Page 69
" Innalillahi wa'in ilaihir raju' un shi daddy ke furta wa , tun bayan samun labarin abin da ya faru da lion da Ahmed gurin dawowar su garin Abuja,
Fitar baza ta ce ta kama mai, nan da nan ya wuce asibitin da aka kai Ahmed shi da rundunar da ke basa tsaro,
Har ɗakin da aka kwantar da Ahmed babban likitan Asibitin ya mai jagora , suka tarar da jami ai cikin ɗakin suna wa Ahmed wasu ƴan tambayoyin akan farkon abun da ya faru ,
Ahmed be ɓoye musu komai ba , ya zayya na musu duk abin da ya sani , na taho War su , da rashin sanin dalilin da yasa lion ɗin bai bari sun tahu da masu bashi tsaro ba,
Da haka suka masu sallama tare da yiwa daddy alƙawarin inshallah ba Jima wa zasu gano su waye suka kai musu hari har suka tafi da lion,
Duk da haka daddy bai bari anan ba ya bada umurnin ga dukkan nin ɓangarorin jami'an tsaron na ƙasar da su bincike al'amarin cikin gaggawa kuma da sirri ,
Dan in duniya ta gano ainihin abin da, ke faruwa mutum ci ne da ƙima na ƙasar zai zube idon duniya,
Duk wannan ɗauki ba daɗin ba daɗin da ake, ko Hajiya asabe , bata san da faruwar lamarin ba,
Dan dama ba shiri suke da daddy ba a ƴan kwanakin nan tun abin da ya faru,
Sai chan ciki dare daddy ya dawo cikin bila, ko da ya kwanta bacci, kasa wa yayi saboda tunanin ko wani irin halin lion yake ciki a halin yanzu,
shin yaci abin ci , koka azzaluman mutanen da suka ɗauke sun barshi yayi bacci, shin wace kalar azaba suke gana mai a halin yanzu,
duk wannan tambayoyin da suka taru mai a zuciya Allah ne masani , sai shi lion din da abin ya sama,
Wai ana cewa bacci ɓara wo , to a wannan karon ko gyan gyaɗi ya ƙasa kama daddy cikin wannan daren,
Daga ƙarshe ma , sai tashi yayi ya fara gabatar da na filfilo tare da roƙon Allah ya kare mai ɗan shi guda a duk inda yake, ya kuma ku butar , da shi daga hannun azzalumai..
Ɓangaren A'ishah haka ne ya faru, tun barin lion gidan zuciyar ta , ta ƙasa samun suku ni , da irin kalamai marasa daɗi da ta faɗa bai,
Bacci ya gagara ɗaukan idon ta , sai juye juye take a kan gado ,
daga ƙarshe she ta ɗauka ko Alkur'ani ta suma karanta wa dumin samun salama cikin kun tacciyar zuciyar ta,
************
Ya ɗau ki tsawon lokaci kafin ya dawo cikin hankalinsa completely , buɗe idon shi yayi me makon ya ci karo da haske, sai duhu , ba abin da yake iya gani sai duhu ,
A hankali duk wani abu da ya faru ya fara dawo mai, a har zuƙe yayi yun ƙurin ya tashi, yaji hannun shi da ƙafafuwan shi a ɗaure,
Na tsuwa yayi ya zauna ya ba tare da yayi yun ƙurin gwada kwance kan sa ba , be nuna alamun damuwa ba ,
sai zaman jiran zuwan ganin wan nan mai gajeren kwanan da ya kira wo wa kan sa jar fa har gida,
Ya jima rufe a gurin kan shi haɗe da gwiwa bai san iya a wannin da yayi ba, ko kuma yace kwanaki da yayi rufe a gurin,
ba wanda yazo gurin ba abin ci bare ruwan sha , baya ganin fito War rana balanta na koma War ta, baya iya gane yanzu dare ne ko rana,
Sai wani lokaci yana zaune yadda yake kawai kwatsam yaji motsin tawo war mutane, natsuwa ya sake yi, ya saki wani murmu shi na iya gefen baki,
Da uban ƙar fi , aka buɗe ƙofar zallar rodi, bannnnm kake ji, take haske ya kewaye ɗakin
Cikin shigar ta , ta ku da yaushe, ta shigo ciki tana taku ɗai-ɗai wasu basa mudawan mutane na take mata baya,
Magana ta Bara cikin shaƙi yan ci da well well well , tana tafa hannu ta,
Ɗago da kan shi lion yayi ya sauke idanun sa a kan ta , murmushin ta ƙai ci yayi , sannan ya furta latifa,
Uban dariyar boss ta fashe da ita , tace mummunan mafarkin ka,
Murmushi lion yayi ya ɗaga kafa ɗa, latifa ƙara sawa gaban inda lion ke zaune tayi, ta tsu gunna,
dai dai gaf da shi har suna iya jin nun fashin juna , ta kai hannun ta kan fuskar shi da ke ɗauke da zaƙo-zaƙon kumbuna, tana shafa fuskar shi,
Sai kuma ta mike , ta kalli dakarun ta, ta fara magana, ina da wani labarin mai matukar ban al'ajabi da zaku so ji,
Akwai wata rana da wata baiwa , ta haɗu da wani yarima , ta ji duk faɗin duniya ba abin da take so ta mallaka sai wannan yarima,
Nan da nan ta shirya, ta sace wannan yarima, zuwa wata duniya da ban,
Ta mai da wannan yarima ya zama na ya dawo bawan ta mai matukar yi mata biyayya,
Baya yin komai sai abin ta ce, amma wata rana, sai latifa ta joyo ta kalli lion , sannan kuma ta juya taci gaba da magana,
Wannan yarima ya yaudare ta ya gudu , a tunanin shi baza ta iya kamo shi ta dawo da shiba a karo na biyu,
Ya cigaba da rayuwa, rana daya wannan bai wa ta sake baiyana ta kuma ɗauke wannan yarima zuwa wata duniyar da ko mutuwa sai ta bata Umar nin dau kar shi,
Dariya lion ya fashe da ita , ya fara magana, wannan labarin sam bai cika ba, a tunanin ƙasƙan tacciyar baiyar ta sake yin nasara ,
sai dai bata sani ba , a wannan karon ɗan zaki ya girma , ya zama shugaba cikin ko wani jeji,
Tunanin baiwar wannan karon ma ta sake cin galaba akan shi , sai dai bata sani ba wannan karan masifa ta kawo wa kan ta har cikin duniyar Tata,
A zafafe latifa ta shaƙe wuyan lion , tana ambaton ƙarya ne,
Da kyar ta sake shi ta fita cikin ɗakin cikin fushi dumin kada ta mai illa fon tana buƙatar shi cikin rayuwar ta dumin shine ma kullin yin nasarar ta,
Sorry
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...