page 61

221 19 5
                                    

Not editing

" Ka shirya in Allah ya kai mu an jima da maraice za muje kai ziyara gidan Alhaji joorda , ya jima yana gaiyata ta tare da kai Allah bai bani dama ba sai yau, inshallah nayi mai alƙawarin zuwa,

Lion cewa yayi but daddy ina da abin yi a asibiti, daddy cewa yayi na tambayi pA ɗin ka yace ba abin da kake da zaka yi a yau , so kayi min shiru ka tashi kaje ka shirya dan today I won't take no for answer,

Tashi lion yayi ba tare da yace komai ba ya wuce part ɗin shi, ran shi a ɓace, be son me yisa daddy yake Mai haka ba,

Shi yana nan yana neman matar shi da ɗan shi, shi kuma nema yake ya haɗa su alaƙa da yariyar abokin shi da ta liƙe mai , ta takura mai a asibiti,

*********

Gidan Alhaji ahmed joorda, me kuɗi ne kuma aboki ga shugaban ƙasa, yana da mata ɗaya tare da ƴa mace kwalli ɗaya da suke matukar so shi ɗa matar

Tun da yarinyar ta kyalla ido akan lion , ranar da ya fara aiki a asibiti ta kamu da soyayyar shi, bata ɓata lokaci ba ta sanar da iyayen ta, dan duk abin da ta nema a gurin ta da rawar jiki suke mata,

Iyayen yan ta sunyi farin ciki da jin wannan al'amarin, Alhaji joorda ya shirya dan ya je ya haɗu da shugaban kasa dumin kai mai wannan ƙudirin na shi,

Daddy yayi farin ciki da zuwan bazata da abokin nashi yamai, bayan sun zauna sun gama gaisa wa , suna cikin fira Alhaji joorda ya saƙo mai zan cen me zai hana su haɗa yaran su aure ko hakan zai ƙara dunƙon zumunci tsakanin su,

Daddy yayi na'am da hakan, sai dai yace kafin nan a fara jin ta baƙin yaran kar a yan ke musu hukunci a kan rayuwar su ba tare da jin ta ayin su a kan lamarin ba, kaga in sun dai dai ta kan su sai aje mata ki naga ba

Alhaji joorda yace kuma haka zai fi, da haka suka yi sallama ya wuce daddy ya mai rakiya

Da ga ranar daddy ya fara takura wa lion akan ya fito da mata yayi aure ko kuma ya aura mai zaɓin shi da ya mai, har dai ya zo ya gano al'amarin da shi lion ɗin ke ɓoye mai ,

ya dena ta ƙura mai kan maganar aure, sai ma temaka mai da yake dan binciko inda matar shi da ɗan suke, sai yau kuma da ya umarci lion ɗin da su shirya zasu je gidan Alhaji Ahmed joorda ɗan kai ziyara ba tare da ya gaya mai dalilin da yasa zasu je gidan tare ba,

Shi kuma Alhaji joorda sanar da matar shi yayi Hajiya Binta akan man yan baƙin da zasu Yi,

Jin wannan labarin ita ma ta je ɗaƙin ƴar ta rukayya da suke wa inkiya da ruky, ta same ta gaba ringin light tana shan rawa a tiktok,

Ruky ganin mahaifiyar ta shigo cikin ɗakin yasa ta ka she wayar tana cewa momma lafiya , Hajiya Binta zama tayi gefen makeken gadon dake cikin ɗakin,

Tana cewa na kawo miki labari ne mai daɗi, ruky ta ce wani irin labari ne haka momma, hajiya Binta ta ce cinka zakiyi,

Dan tsaya wa tayi tana tunani , sannan ta ce visa na ya fito na tafiya Cairo Egypt, hajiya Binta ta ce a'a baki cin ka dai-dai ba,

Ruky sake tunani tayi amma ta kasa gano labarin da Hajiya Binta ta zo mata da shi , cikin shagwaɓa ta ce common momma gaya min mana

Hajiya Binta cewa tayi ok ok , yanzun nan baban ki ya kira Ni ya gaya min , an jima mai girma shugaban kasa tare da Aliyu zasu zo gidan nan, kuma ina tunanin akan maganar auren ku zasu zo,

Ihu ruky tayi ta rungume mahaifiyar ta , tana cewa wow momma Amma wannan kyakkyawan labari ne , me yakai mata nayi ,

ta shi tayi ta buɗe closet ɗin ta tana wu go kaya ƙasa, tana cewa oh my God wani irin kaya ya kamata ace nasa , i have to look good, everything have to need in it way,

Momma me kike ganin ya kamata ace an girka musu , cewa tayi yau wa , ina wannan sabuwar cooker ɗin tamu naga ba lefi ta iya girki ,

Bari in kira ta in bata list na abin da zata girka masu, landline ɗin daƙin ta danna , ana ɗauka ta bada umurnin da a toro mata da wacce ke musu girki,

*********

A'ishah yau kusan satin ta biyu a garin Abuja ita da AHYAN bata samun matsala a aikin ta tun da ta zo,

Yanzu haka ma kwance take ita da AHYAN cikin ɗakin da aka bata, suna kallo a wayar ta, taji anyi knocking ƙofar ɗakin , ta tashi ta buɗe dumin ganin ko waye,

Shugaban ma'aikatan gidan ce, murmushin A'ishah ta mata, matar ta ce ƴata maza ɗau ko mayafin ki muje,

Hajiya na son ganin ki, da to A'ishah ta amsa sannan ta sanya hijabin ta ma dai dai ci iya guiwa , sannan ta jawa AHYAN kunne da kar ya sake ya fito waje sannan ta bi bayan matar suka wuce,

Mata biyu suka iske a falo a zaune ɗaya ita ce matar da ta haɗu da ita lokacin da aka kawo ta , ɗayar kuma tana ganin ita ce yarinyar gidan,

Shugaban ma'aikata ce tace Hajiya gata na kawo miki ita, Hajiya Binta cewa tayi shike nan zaki iya barin ta ki wuce, tafiya ta yi,

Ruky ƙare wa A'ishah kallo tai tayi, har sai da Hajiya Binta ta ce , mu ruky in kin gama making list ɗin bata ta je ta fara girka wa, ta ɓe baki ruky tayi sannan ta miƙa wa A'ishah takar Dar da ke hannun ta,

A'ishah ta sa hannu ta amsa, ruky tace ga list nan kije ki girka min wa'in nan kalolin abin cin, kuma bana son ayi Making single mistake, Dan kuskure ɗaya aka samu you're done, zaki iya wuce wa,

A'ishah cikin zuciya ta ce tofa , kafin ta wuce kitchen ta fara ......

Enjoy reading Kai na namin ciwo

Kuyi manage , don't forget to vote and comments thank you..

MAI SONA  { 2023 }Where stories live. Discover now