Page 55
( Yanzu komai ya canza , sai kun yi comment da like zaku ga posting, amma in bakwa so kuji yan da wannan yaki zai kasance to, duk wanda ya karanta littattafin batare da yayi comments ko like ba shida Ubangiji )
" Ɗaga can ɓangaren cewa aka yi, you're Excellency ki kwantar da hankali ki kwanta kiyi bacci zuwa gobe zan shigo sai mu san abin yi ,
Da kyar Hajiya asabe ta kwanta bacci shi ma sai ɓarawo ya kwashe ta, da tunanin duk yadda za ayi baza ta bari dady ya haɗu da lion ba,.
Washe gari bayan waye War gari dady da yaje office aikin da ya fara yi na farko shine, ya haɗa tawa ga guɗa su tafi India dan ƙara bincika mai in da lion ke zaune, aikin da yake da kuma wacce suke zaune tare,
Dan a baya nan binciken da ya karan ta , ya tabbatar mai da lion yana zaune ne tare da wata mace,
Ƙawar Hajiya asabe , Hajiya rabi da sassafe ta taho Government house da izinin Hajiya asabe a ka bar ta ta shiga ciki,
A falo ta same Hajiya asabe da ta lula duniyar tunani, bata san ta shigo bama har sai da ta taɓa kafin ta dawo cikin Hai ya cin ta firgirgit ,
Hajiya rabi cewa tayi you're Excellency duk akan wannan ƙaramar matsalar ce kika shiga cikin damu haka,
Hajiya rabi ta ce, baza ki gane halin da nake ciki bane kawai, Hajiya rabi samun guri tayi ta zauna cikin lausassun kujeru , tace, bana ce ki kwantar da hankalin ki zamu sha kan matsalar,
Hajiya rabi cewa tayi, to yanzu me kika gani shine abin yi, Hajiya rabi dan murmushi tayi sannan ta ce,
you're Excellency mai zai hana mu koma gurin malam a wannan karon, tun da tun farko shi yayi mana aiki Aliyu ya bar kasar nan,
Hajiya asabe cewa tayi in haka kike gani shine mafita zan baƙi kuɗi kije gurin shi mugani, dan kin san Ni ba yarda za ayi in fita sai da masu bani tsaro,
Sannan ya shiga cikin ɗakin da take ajiya ta ɗauƙi wata jaka ta zuba kuɗi a ciki da yawan su ya kai wajen million biyar, sannan ta fito ta bawa Hajiya rabi ta ce gashi kije da wannan ina ma basu isa ba kimin waya , zan karo nin kin su ,
Ni dai buƙata kada Alhaji ya haɗu da Aliyu har abada, tashi Hajiya rabi tayi ta ce sha kurimin ki ƙawata , ki sa a ranƙi burin ki ya gama cika ko gida bazan ce , har sai naga haƙar mu ta cimma ruwa,
Da haka a yanzu na miki sallama sai kin ji yadda muka yi da boka, tana cewa haka ta wuce,
Hajiya rabi na barin Government house, ta wuce wani sur kukun unguwa ta faka motar ta , ɗan nesa da wani gida da naga mata maƙil cike da ƙofar gidan,
Tana gama fakin ta ɗau ki jakar ta, kafin ta gama fito wa Ni mutun dake tsaye jikin gidan yayi maza yazo ya tsaya jikin motar har sai da ta fito,
Ya zube a ƙasa yana gai she ta kamar zai mata sujjada, tace; malam ɗan tani kenan ya kake kwana biyu,
Ya amsa da wallahi lafiya lau Hajiya, tambayar shi tayi da cewa malam yana nan , yace eh Hajiya bari aje a miki iso,
Shiga cikin gidan yayi, Hajiya rabi ta samu guri ta tsaya, ba dade wa ya fito yace Hajiya za ki iya shiga,
Shiga cikin gidan tayi, ta shiga wani ɗaki ne a cikin zauren gidan, ɗauke da kwayoyin tsafi , da wasu turarurruka a gefe,
Wani mutumi ne ɗan dattijo zaune a tsakiyar ɗakin sanye da kayan saƙi na mafa Rauta gaban shi wani ƙaton faran tine cike da ƙasa,
Ba tare da Hajiya rabi ta yi sallama ba ta shiga cikin wannan ɗakin ta samu guri ta zauna a gaban wannan mutumin,
Ta buɗe baki zatayi magana , ya ɗaga mata hannu alamar tayi shiru sannan ya ce , na san abin da ke tafe da ke ba sai kin faɗa min ba,
