , KADA KU MANTA KUYI VOTE DA COMMENTS BAZAI DAUƘE TSAWON LOKACI GURIN YIN FOLLOWING ƊINA BA NAGODE..
By Iqbal

YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...