Hajiya rabi ta ce to Allah gafarta malam meye abin yi, shiru yayi ya fara zane zane a saman ƙasar da ke gaban shi,
Bayan wasu ministoci ya ɗago idon shi ya kalle Hajiya rabi, sannan ya fara magana kamar haka,
A wannan lokacin ba abin da za mu iya akan wannan al'amarin, ba Ni ba duk gurin wanda za kije a wannan karon sai sun haɗu , duk girman tsafi ko matsafi a wannan karon bazai yi tasiri a kan su ba,
Hajiya rabi cikin tashin hankali tace yanzu malam ba yadda za ayi ko jin kir ta ha ɗuwar su ayi kafin musan abin yi,
Cewa yayi tun farko ku kuka jawa kan ku an muku aiƙi kun ɗena shiku a cigaba da duba al'amari , ina ma wata matsala ta bullo musan ta yadda za mu cimma abin , har kun ja aljanu sun yi fushi da ku
Yanzu abu ɗaya zan iya muku , ɗau ko wata kwalbar turare ya miƙa wa Hajiya rabi, ta amsa , sannan ya ce ƙi kai mata wannan ta shafa a jikin ta sannan ta tabbatar shi ya fara shaƙar ƙam shin turaren ,
Zata iya juya shi yayi duk abin da take so har na tsawon kwanaki arba'in, kafin nan sai asan Abin yi,
Godiya Hajiya rabi tayi mai sannan ta ɗebo kuɗi masu tarin yawa da bata san adadin su ba ta zuba mai a gaban shi sannan ta tafi,
Sai bayan kwana uku kafin ta samu damar haɗu wa da Hajiya asabe , ta bata turaren ta gaya mata duk yan da zata yi amfani da shi sannan suka rabu ,
Da daddare Hajiya asabe tayi shirin ai watar da aikin ta, ta shirya tsaf ta ɗau wanka sannan ta nufi shashin mai girma shugaban kasa dady kenan,
Sai da tabbatar ba kowa a part ɗin sannan ta ɗauko kwalbar turaren ta shafa sosai wai dan Duk ayikin yaci fiye da yadda ake tsammanin,
Sannan ta shiga cikin palon , tana shiga me makon taga dady , sai taga wan da ke gyara part ɗin yana gyara wa,
Yana cikin aikin shi bayan Excellency ya shi ga daga ciki , yaji wani ƙam shi ya doki han cin , tun kafin ya wai ko wata irin muguwar soyayyar me wanna ƙam shi ,
ta ratsa ƙashi da kwakwalwar kan shi , har yana ji in bai samu wannan mutumi ba zai iya mutu wa,
Juyo wa yayi ya ci karo da Hajiya asabe, washe baki yayi yana dariya yace Hajiya kece ashe,
Gaban Hajiya asabe bane ya faɗi ganin irin kallon da yake bin ta da shi,
Ta daure ta ce Ni ce , da wani abu ko shishigi ne kana so in sa a hukunta mun kai,
Dariya ya sheƙe da ita yace wallahi ina son ki , kawai ki aureni,
Hajiya asabe ta ce kai kana kiran wa kan ka mutuwa ko, ina bai ma sauraren ta ba ya nufo ta yana cewa Hajiya tawo gare Ni , zo muyi aure, zo mu tafi duniyar da babu Kowa daga Ni sai ke sai tsuntsaye,
Nufo ta yake tana ja da baya, dady ne yana daga cikin ɗaki ya jiyu yar haya niya, ya tashi ya fito,
Yana fito wa.........
This is for to day
Maybe we will meet tomorrow by God wish
Ku dai cigaba da kasan cewa tare da Ni a cikin wannan chakwalkwalin chakwakiyar,
Tare da danna min comments da like bazai ɗauke ku tsawon lokaci ba gurin following ɗina,
Sanna akwai sabbin littafi na guda biyu na fara ɗaya , nisan kiwo, na biyun mai suna SANYIN ADALCI is a Hausa mafian love story na tabbatar baku taɓa ji ko karan ta irin shiba ,
me kuke jira muyi maza ku aje shi a Library ko reading list ɗin ku , tun kafin na yanke shawara na maida shi na kuɗi madadin na kyauta,
YOU ARE READING
MAI SONA { 2023 }
Romance* 𝐒𝐞𝐱𝐲-𝐫𝐨𝐦𝐚𝐧𝐜𝐞-𝐡𝐞𝐚𝐫𝐭𝐛𝐫𝐞𝐚𝐤 * *Best in Wattpad ( 2022-2023 )* ★★★★★★★★★★★★★★★ Tana taka duk inda ya taka. Tana zuwa duk inda yake. Tana yin duk abin da yace Bata san komai ba sai soyayyar shi. Duk abin da yayi bata gani...